← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 162

Sashe 123

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

A gida kam su Inna suna kalaci sukaji wani irin ihu,  ana buga gate da karfi,  Mai gadi sukaji yana cewa
"Waye haka... " inji maigadi,  basu ji abinda aka fad'a ba kawai sai sukaji anyi harbi, haba nan  take jikinsu Inna ya dau rawa,  gashi babu hanyar fita sai  ta gate, harbin gate aka dingayi har sai da ya bude,  Mai gadi kam tun har bin farko yaji kanshi kasa, suna bude gate suka shiga maza ne sun Kai su bakwai sannan kallonsu kawai abun tsoro ne,  duk idanuwansu jajir saboda zalunci,  irin mutanen nan wayan da manyan mutane ke amfani dasu wajen aikata dirty things dinsu, ko. Kadan basu San tausayi ko rangwame ba, duk Wanda ya shiga gabansu in suna aiki sunanshi sorry. Part din safwan suka shiga suka birkita koina amma babu kowa, Inna da asiya da sauran yara sun dunkule cikin bathroom jiki sai rawa yake, inna sai karfin hali take Tana Danne masu baki wai kar suyi ihu Suji, kiran alhaji sukayi suka sanar mashi babu kowa gidan, cewa yayi ko birkita gidan zasuyi su nemo mashi su, kar su dawo empty handed. Nan suka shiga karamin part din suka fito da Inna da yaranta, sai rokansu take, ganin an dora mata bindiga a goshi tayi shuru, asiya kam bata san inda kanta yake ba, nothing frighten kaman a gun to the head, wata irin sharon biyu sukazo dashi, cikij daya suka tura su Inna da wasu gangs.
Kafin a kaisu inda zasu yaran sun bata jikinsu da excretion, duk saboda fargaba, alhaji Mai saa kam yana kiransu ya Mike ya hau mota driver ya fita dashi ko inda Mai gadi yake bai kalla ba, in kaji ana maganar masu gadi bakaga tashin hankali ba, yasan safwan is dangerous dole ya nuna mashi bacin ranshi, he have to be thought a lesson of a life time. Ana kawosu wannan gidan dake slaughter house din Mai saa inda yake kawo victim ya kashe ya cire wasu abu in bukatar hakan ya taso, ingizasu akayi ciki babu abunda ke tashi sai wari saboda wannan yaran da suka bata jiki da feaces, Inna sai kuka take tana dana sanin haihuwar safwan. She cried and cried and cried until no tears coming out of her eyes. Bata taba tunanin haihuwan da yana zama balai ba sai yanzu, Mai saa ne zaune ya dora kafa daya kan daya, duk kneeling aka sa sukayi a gabanshi yana kallonsu one after the other,
"Wato dukda nazo har gida da kaina nayi maki kashedi baki ji ba har sai..." da sauri inna tace
"wallahi... "wani irin kara taji a kunnenta, komai nata tsayawa yayi as a results of Marin da akayi mata ta baya,
"kar ki sake magana sai an baki daman yi... "shine abinda wanda ya mareta ya fad'a mata, inna km bataji ba because she became deaf in an instant, Dummm kawai takeji a kunnenta, bakin Mai saa tagani yana motsi amma bata San abunda yake cewa ba, asiya dora hannu bisa baki tayi hawaye ba zuba idnwuanta, yaran kam duk idanuwansu waje saboda balai, ya Allah don't make us the victim of our father's, mother's, sisters, brothers bad family sins. Alhaji Mai saa kallonsu kawai yake not knowing what to do withthem, he will really love to kill them amma yana tuna abinda safwn yace
"one of my family is equal to three of your Family "wannan statement din yana yawo a kunnen Mai saa. Kanshi ya maida kan asiya yana kallonta, daya daga cikin gangsters din mai saa ya kalla sannan ya nuna asiya yace
"kai min ita ciki... "yafada mashi.

Thanks47❤🧡💚💜💙
Sirrin wasu gayun
💚❤💜🧡💙💛

®Zuwairat (ummumaryam)

4⃣7⃣
Chapter 123 · 0% Book details