Sashe 4
Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
tafi..." "Ina usman..." Sufwan ya tambayi habib, "Nasan yana daf da shigowa...Yanzu na ganshi yace babanshi ya aikeshi layin jankai...amma daga chan zai zo nan..." Habib ya fada yana kwantawa kan katifar, ahankali sufwan ya Mike ya dauko Vaseline ya shafa Sannan yadauko wata neat blue yard ya saka, takalmin shi ya goge da old labulen bakin kofa ya saka, fita sukayi tare da habib sai suka hango usman karshen layin ya taho, jawo kofar sufwan yayi ya kulle, usman na zuwa suka gaisa Sannan suka nufi gidan shinkafa da wake, habib ya sayawa sufwan na 70 yaci Sannan suka bar wajen, "Nifa Allah na gani bazai yu Insha inuwar ceiling in dawo Ina saida garuwa ba...kawai mu nemi wani abunyi..." Usman ya fada not in support of abinda habib yace, "Me zamu nema Yanzu?... Ai munyi kokarin nema amma hakan baiyuba...kawai muyi garuwa in da rabon mu hole a gaba mun hole..." Habib ya fada, shidai sufwan baice komai ba, "Gaskiya aa...kawai I suggest mu cikin gari muna bin shaguna ko suna butatan maaika...kilan muci saa..." Shuru habib yayi ya kalli sufwan dake tafiya kaman Ana ingiza shi yace "Wai Kai won't you say anything?.." Habib ya fada cikin bacin rai, ajiyan zuciya sufwan yayi yace "Hmmm me Zance...kawai let's Allah's will be done..." Yafada cikn sanyinmurya, tafiya sukayi har cikin gari which takes them about one hour, wani katon shigo suka shiga sukayi tsaye suna kallon masu shopping, wajen Wanda ke zaune counter sukaje, habib yace "Dan Allah Ana samun aiki?.." Ya tambayeshi, Mutumin kallon su yayi from head to toe Sannan yace "Aa ba vacancy..." Aka amsa masu atakaice.