← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 162

Sashe 75

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safwan na gida yana bacci har karfe 4 na yamma, wanka yayi ya fita zuwa gidan kawunshi, daman labari ya samu labarin safwan yayi naira amma sai yace haka ba bai yuwa bane, yau karfe biyar ya zo unguwar cikin motarshi, Kofar gidan uncle dinshi yayi parking Sannan ya fito looking like human, handsome human, gate din uncle dinshi yayi knocking ranshi bace, he remembers lokacin da yake zuwa wannan gate din naima taimako sabida shi da sisters dinshi amma har ya kaiga uncle dinshi ya hana maigadinshi bashi daman shiga gidan, he's treated like a total stranger, in ya shiga gidan ko matan gidan na cin abinci basu bashi, at times da yunwa yake zuwa gidan amma ko ruwa basu bashi, he don't know what he's uncle told he's family about them da saa suka tsanesu sosai haka, yana knocking idanuwanshi kaman ba nashi ba, maigadi dake bude Kofar sai da yayi saurin ja baya dayaga eyes din safwan. Yana rumtse idanuwa Sai kuma yaga idanuwanshi are normal, shidai yasan abinda ya gani Don wani irin kallon tsoro yake mashi, sallama safwan yayi mashi tare da mika mashi hannu, ahankali ya mika mashi hannu shima but eyes dinshi kan na safwan,
"Dan Allah kawu na nan..." Ya tambayeshi, Mutumin that is still shocked yace
"Eh yana nan..Yanzu ya dawo..." Ya amsa mashi still not sure  ko ya gudu ko ya tsaya saboda shi dai yaga idanuwanshi dukda Abun ko second biyu baiyi ba ya gushe,
"Dan Allah yi min sallama dashi...kace safwan né yazo gaisheshi..." Yafada mashi, yana juyawa, idanuwa yayi rolling yana tunanin dole ya rage wannan temper nashi before ya fara tonawa kanshi asiri, yana son ya kauda tunanin yanda alhaji musa kanin sad dinsu yayi treating dinsu amma ya kasa, yana nan cikin ac da iyanashi amma su ko kudin biyar nepa basu dashi, Dan juyawa yayi ya kalli gidan tare dacewa
"He will surely learn he's lessons..." Yafada under he's breath,  gate aka sake budewa alhaji musa ya fito,
"Wai Kaine?.." Ya tambayeshi yana kallon daga kasa zuwa sama, Dan murmushi karfin Hali safwan yayi Sannan ya durkusa kasa yana cewa
"Good evening kawu..." Ya gaisheshi sounding so respective, uncle dinshi kasa magana yayi saboda yanda safwan ya Chanza kaman bashi ba, yasan Yanzu baifi wata uku rabon da ya ganshi ba amma kaman sunyi shekara uku basu hadu ba saboda yanda ya sauya cikin kankanin lokaci, safwan dake dukrushe can hear he's thought loud and clear, duk abinda ke yawo cikin zuciyar shi yana ji,
"Lafiya lau safwan....kaine ka koma hakan?.. Ikon Allah..aikin me kake?.." Ya tambayeshi sounding so confused, ahankali safwan ya Mike Sannan yace
"Wani né ya taimaka min..." Gani yayi uncle din yana kallon motar dake tsaye,
"Wannan na waye?.." Ya tambayeshi sounding out of words, Sannan yana takawa zuwa wajen motar, bayanshi safwan yabi yana cewa
"Nawa né kawu..." Yafada yana mashi wani irin kallo Mai tsoratarwa, Don indazai juyo sai ya gudu saboda tamkar yanda lion keyi in yaga abinda yake son hallakawa haka safwan ya dingayi,
"Yanzu safwan Kai né Mai Wannan motar?..unbelievable.." Yafada yana rike da handle din motar,
"Eh kawu nawa né..."
"Kai am so happy..am so excited...daman kana da kokarin nema...Allah yayi maka albarka..." Yafada cikin farin ciki, safwan tsaye yayi yana kallon shi, kawai Yana mamakin ko ya mance yanda yayi treating dinshi da family dinshi Don Yanzu he's acting so friendly and nice,
"Daman nazo né..." Safwan ya fara fada masu Sai kuma ya katseshi dacewa
"Mu shiga ciki...lets go inside..." Yafada yana shige mashi gaba, murmushi safwan ya saki tare da girgiza kanshi,
"It's a little bit late for all this kindness...." Yafada cikin ranshi yayinda yake bin shi cikin compound dinshi, Mai gadi kam baki ya bude yana kallon bayan safwan, part dinshi ya shiga safwan na biye dashi,
"Feel at home...am coming..."ya fada yana fita daga dakin, ahankali safwan ya zauna ya Dora kafa daya kan daya yana kallon falonshi, kawai tunanin da yake is inda uncle dinshi ya taimaka mashi da ko small amount of pity and advice né da bai shiga halin da yake ciki ba, amma sai gashi yau har da kiranshi cikin falonshi, bayan kaman minti uku ya dawo ya zauna aka fara biyoshi da abinci, second daughter dinshi ce ta shigo da ruwan sha, daga Kai yayi ya kalleta yana tunanin
"Target number one..." Yafada cikin ranshi, 
"Yaya Ina wuni..." Tafada cikin calm voice, murmushi ya saki yana cewa
"Lafiya lau Aisha...ya kike ya karatu?.." Ya tambayeta,
,"lafiya lau.." Ta amsa mashi cikin natsuwa Sannan ta ajiye ruwan ta fita,
"Pls eat,,," uncle dinshi ya fada mashi, bai yi mashi musu ba ya Dan ci Abincin kadan Sannan ya dawo seat dinshi, still Aisha tazo tayi parking plates, mikewa yayi yana cewa
"Uncle Bari in gaido ya cikin gidan ...sai in dawo in fada maka abinda ke tafe Dani..." Yafada yana mikewa, kawunshi dadi  kawai yake ji after everything safwan bai mance dashi ba, he's happy ya dawo gareshi after the way he treated him, baisan he's back to ruin him totally ba, daman matanshi biyu kuma akowacce da part dinta, amayar bata da manyan yara Don haka bai ma shiga wajen ta ba, part din uwar gidan ya shiga da sallama lokacin Aisha har ta ajiye plates ta dawo falo, sanye take cikin doguwar Riga, he don't know abinda uncle dinshi ya fada masu daya shigo amma they all look friendly, mutanen da before in ya shigo ko kallon inda yake basuyi su suke sakar mashi face haka har da tambayan shi ya aiki, zama yayi yana kallon Aisha da at least zata Kai 22 years Yanzu,
"Wai Aisha kin gama karatu kou?.." Ya tambayeta,
"Eh yaya...Yanzu service nake jira..." Ta amsa mashi kanta kasa,
"Madallah...Ina baraka?.." Ya tambayeta
"Tana school har Yanzu bata dawo ba..." Baraka itace Mai biwa Aisha,
"Har Yanzu?..naga har kusan 6.." Ya fada yana janta da hira,
,"eh...amma nasan Tana daf da shigowa..." Ta amsa mashi, mikewa yayi yana cewa
"Pls Aisha let me talk to you..." Yafada mata juyawa, da sauri ta bishi waje,
"Yauwa number dinki zaki  bani..." Yafada rike da phone dinshi,  ahankali ta mika hannu ta amshi wayar ta saka mashi number Sannan ta mika mashi,
"Thanks sis..." Ya fada, killer smile ta sakar mashi Sannan ta shiga ciki, wajen uncle dinshi ya koma yayi relaxing Sannan yace
"Daman yau nakeson daukan su Inna daga chan unguwar zuwa sabon gida...shine nace I should inform you..." Baki uncle ya bude not believing abinda safwan yake cewa
"Gida fa kace?.."
"Yes kawu..." Ya amsa mashi,
"Kai alhamdulillah....ai wannan abun farin ciki né..." Yafada sounding so excited, sake tambayan shi aikin da yake yayi nan ya zauna ya zayyana mashi karya shi kuma ya amince, safwan relaxing yayi har bayan sallah magrub Sannan ya bar gidan, yana daf da shiga unguwar ya Kira rabia ya fada mata ya iso, kaman Tana jira ta saka hijab ta fita, Mai gadi dake sallah sai hum hum hum yake amma ko kallon shi batayi ba ta fice, abunka da unguwar talakawa babu hasken nepa, koina is dark har suka gama abinda zasuyi cikin  mota babu Wanda ya gane, da sauri ta fito ta shiga gidan ta tarda babanta da sauran ya gidan tsaye a compound, duk Wanda ya ganta yasan bata da gaskiya,
"Daga ina kike..." Shine tambayan da alhaji Ibrahim yayi mata, shuru tayi Tana wasa da yatsunta,
"Wato ke Yanzu kin zama Mara Jin magana kou...now ki shiga cikin kiyi parking...gobe da safe you're leaving for kaduna..." Ya fada mata, bata ce komai ba ta shiga ciki, kawai she have decided ko Tana kaduna gidan aunty dinta ranar da safwan yace zasu tafi zata bar gidan ta bishi.

Takawa safwan yayi ya shiga unguwar su, Kofar gidansu ya tsaya yana kallon yanda gidan ya koma mashi very tiny, ko sallama baiyi ba ya shiga Inna da asiya da sauran family dake zaune suka kusa rugawa da gudu ganin mutum kaman daga sama Sannan gashi babu hasken nepa, wayar shi ya fiddo ya kunna touch light Sannan ya karaso, kallon sisters dinshi dake kallon shi sama sama yayi yace
"Wai Dan ubanku Baku iya gaisawa ba?.." Ya daka masu tsawa, jiki na rawa suka gaidashi duk sai bin faces dinsu yanke da hasken wayar, sai da ya gama kallon su ya koma kan Inna data saki baki Tana kallon ikon Allah,
"Ina wuni..." Ya gaidata kaman baison magana, kasa amsawa tayi sabida yanda ya koma, dukda koina is dark she can see him,
"Yanzu dai nazo in daukeku...Inna tashi mu tafi sabon gida..." Yafada atakaice,
"Ban gane ba...," tafada kaman bai ta ba, bai Kara cewa komai ba ya shiga cikin sakinta ya nemo wata hijab ya dauko kaman yana rike kashi ya wurga mata Sannan ya juya ga su asiya yace
"Kowacce ta dauko hijab dinta..."  Babu musu suka shiga ciki suka fito da hijab har lokacin Inna na zaune ta kasa ko motsawa,
"Inna tashi mana.,dare nayi..." Ya fada kaman he's talking to he's daughter,
"Wai Ina zamu?.." Ta tambayeshi kaman she's finding it difficult to talk,
"Muje zaki gani..." Yafada atakaice yana Kama hanyar waje, juyowa yayi ya kalli su asiya da hasken touch dake hannunshi, da sauri suka shiga mashi gaba, Inna kam Tana zaune inda take,
"Wai Inna kefa nake jira..kar ki bata min lokaci..." Yafada sounding very angry
"Ina aka taba tashi ba'a kimsa Kaya ba..." Bai Bari ta karasa ba yace
"Muje gobe da safe zan maidoki ki dauki duk abubuwan da kike bukata...hakan yayi?.." Ya tambayeta bata amsa ba ta Mike ta shiga ciki ta fito da kuba hannunta, bai Kara cewa komai ya fice, itama fitowa tayi ta kulle gidan tabi bayansu.

Thanks.25💜💚💛💙❤️
Sirrin wasu gayun
💛💙❤️💜💚

® zuwairat (ummumaryam)

2️⃣5️⃣

Don't read if you didn't pay if you do you owe me.
Chapter 75 · 0% Book details