← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 162

Sashe 10

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acikin wata karamar kauye nan cikin garin Kano wata matured woman ce zaune sai soya awara take while wata budurwa da bazata wuce 16 to 17 ba Tana zaune gefen daya Tana zuba awarar da matar ke soyawa cikin wata katuwar farar roba, hannunta na konewa saboda zafin awarar amma hakan bai hanata zuba awarar ba, sai yarfa hannunwa take Tana kwacewa,
"Inna kiyi sauri mana..." Bata karasa ba matar ta hantareta dacewa
"Dalla ki rufemin baki..kin dameni da Inyi sauri...wane irin sauri kike son in karayi  bayan wannan..." Matar ta fada sounding angry while Tana juya awarar dake kan wuta,
"Ai Inna tafiya zasuyi su barni..." Matar kallon saitin rana tayi Sannan tace
"Ke Wallahi matsala gareki...Yanzu Fatima har Karfe sha biyu tayi da zaki sha min Kai?.. Dan Allah ki kyaleni Inji da Abunda ya dameni..." Matar ta fadawa yarinyar,  shuru yarinyar Tayi bata Kara cewa komai ba, daka gan yarinyar da matar kasan uwa da diyace, saboda suna Kama babu laifi, gidan su is a very tiny house Wanda bai da fili sosai, but still da akwai tumakai a yar karamar compound dinsu, da ka gansu kaga Fulani na asali, matar sai suya kawai take Tana sauri, sai da ta kusa cika robar tallan da awara Sannan ta kalli yarinyar tace
"Maza shiga daki ki dauki ledar da yaji..." Matar ta umarceta, da Sauri Fatima ta Mike ya shiga cikin yar karamar dakin da bai da komai sai old furnitures ta dauko abinda mahaifiyar ta ta umarceta ta dauko, Fatima yarinya ce Mai kyau fiye da tunanin Mai karatu, she's so nice and gentle, bata da hayaniya Sannan batason hayaniya, iyayen ta are poor village farmers wayanda suke Kaunar da two siblings dinta, kullum mom dinta Tana soya mata awara kaman the rest of the villagers ta dauka Sannan tabi bayan sauran mutane su shiga near by park su saidawa mutane, she sells a lot saboda duk rana saida ta saida awara ya Kai na 2k, Tana fitowa yayi daidai da shigowan wasu yanmata da suke age mate dinta su hudu, kowacce dauke da robar Kayan sanaar ta, daya dauke da gyada sai wata same awarar wata kunu wata boiled egg,
"Wai zarau baki gama ba?.." Mai dauke da Kwai ta fada mata,   .
"Yanzu zan gama..." Tafada da sauri Tana ajiye Leda da pounded and spicy pepper cikin robar awara, sauran awarar mom dinta ta kwace ta zuba mata Sannan ta dauki robar
"Allah ya tsare ya kiyaye...ku dawo lafiya...kar ku kuskura ku tankawa mazan birni...kinji kou?.." Matar tayi warning dinta,
"Tou Inna...amma in ban saida a tasha ba in tafi hanyar Kano kou?.." Ta tambayeta
"In ba ke kadai zaki ba . Kuje tare...amma in nasu ya kare naki bai kare ba ki biyosu ku dawo gida..." Ta umarceta,
"Tou shikenan Inna..." Tafada Tana biye da sauran yanmatan dake dauke da Kayan sanaar su.

"Abba Wallahi in ba hostel ba bazan samu Inyi karatu yanda ya  kamata ba...Dan Allah kuyi hakuri ku Bari in samu daki a hostel..." Nana ta fada Tana zaune gaban dad da mom dinta Tana shirga masu karya kawai Don su amince ta zauna hostel,
"Wannan yarinyar is unbelievable...wato Don muna Mara hankali sai in sakeki kije hostel ki zauna....wato you are looking for a way to get out of this house...Wallahi ki yi karya...day zakiyi ba campus zaki zauna ba..." Mahaifiyar ta tafada mata babu wasa, ahankali nana ta turo baki Tana kokarin kuka
"Wallahi da akwai nisa daga nan zuwa buk....kuma ya kashe kudin abun hawa...nidai abba ka barni in je duk weekend in dinga dawowa gida...." Tayi directing maganar ta to her father that is quite, wata yar bazawarar dariya mahaifiyar ta tayi Tana cewa
"Wato Yanzu nana kina nuna min ni ban isa in saka baki kan alamranki...well kuyi duk yanda kuke so..." Ta fada Sannan ta Mike ta bar masu dakin, nana fashewa tayi da kuka Tana cewa
"Nidai abba ka barni in zauna campus...kaga Kai ba Mai kudi bane balle Ashe kullum ka dinga kashe min kudi Ina zuwa makaranta...kaga ko Maryam ma hostel zata zauna..." Tafada cikin hawaye,
"Wai ke nana meye matsalar ki?.. Meyasa duk yara mata suna son zama karkashin inuwar iyayen su amma Banda ke?.." Mahaifinta ya fada calmly, da sauri nana tace
"Wallahi abba ba haka bane...inason zama gidan mana..,kawai Ina tausaya maka né saboda nasan Baka da kudin da zaka dinga bani kullum Ina zuwa makaranta...Wallahi abba duk asabar da lahadi Ina gida...pls abba..." Ahankali dad dinta ya girgiza Kai yana cewa
"I don't believe abinda kike cewa...kawai ke ki nason zaman hostel din né ba Don tausayi na ba..."
"Wallahi abba..." Ta katse dad dinta, shima bai Bari ta karasa ba ya Dora mata hannu a baki alaman tayi shuru, babu musu tayi shuru Tana kallon dad dinta
"Nidai tell me why kikeson zaman campus..." Ya sake tambayan ta cikin natsuwa,
"Abba saboda in samu damn karatu...abba gidan nan ban samun lokacin Kaina balle na karatu...Dan Allah abba ka Bari in zauna hostel plssss..." Tafada cikn begging dinshi,
"Ok shikenan...amma in first semester result dinki ya fito naga baiyi kaman na brothers dinki ba zaki dawo gida...deal?.." Da Sauri ta daga mashi Kai farin ciki kwance kar face dinta, she looks so happy she's finally getting away from home, ji take kaman ta tashi Ta daka tsalle saboda farin ciki, she never thought of her home as a shelled or protector, kawai she sees it as a place where babu komai cikin ta sai aiki.
"Abba nayi maka alkwarin zanyi karatu fiye dasu yaya...results Dina sai yafi nasu kyau, I promise..." Ta fada mashi Tana mikewa, barin dakin tayi taga mom dinta zaune a compound, ko inda take zaune bata kalla ba ta shige dakinta, da sauri tayiwa Maryam text cewa an amince ta zauna hostel itama ta kokarta a barta.

The following day bayan sufwan ya sayi kosai da koko yayi breakfast ya fito daga dakinshi ya shiga cikin gida sharye cikin wasu faded Jean da Riga, sallama yayi siblings dinshi suka amsa mashi amma Banda Inna,
"Inna na fita néman aiki..." Yafada tare da durkusawa gabanta, face dinta daure ta daga Kai ta kalleshi tare dacewa
"Sauran kuma ka dawo hannu rabbana..." Tafada mashi atakaice, 
"Allah yasa in samu Inna..." Yafada cikin sanyinmurya, tsoki taja without saying a word ya Mike,
"Yaya a dawo lafiya,,," wata sister dinshi ya fada mashi, murmushi ya saki yace
"Allahumma ameen..." Ya amsa mata Sannan ya fice daga gidan, cikin natsuwa ya taka ahankali zuwa gidansu usman, gaisawa sukayi da iyayen usman Sannan suka fito zuwa gidansu habib, sallama sukayi suka shiga, mahaifiyar shi dake zaune compound Ta amsa masu face dinta dauke da murmushi, durkusawa sukayi suka gaisheta Ta amsa masu Tana cewa
"Manyan gobe kun iso.." Ta tambayesu cikin kulawa,
"Eh mama..." Sufwan ya amsa mata
"To Allah yayi maku albarka, ...Allah ya Baku aiki na gari..." Ta fada masu cikin so da kauna, idanuwa sufwan ya lumshe tare dacewa
"Ameen mama..." Habib né ya fito daga wanka ya kallesu tare dacewa
"Yau kun fito da wuri..."
"Eh mana..,we have to be early..." Usman ya amsa mashi, ciki ya shiga Shima ya shirya ya fito ya kalli mom dinshi yace
"Mama sai na dawo..."
"Tou dana...Dan Allah ku guji haram...Dan Allah kar ku dauki abinda ba naku ba....Allah ya Baku aiki na gari...Insha Allah sai kun biya mana makka..." Yafada masu, sufwan shuru yayi yana kallon ta, he wish he's hearing this firm he's mom
"Insha Allah mamanmu..." Usman ya amsa mata,
"Allah ya yarda...kundai ji abinda nake fada maku....banda cin hakkin wani...Wallahi komin kankantarta Allah bai yafewa...ku nemi halal ku guji haram...kunji kou" Ta fada masu kaman yanda take fadawa danta kullum in zai fita nema
"Eh mamanmu..." Duk suka amsa mata lokaci guda,
"Tou Allah ya tsare ku dawo lafiya..." Ta sake fada masu suka amsa da ameen Sannan suka bar gidan as usual Don néman abinyi. Suna fita zuwa  bakin titi suka hau adaidaita zuwa cikin gari inda suke tunanin zasu samu aiki, kaman kullum suka fara shiga manyan shops suna tambaya in suna bukatar Mai aiki, duk inda suka shiga basu samu ba har wajen Karfe biyu na rana, yau da sauki kan jiya tunda sun San da akwai abinda yan gida zasu ci, bayan sallah zuhr suka sayi abinci sukaci Sannan suka taka zuwa wata katuwar building da aka rubuta jifatu,  ciki suka shiga suka nufi kan counter inda wani mutum ke tsaye da beautiful matarshi, Kaya né da yawa kan table wani dake zaune yana calculating, Mutumin dake da Kayan juyawa yayi ya kalli matasan uku while shima Wanda ke calculations ya daga Kai ya kallesu  yaga babu alaman komai hannunsu Sannan sunyi tsaye suna kallon su,
"Lafiya dai?.." Cashier ya tambayesu, Mutumin dake tsaye da matarshi kallon su kawai yake without blinking,
"Assalamun alaikum.." Sufwan yayi masu sallama, amsawa cashier yayi Sannan sufwan yace
"Dan Allah munzo né ko zamu samu aiki.." Ya fada mashi cikin natsuwa, cashier kallon su yayi from head to toe yaga yanda legs dinsu yasha kura Sannan yace
"Kuyi hakuri babu vacancy..." Ya amsa masu atakaice Sannan ya maida hankali shi kan calculations din da yake, Mutumin tsaye yayi yana kallon su, marairacewa habib yayi yace
"Don Allah ko aikin shara bazamu samu ba?.. Wallahi mun dade muna néman abunyi..." Habib Yafada kaman zaiyi kuka,
"Malam nace maka babu aiki..." Cashier ya amsa mashi sounding a little bit harsh, basu Kara cewa komai ba suka juya shima Mutumin ya bisu da kallo, sai da suka fita Mutumin ya jiya ga  matarshi  tare dacewa
"Hajiya am coming..." Yafada yana juyawa, hanyar waje ya Kama yabi bayan su sufwan.

Share thanks...4💚💜❤️💙💛
Sirrin wasu gayun
💜💛❤️💚💙

® zuwairat (ummumaryam)

4️⃣

Free page
Chapter 10 · 0% Book details