← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 162

Sashe 29

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Chest dinshi ya dafa yana sakin ajiyan zuciya da karfi, he can't believe this is how easy it is, kukan da yake ji a neighborhood dinsu bai dameshi ba, all he's thinking about is wannan makudan kudin da ya gani, it scares him, bai taba ganin kudi ko a film Mai yawan wAnda ya gani a dakin shi ba, sai da ya gama surprise breathing Sannan ya sake lekawa cikin dakin, sai gani yayi kudin yayi multiplying, idanuwa ya zaro kaman zasu fito waje saboda yanda gabanshi ke faduwa, this time shiga dakin da babu wajen saka kafa yayi Don ko Ina dakin kudine, da sauri ya maida Kofar ya rufe, yana nan tsaye kudi ya Kara appearing, ihu ya saki yana cewa
"Money..." Da karfi sai kuma yayi saurin rufe bakinshi kar ajishi, Allah ya taimaka da akwai hasken nepa so he can see clearly, zama yayi gabanshi na faduwa, sai kallon kudin da ke multiplying kawai yake, the money is too much, jiki na rawa ya dauki wayarshi ya kira number usman, ringing biyu usman dake chan yana tunanin who he's first victim will be yayi piçking,
"Usman nayi kudi...kudi everywhere..usman zo kaga ainahin kudi...original money..." Safwan Yafada kaman sabon shigan mad person,
"Am coming..." Usman Yafada atakaice Sannan ya katse wayar, safwan zama yayi kan kudin yana debo da both hands dinshi,
"Welcome to the world of classy people...na shigo gari...na shigo gari...you better watch your back..." Yafada yana zufa, more money was still coming, after kaman minti biyar yaji murya from nowhere ance
"Your sacrifice is accepted...welcome to the world of fame..." Yaji maganar kaman daga sama, ko kadan bai wani razana ba, some of the money is not Nigeria currency, ya dai San dollars but sauran bai San ko na wanne countries bane, da akwai at least 5 different currencies wajen, sai ware idanuwa kawai yake yana ganin he's a rich man already, duk bag dinshi ya dauko  ya bude su, kudin ya fara kwasa yana zubawa amma more is still coming, har ya gama deban dukkan kudin ya cika two bags din amma still da akwai sauran kudi and still wasu da appearing, a sauri ya Mike ya fita zai shiga cikin gida sai suka hade da Inna, kallon yanda jikinshi ke rawa tayi amma she didn't ask what's wrong with him,
"Inna Ina zuwa haka?..' Ya tambayeta gabanshi na faduwa Don he was thinking she heard he's screaming about money, kallon banza ta watsa mashi not minding yanda yake zufa and the guilt that  is written all over him tace
,"bakaji anyi rasuwa nan makota ba?..." Tafada Tana wuceshi fuuu kaman zata tashi sama, Dan tsayawa yayi ya bi Bayanta da kallo har ta bace mashi saboda yana tsoron kar ta shige dakinshi, sai da ta sha corner Sannan yayi saurin shiga cikin gida ya wuce inda Inna take ajiyan buhunna ya dauko Kato guda daya ya, yana kokarin komawa sister dinshi itama. Ta fito, kallon shi tayi from head to toe taga yanda yake zufa then jikinshi na rawa tace
"yaya..lafiya..." Tafada Tana noticing abinda mahaifiyar su ta kasa ganewa saboda rashin lura, Dan murmushi ya saki yana goge face dinshi yace
"Me kika gani?.." Ya tambayeta, kura mashi Ido tayi taga he's scaring her son dukda he's her brother and she loves him she can smell something fishy,
"Nima bansani ba.,amma duk naga ka firgice..." Wani irin kallo yau watsa mata before saying
"Ni mate dinki né da zakice na firgice...wai ubanme kike baki kwanta ba..." Ya tambayeta sounding so harsh,
"Rasuwa akayi Ai...yaya habiba ta rAsu...." Tafada mash kaman zatayi kuka, bai Kara cewa komai ba ya fice daga gidan rike da buhu sister dinshi tabi bayanshi da kallo yana mamakin abinda yasa ya koma haka kaman wani sabon shigar mahaukaci, safwan na fita usman na zuwa, lokacin shadaya saura amma saboda rasuwa da akayi da akwai mutane saboda duk mutuwar yarinyar ya tada masu hankali sosai, inda mutane zasu maida hankali ga safwan da usman da nan take za'a gane something fishy is happening Don while some people where busy discussing abinda ya samu yarinyar su kuma suna ciki sun rufe kowa sai kus kus suke,
"Wai ance yarinyar ta rasu..that means duk wacce mukayi amfani daita will not survive..." Inji usman, safwan ko sauraron shi baiyi ba sai kwace kudi yake yana zubawa a buhu, a ranar duk unguwar basuyi bacci ba sai very few da basu da human feelings, uwar yarinyar kam sai suma take Tana farfadowa because she can't believe her daughter is gone, safwan na tashi da asuba dukda sai 4 bacci ya saceshi yayi saurin duba buhun kudinshi da kuma bags yaga it's not a dream it's real, fita yayi yaga rana ta fito duk an shimfida mats  Kofar mahaifin yarinyar, da sauri ya fita ya shiga cikin gida, Inna na zaune tsakar gida ta bishi da harara har ya shige bathroom Tana hararanshi, yau ko irin gaisuwa daya sabayi mata Ta amsa a wulakance bai yi mata ba, fitowa yayi da bucket zai debi ruwa tayi saurin cewa
,"kull...kar ka kuskura ka debi wannan ruwan...yaushe rabo daka debo ruwa gidan nan?.. Kai Yanzu ka girma Ai..." Tsoki yaja ya ajiye bucket din, Inna ta bude baki tace
"Ni kake jawa tsoki?.." Ta fada afusace Tana kokarin mikewa, da sauri ya bar compound din  Don yasan in har ya tsaya he can strangle her to death, da yana fushi amma na Yanzu ya linka na da, he easily get angry and in yayi fushi sai yaji he's becoming uncontrollable,
"Da ka tsaya inci uwarka shege matsiyaci..." Tafada, yana jinta ya sake Jan tsoki yana cewa
"Let's see..." Yafada yana shigewa dakinshi, wayarshi ya dauka ya Kira alhaji idris ya Sanar mashi abinda ke faruwa,
"Zan aiko da mota anjuma a daukeka da kudin,ka samu waje kayi counting sai a samu gida ka saya yauyau din nan..." Ya fada mashi
"Ok..amma za'a yi janaizar yarinyar...in an gama sai in kiraka..." Safwan ya fada mashi yana zufa,
"Ok babu matsalar..." Ya amsa mashi, Kaya safwan ya dauka ya saka ya fito waje, bayan kaman minti ashirin da zamanshi aka fito da yarinyar tare dashi aka sallaceta aka kaita makwancinta, yana zaune wurin amsar gaisuwa yana Jin yanda mutane suka dinga cewa
"Ai gamo tayi.,shiyasa babu kyau aiken yara mussanman mata bayan magrub..." Yaji suna ta maida yanda aka yi..

Yau bayan nana ta shirya in a sexy gown Wanda bai wuce 3k ba tayi rolling kanta ta zauna ta tsara makeup dinta da kanta ta fito tayi kyau sosai, bag dinta ta dauka ta fito Don daman Maryam ta dade da tafiya lecture kuma daman tunda suka dawo hostel basu taba tafiya school area tare ba saboda yanda nana ke behaving yana damun Maryam sosai amma ko advice ta bata sai ta datsa mata magana Wai Ina ruwanta, jiya ma haka bayan ta gama lecture ta dawo hostel ta dau wanka ta fita da Maryam ta tambayeta inda zata sai tace iska zata sha, haka ta tafi sanye da Kayan that's almost nothing,  kawai ita gurin ta taci kwalliyarta ko Allah yasa ta hadu da wani big boy, she's so much in love with fairytale life, she thinks kawai good looking, handsome, hot guy will come from nowhere and just marry her, or date her, yanda take yi a hostel Baka taba tunanin yar civil servant ce because ta kashe kudin upkeep dinta for wears. Tana fita ta kulle kofarsu, daya daga cikin matan da suka taba maganar ta nufota Tana cewa
"Excuse me..." Ahankali nana ta juyo ta kalleta,
"Hi.." Itama Ta amsa mata sounding nice, karasowa matar tayi tace
"Yanmata ya kike?.."
"Lafiya lau..." Nana ta amsa mata Tana ajiye keys a bag dinta,
"Kawai I want to tell you tunda kika dawo hostel din nan I like you swag...dukda ke ba mate dina bace I will want us to be friends..." Matar ta fada, murmushi nana tayi Wanda ya sake bayyana beauty dinta
"Amma anty nagode...na gode sosai..." Tafada Tana murmushi,
"Yauwa..." Matar dake sanye sa jeans Wanda ya matse ta sosai  Sannan Tana sanye da just singlet kuma da ganinta kasan first class bitch ce, amma nana bata damu da yanda take ba, asalima she loves people with class da effizy,
"Pls can I have your number? " Inji matar,
"Eh mana..why not..." Ta amsa mata, hannu mata ta saka bayan Jean dinta ya dauko iPhone x da ke cikin aljihunta saka number nana Sannan Tayi mata flashing, yar small phone din nana yafara ringing ta Fiddo ta,
"Wannan itace wayarka ko kina da wata?.." Matar ta tambayeta,
"Itace wayata..." Nana ta fada mata Tana kokarin storing number  gira daya ta daga Sannan tace
,"store my name with big mama..." Inji matar, babu gardama tayi storing Sannan tace
"Anty zan tafi...lokacin lecture ya kusa..." Nana Tafada mata,
"Ok ba matsala.....zan kiraki bayan lecture...hope zakizo dakinmu?.."
"Eh mana..." Inji nana,
"Good...ayi karatu lafiya..." Big mama Ta fada mata Sannan ta juya itama nana ta tafi cikin ranta sai dadi take ji she's coming close to classy people, San ajinta ba ga Maza kawai ya tsaya ba , har mata indai suna da class tanason su.
Chapter 29 · 0% Book details