← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 162

Sashe 19

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau né zasu tafi anambra state, kowannensu kwana yayi yana Allah Allah gari ya waye su shirya su Sami alhaji idris a gidashi kaman yanda ya umarcesu, Ana kiran sallah asuba duk suka Mike, safwan fita yayi zuwa cikin gida yayi alwallah is a tafi masjid inda suka hadu da Junansu, gaisawa sukayi kowa ya koma gida Don shiryawa. Cikin sauri sufwan ya dawo gida yay wanka ya shirya cikin wasu new shadda ya Dora da hula looking corporate, wata bag  daya saya ya saka kayanshi kaman kala biyu ya fito lokacin gari ya fara wayewa, cikin gidan ya sake shiga ya yaye labulen Kofar Inna ya shiga ciki, Inna dake zaune kan praying mat ta kalleshi from head to toe Sannan tace
"Amma Kai da son kanka kake...Yanzu wa zai ganka yace daga wannan matsiyacin gidan ka fito?.. Amma mu ka barmu kaman almajirai...gaskiya da akwai sakal..." Dan murmushi ya saki yana cewa
"Inna kar ki samu damuwa...indai kudi ya samu kome kikeso zaki samu..."
"Allah yasa..." Ta amsa mashi atakaice,
"Yanzu zan wuce..."
"Tou a dawo lafiya..." Ta amsa mash , mikewa yayi ya fita zuwa compound, Kofar Dayan dakin yaje yayi sallama sisters dinshi uku suka fito, nan yayi masu sallama Sannan in a fito ya kaman hanyar gidansu usman kasancewan gidansu safwan shine a baya duka, yana zuwa shima usman ya fito shirye cikin Jean da Riga, yayi kyau sosai,ciki safwan ya shiga ya gaida iyayen usman sukayi masu aduar saa Sannan suka fito zuwa gidansu habib, sallama sukayi suka shiga ciki suka ga mamanmu rike da habib sai kuka take kaman wata yarinya, habib najin sallamansu ya juya da red eyes dinshi ya kallesu, ahankali yace
"Kawai ku tafi...ni na fasa zuwa..." Yafada masu, cikin kuka mamanmu tace
"Aa ka tafi...Allah ya karemunka...ya kaiku ya maidoku lafiya...Allah ya kauda idanuwan makiya kanku...kawai zanyi kewarka né..." " Ta fada Tana sakinshi,
"Aa mamanmu...nasan bakison Inyi wannan tafiya...kawai na hakura..Allah zai bani wani aiki...bazan je ba..." Yafada mata sounding firm. Safwan da usman tsayawa sukayi suna kallon su, daman sun San this will happen tunda lokacin da suna school duk sanda zai tafi sai tayi kuka,
"Aa kaje..." Ta fada mashi cikin sanyinmurya Sannan ta juya ga safwan da usman
"Dan Allah ku kula da kanku...Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya...kunji kou?.."
"Ameen..." Suka amsa mata cikin sanyinmurya, safwan kam he's feeling inama shi mom dinshi take ma haka, ciki habib ya shiga ya dauko Dan karamin bag kaman nasu safwan saboda lokaci daya suka sayi shi, wayar safwan né ya fara Kara ya fiddo ta yaga alhaji idris,
"Kayi sauri gashi yana kirana..." Safwan ya fadawa habib Sannan yayi piçking wayar, alhaji idris ya fada mashi he's waiting for them.
Karfe 8:30 suna gidan alhaji idris, bai tsaya bata lokaci ba suka Kama hanya yaja cewa
"Next time ku dinga sauri...tafiyar ba ta nan bace" Yafada yana tuki, safwan  zaune gaba sai habib da usman zaune baya, tunani suke why is he's driver not driving Sannan why bai hau jirgi ba tunda yana cewa it's a very long journey. Babu Mai cewa komai har sukayi tafiya na hours biyar, tsayawa yayi sukaci abinci Sannan suka cigaba da tafiya. Ganin bayan asar suna tafiya yasa gabansu fara faduwa, habib Sufwan kallon habib da usman yayi ta mirror suma suka kalleshi, wayarshi ya dauko daga cikin aljihunshi ya rubuta
"Ina wannan Mutumin zai kaimu?...ka maida wayarka silent kar ya gane..." Ya turawa habib, Jin Kara message yasa habib ya fiddo wayar shi, silent ya maida wayarshi Sannan ya rubuta
""Nima wannan tafiyar is scaring the hell out of me...Kodai mu fada mashi ya tsaya in yaki mu zaneshi?.." Ya turawa safwan, Sannan ya mikewa usman wayarshi Don ganin abinda suke tattaunawa, Sufwan na ganin message din ya saki murmushi Wanda yasa alhaji idris dake tuki ya Dan juyo ya kalleshi,
"Lafiya dai?.." Ya tambayeshi wearing a smile
"Wallahi ba komai.." Safwan ya amsa mashi, Sannan ya rubuta
"Ka ban dariya Wallahi..kawai dai mu tambayeshi inda zamu haka..Don mi Wallahi na gaji..." Ya turawa habib, habib na karantwa ya saki hamma tare da mika Sannan yace
"Ranka shi dade wannan tafiyar tayi nisa da yawa...." Habib Yafadawa alhaji idris, Dan dariya alhaji yayi Sannan yace
"Zaku Saba né...Nima lokacin da aka fara kawoni har fargaban kar a kasheni na dingayi...amma Yanzu na Saba..." Yafada sounding so friendly
" tab gaskiya Nisan is too much..." Usman ya fada mashi
"Ai Dadin abun Baku sake dawowa sai nan da wata daya...kunga da sauki kenan..." Alhaji idris ya fada masu
"Ni Wallahi Ina da kudi kaman Kai ban wannan doguwar tafiya a mota...jirgi zan dinga hawa..." Inji safwan, dariya alhaji idris yayi Sannan yace
"That means you want people to know where you go every month..." Yafada mashi, habib zaiyi magana alhaji yac
"Pls ku barni in maida hankali kan driving...inason mu Kai before 7.." Yafada atakaice, shuru sukayi babu Wanda ya sake cewa komai har suka Isa cikin garin anambra. Hotel daya Saba sauka ya nufa yayi parking, a gajiye suka fito suna kallon hotel din dake walkiya kaman rana, duk Wanda ke wajen babban Mutum né, suna shiga ciki alhaji idris yaje wajen receptionist ya bukaci rooms guda biyu, safwan da habib da usman baki suka bude suna kallon wannan wajen, wani matashi né yazo ya amshi bags dake hannunsu,
"Follow me..." Saurayin ya fada masu, suna dab da juyawa wani babban Mutum ya shigo wajen, dariya alhaji idris ya saki ya nufo Mutumin Wanda da ganin shi he's Yoruba, gaisawa sukayi  Sannan suka Shafa zobensu kaman yanda sukeyi, idanuwa su safwan suka zuba masu suna kallon irin wannan gaisawa, Mutumin Dan lekawa yayi yaga yanda suka zuba masu Ido, kallon alhaji idris yayi ya rada mash wata magana, dariya alhaji yayi Sannan yace
"New recruits..." Ya fada mashi yana kallon su safwan, dariya Yoruba man din yayi da karfi Sannan yace
"Welcome to the world of power..." Mutumin ya fada masu, murmushi suka sakar mashi not understanding what he meant. Baya suna gama gaisawa suka hau upstairs, kafin su shiga dakin alhaji idris yace
"You should relax and rest...za'a kawo maku abinci..." Ya fada yana kokarin shiga nashi dakin
"Sir Ina kibla?.."habib ya tambayeshi, wata direction ya nuna masu sanna ya shige abinshi. Suna shiga duk sukaware idanuwa suna kallon wannan makeken dakin,
"Wanna shine five stars hotel...." Inji safwan dake wulla tired body dinshi kan wata large cushion, 
"Wannan waje abin tsoro né...ya hadu da yawa..." Inji habib,
"Wai wane irin gaisuwa sukayi dazun?.. Abun ya tsaya min a rai..." Inji usman,
"Nima abun ya bani mamaki...kaman na matsafa Wallahi...wai Shafa zobe kan junansu Sannan irin zoben daya..." Inji habib
"Well zato zunubi...muje muyi sallah ..." Safwan ya fada yana mikewa cikin kasala, hanyar wata kofa yabi ya bude yaga makeken gado daya sha duvet cover, 
"Wow....duniyar Hutu..." Safwan ya fada cikin natsuwa, bayanshi habib da usman sukabi sukayi tsaye bakin Kofar suna kallon irin gadon da koma film basu Taba ganin irin ta ba, safwan né ya shiga ciki sukabi bayanshi, wata kofa ya sake budewa yaga bathroom, few minutes later ya fito da alwallah, Sannan habib ya shiga shima fito then usman, daya daga cikin rigarsu suka dauka suka shimfida sukayi sallolin da ake bin su Sannan aka kawo masu abinci Mai rai da lafiya suka zauna nan sukaci, kwanciya sukayi nan kasan carpet, basu farka ba sai wajen Karfe shida na safiya, da gudu suka shiga bathroom sukayi alwallah tare da sallah asuba, Karfe goma aka kawo masu breakfast, bayan sun gama suka koma bakin window suna kallon compound din hotel din,  manyan mutane dake shige da fice suka zubawa Ido, bayan kaman minti goma aka bude kofa, alhaji idris né ya shigo,
"Ku taho mu tafi..." Ya fada masu ,
"Mu dauki bags dinmu?.." Habib ya tambayeshi
"Aa..leave them here...zamu dawo nan Ai..." Ya fada masu,  fitowa sukayi still wearing Kayan da suka zo dasu, inda motarshi take sukaje suka shiga bar wajen, tafiya ya dingayi har suka kaman hanyar dajin da gidan haduwansu yake, dukkan su tashin hankali da tsoro né kwance kan face dinsu,
"Sir Dan Allah ka tsaya...wannan dajin na bani tsoro..."  Habib ya fada cikin tashin hankali, dariya alhaji yayi yac
"Haba be a man mana...ai ku Yanzu Baku da sauran tsoro..sai dai aji tsoron ku ba dai ku kuji na wani ba..." Yafada cikin confidence, bayan kaman minti ashirin da wannan maganar suka hango wata katuwar gida kaman cattle a tsakiyar daji,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Duk suka fada atare
"Dan Allah kar kayi mana komai....ka rufa mana asiri..." Safwan ya fada yana kokarin fashewa da kuka, Banda dariya babu Abunda alhaji idris yakeyi
"Haba babu abinda sanyi maku...inda Ina da niyyan cutar daku da tuntuni nayi hakan...kawai I want to give you what any guy out there is hustling to have...money and power..." Yafada yana kaiwa gate din gida, horn yayi sau uku aka bude gate din, motocin da suka gani a compound din ya Kara tada masu hankali, kulle giant gate din akayi alhaji idris yayi parking a available space,  fitowa alhaji idris yayi while su safwan suka makale cikin mota
"I always heard a bad feeling...gashi..." Habib ya fada hawaye na taruwa idanuwanshi, Bai karasa ba yaji alhaji ya bude masu kofa,
"Ku fito mu shiga ciki..." Yafada yana kallon faces dinsu that is all looking so frightening,
"Kuma banson any fuck up..accept anything you're asked to do..." Yafada sounding firm and strong.7💛💜💙💚❤
Sirrin wasu gayun
💜❤💚💛💙

® zuwairat (ummumaryam)

7⃣

Don't   read if you didn't pay

Dedicated to the strongest woman I have ever known, anty Allah ya kare ki daga sharrin masu sharrin.
Chapter 19 · 0% Book details