← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 162

Sashe 41

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaren usman ma abun babu sauki, shi sauran kadan daya haukace daya ga ghost amma tunda yasan of he's not careful zaa gane shi sai ya basar har ya wuce, Yanzu shi gurinshi ya dinga ganin alert, tsakanin shi da safwan Allah kadai yasan who's more dangerous, the difference between them is shi safwan yana da target and goals while shi kuma babu, kawai ya samu gida ya saya baya fita sai dare, shima don néman who to quench his thirst with. Yanzu wannan friendship din babu, kowa it's on he's own,
the following morning wajen karfen ukun dare Habib ya dinga yi yana kiran
"Kar ku kasheni ..kar ku kashe...wayyo mamanmu..." Duk neighbors suna Jin wannan ihun dayake da gudu mamanmu ta tashi rike da touch light ta  shiga dakin, ganin shi   tayi yana zuwa sai magana yake yana cewa
"I can't...I won't...I will rather die...." Yafada yana fighting, adua mamanmu zama tayi Tana dafa shi Tana cewa
"Modibbo..." Takirashi amma baiji sai tirje2 kawai yake yana cewa
"Pls kar ku kasheni..." Yafada yana fashewa da kuka da m, adua mamanmu ta fariyi Tana tofa mashi, kuka kawai yake yana rokon kar a kashe shi, adua mamanmu ta cigaba sayi har ya daina wannan ihun da magana sai ajiyan zuciya kawai yake, har lokacin bai bude Ido ba mamanmu ta sa hannunta goge zufan gaban goshinshi, har garin Allah ya waye mamanmu Tana dakin, ta Lura bbai minti goma bai firgita ba, da safe bayan duk su yi sallah asuba abban Fatima ya shigo yana tambayan Abunda ya faru yake Jin ihu yau,
,"Dan Allah ku taimaka min...banason rasa modibbo..." Mamanmu Tafada Tana hawaye,
"Wai daman shine ke ihu?... Nayi tunanin ko wani né ko kuma barawo aka kama." Yafada sounding so surprised, kallon habib yayi yana tambayanshi yana cewa
"Me yasa meka?.."
"Kawu mafarki né kawai..." Habib da duk ya rame ya fada mashi
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...aljanu né...bakake..." Yafada yana rike da waist dinshi , ajiyan zuciya habib yayi ya rafka tagumi
"Sunfi aljanu..." Yafada cikin ranshi,
"Rukiya zaa yi mashi...Insha Allah zaa dace..." Kawunshi ya fada, habib dai bayason yi mashi gardama amma yasa nothing can save him now, he feels he's soul is not with him, ko Yanzu da yake zaune  yana ji kaman he's in another world, he feels like ya Dora hannu bisa Kai ya dinga ihu ko ya samu sauki,
"Kawu..." Ya Kirashi, amsa mashi yayi Sannan habib yace
"Nidai a bar zancen auren nan..." Bai karasa ba duk mutanen tsakar gida suka saki salati har da gwaggo,
"Amma wannan yaron yana néman haukacewa...in ba hauka ba ka taba ganin an fasa aure Ana kwana biyu daurin aure?.." Gwaggo ta fada cikin bacin rai, hakuri habib ya basu ya Mike jiki babu kwari ya fita daga gidan, shidai kawai he wants nothing, ji yake Jin dadin duniyar na gushe mashi ahankali, yana ji kaman an fixgar wani Abu cikin jikinshi, takawa ya dingayi har ya bar cikin gari ya samu waje ya zauna ya dinga kuka, kawai he's feeling so bad and weak, ko appetite bai dashi kuma bai ci komai ba. Gidan su kam har yanuwa na nesa sun fara zuwa biki kunsan yan kauye da akwai su da zumunci, duk da it was on a short notice bai hanasu zuwa ba, Fatima kam sai shirya ta suke in their own little way, Ana gobe daurin aure akayi jere, it looks so beautiful dukda it's in the villa, Tana da complete set na gado da komai da mutum ke buka na rayuwar yau da kullum, nasiha ake bata kan zaman aure, shi kam habib bai zama gida  Yanzu, gari na wayewA yake komawa bayan gari ya zauna ko abinci baici, mamanmu ta shiga damuwata sosai saboda yanda yake komawa, kullum Rama yake then he's acting weird, at times sai ya firgita ya juya da sauri, hakan na Kara tadawa mamanmu hankali, wurin abban Fatima taje ya gaita gidan babban malami a kauyen tayi mashi bayanin abinda ke faruwa dukda bata da details, nan ya ce a dinga zuwa Ana amsar mashi rubutu kullum.

A gidan alhaji bello kam Ana cikin tashin hankali, alhaji bello yana daga cikin yan kasuwa masu néman kudinsu ta hanyar halal, Sannan abun duniya bai rufe mashi Ido ba Don in har yana da million biyar yana iya bada kyauta da rabi, Sannan a sanaar shi bai zalunci bai cin hakkin mutum Sannan yana fita hakkin neighbors dukda a unguwar dayake babu talaka sai masu Hali irinshi, kap family dinshi babu Mai kuka dashi saidai kawai aki shi saboda nasu dalilin, yana da mata daya da yaran shi hudu, yan mata biyu sai Maza biyu, babban danshi is married da Nashi family so is he's second daughter sai na ukun Mai suna shahid than autarshi mufida, duk yaranshi suna da allowance da yake basu har masu auren bai Bari a baya ba, farin cikin shi shine ya gan duk na kusa dashi cikin walwala, he helps lots of people Don in har kayi 5years kana mashi aiki zaiyi settling Dinka to become your own boss, bai yarda da enslaving mutane for a long time ba,  ba karamin adua yake samu wajen jamaa ba Don da wuya ya wuce talaka bai taimaka mashi ba, bai siyasa amma most yan siyasa suna kamun kafa dashi saboda yanda yake da jamaa, yanda da arziki da bai kamata yana néman wani Karin kudi ba, kullum matarshi Tana fada mashi he should step down ya huta haka nan because life is short sai yayi murmushi ya amsa mata da
"If I can't spend am sure da akwai people that can spend..If I stop working who will take care of them?.....its better inyi hustling Yanzu ko Allah yasa in huta a Chan..." Wanna shine reply da yake bata duk sanda ta nemi ya rage stressing kanshi, he's rich da yakama ya tara uwayen dukiya amma bai Tara ba, because he normally says
"Wai mutum na iya kwanciya cikin daki biyu at a time?..then why should I keep many houses while da akwai wani da bashi da rabin nawa?..", hakan yasa yana da mansion guda daya tal a garin Kano Sai kuma wasu abroad shima Don kar su nemi masauki da family dinshi in sun fita waje kawai in yaje inda life dinsu is so poor sai yayi choosing lucky ones ya samu contractors su sake masu gida zuwa modern building or in renting kake kana iya Jin an Baka kyautar gida from unknown person, Family dinshi are happy until what happened to mufida, har bayan kwana uku mufida bata iya takawa da legs dinta, she's taking drugs and Doctor yana kula daita a gida amma it's not working, family na tsoron fita daita hospital saboda yanayin case din zai bata masu suna, dad dinta kullum cikin kuka yake saboda wannan bakin cikin, he loves mufida so much, he never knew ita ta Kai kanta despite duk kokarin da yake kanta, tun ranar babu ranar da bata ganin jini, mufida ce kwance kan gado da drip hannunta mahaifiyar ta na zaune gaban gadon, duk Wanda yaga mufida sai ya tausaya mata,  duk ta koma kaman baita ba, she looks so pale and weak, kullum babu abinda take cewa sai she's sorry, dad dinta ya hanata cewa sorry amma kullum bata da word daya wuce she's sorry, kawai abinda take tsoro shine in dai ta mutu a haka she's going to hell straight saboda she have everything but was still greedy, dukda Tana da lavish spending dad dinta bai barinta babu kudi amma 500k was huge that she can't turn her back on, gashi 500k ya kaita ya baro ta, she never knew namiji yana iya yiwa mace abinda wannan mugu yayi mata, she don't even know he's name, Yanzu she will give a million to go back to her normal self, kawai ji take inama if she can tell her mother exactly abinda ya faru amma tasan he mom will strangle her to death, idanuwa ta daga ta kalli mahaifiyar ta,
"Mommy..." Ta kirata cikin sanyinmurya,
"Yes dear..."
"A bani pad....yana zubowa..." Tafada mata hawaye na taruwa idonta, ahankali mahaifiyar ta ajiye phone dinta ta taka zuwa inda suke ajiyewa ta dauko mata, daga ind take kwance ta tura pad din gabanta ta Dan matse legs dinta, few minutes later alhaji bello ya shigo da sallama, amsawa sukayi,
"Ki shirya nayi Making arrangements da doctor victor...gobe ku tafi Chan adubata..." Yafadawa matarshi, Tana Jin Doctor victor tasan England né,
"Alhaji Tana iya long flight kuwa" Ta tambayeshi
"she will try..." Ya fada kuka na néman kufce mashi sai ya bar dakin, falo ya koma ya zauna yana cewa
"Who ever have hand in this will know no peace...ya Allah ka sakawa mufida ka sakawa family Dina.....ya rabbi ka wulakanta Wanda ya wulakanta rayuwar mufida..he should suffer more than she's suffering..." Yafada cikin hawaye. Itama mufida kuka ta dingayi Tana Danasanin yanda akayi ta jefa family dinta cikin wannan tashin hankali,
"Am sorry..." Ta furta cikin kuka,
"Wai mufida wannan am sorry din da kike cewa is getting me suspicious...tsakanin ki da Allah  kin San Wanda yayi maki wannan abun?.. If you know just say it...or ko ke kika Kai kanki?.. Because I could remember ranar bada amincewa ta kika bar gidan nan ba..." Ta fada idanuwanta kan mufida dake zubar da hawaye kaman tap,
"Aa mommy...kawai Ina bakin ciki halin da kuka shiga né..."
"Aikin banza...baki damu da halin da kika shiga ba sai halin da mu muka shiga?.. You're so undispicable ..." Tafada atakaice, bakinta taja ta rufe kar mom dinta ta gano ta.
Chapter 41 · 0% Book details