← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 162

Sashe 7

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Shi kam habib yana zuwa gida sai da ya kusa fashewa da kuka saboda yanda mahaifiyar shi ke kwance kan taburma a yar karamar compound dinsu, idanuwanta lumshe kaman Mai bacci amma she's not sleeping, she's just hungry, Tana Jin sallaman shi tayi saurin bude Ido tare da mikewa zaune, duk ilahirin jikinta sai kyarma take saboda yunwa, idanuwanta duk sun koma ciki, ahankali ya ajiye Kayan hannunshi nana cewa
"Murja..." Ya Kira sister dinshi, da sauri ya fito, kallon mahaifiyar shi yayi yace
"Mama baki Jin dadi né?.." Ya tambayeta eyes dinshi na Chanza launi saboda bakinciki da tausayinta,
"Yunwa..." Tafada Tana nuna stomach dinta, da sauri ya mikewa sister dinshi Dari biyu yace
"Yi sauri ki sawo biredi..." Ya umarceta, da sauri ta amshi kudin  ta dauko hijab ta fita, mom dinshi jingina tayi da bango Tana sauke ajiyan zuciya kaman Mai asthma, hannunta ya Kama yana shafawa ahankali
"Mama Insha Allah sai kinci gajiyata ko ta halin kaka...sai na sa ki cikn makeken gida da masu aiki.." Yafada hawaye na taruwa idanuwanshi,
"Ameen..." Kawai Ta amsa without opening her eyes, suna haka sister dinshi ta shigo da bread din, da sauri ta amsa ta bude ta fara ci, kallon murja yayi yace
"Ina sauran.." Ya tambayeta
"Suna makota..." Bai Kara cewa komai ba ya sa hannu cikin aljihunshi ya dauki Dari biyar yace
"Maza kiyo cefane Sannan ki sayo itace kizo ki dafa abinci..." Ya umarceta, babu musu ta amsa ta bar gidan. Sai da taci bread din ya debo mata ruwa cikin randa Tasha sanna ta saki ajiyan zuciya tace
"Allah yayi maka albarka...nagode.." Tafada cikin sanyinmurya, murmushi ya saki before saying
"Mama kalli.." Ya fada yana nuna mata Kayan Abincin daya shigo dashi, juyawa tayi ta kalli Kayan ta zaro idanuwa
"Ina ka samesu?.." Ta tambayeshi sounding so excited, nan Yafada mata yanda akayi
"Allah ya saka masu da alkhairi..Allah ya biyasu..."Tafada cikin farin ciki, this is the difference between mahaifiyar sufwan da na habib, she appreciates duk abinda danta yayi, kullum cikin yaba mashi take,  shi kam usman ya tarda abinci gida, sai da yaci ya koshi Sannan ya dauki 2k cikin kudin ya bawa mom dinshi, adua ta dinga jera mashi saboda farin ciki.

Nana kam tana  gama girki ko ci batayi ba ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya ciki. Lace Riga da skirt, brown vail tayi rolling dashi ta dauki bag dinta irin na yanmata ta fito zuwa dakin mom dinta,
"Zan tafi..." Ta fadawa mom dai ta, pause dake kusa daita ta bude ta dauko Dari biyar ta mika mata Sannan tace
"Sauran ki dinga gantali a titi...nasan halinki da son yawon banza..." Ta fada mata,
"Mommy gidansu Maryam kawai zanje sai mu wuce school..."
"Na dai fada maki..." Ta amsa mata atakaice Sannan ta fita jikinta na rawa, takawa tayi Tana sauri zuwa bakin titi, sai kallon flashy cars dake wucewa take Tana imagining inama wani daga cikinsu ya tsaya yace zai bata lift da dagudu zata shiga, she loves class and  riches, wata shiny car yaso wucewa ta kurawa motar Ido tayi har yazo wucewa ta inda take taga wani young guy da wata babe zaune a gaba
"Inama ni..." Tafada Tana biting lips dinta, ganin in ta tsaya kallon cars she won't go yasa ta tsaida adaidaita ta hau zuwa gidan su Maryam daga nan suka wuce buk, luckily ita da Maryam sun samu admission, tsalle ta dingayi Tana ihu not minding mutane dake kallon ta,
"Wai meye haka Dan Allah?.. Kar ki Bari mutane suyi tunanin am together with a mad person mana..." Maryam ta fada mata amma nana bata bar tsalle ba sai cewa take
"Wallahi su kalleni it's their business...you won't understand what am feeling..kawai I can't wait to get out of that house...." Tafada sounding carefree,
"Ke kam you're funny...you can't wait to get out of that house kaman ba gidan ubanki ba?.. Kaman dafa ki ake Ana ci?.. Haba nana ki bar wannan maganar mana kar wasu sujiki..." Maryam ta fada mata calmly,
"Ai inda dafa ni ake Ana ci da yafi min..kullum a wahale nake kaman wata baiwa...Wallahi ko kadan bani da Hutu gidan nan...from this to that haka nake rotating cikin gidan kaman Mara galihu..." Tafada hankalinta kwance,
"Hmmm ke kam Ai iyayen mun Don su bamu tarbiya Mai kyau suke hakan..bawai Don basu kaunar mu ba...ba ki ganin yanda wasu yanmata basu iya zaman aure saboda basu iya komai ba?.. Ai in uwa ta koya maka komai to ta tsirar dakai daga cin fuska nan gaba...ki tuna in dai da rai da lafiya aure zamuyi fa.." Ta fada mata Tana Dora hannu kan shoulder dinta,
"Ke dai baki ganewa Wallahi...inda na nufa daban inda kika dosa daban...kawai nidai I want be free ko da na months né...in zauna babu takura babu command...because kaman yanda kika ce aure zamuyi so Yanzu in ban Dan shana ba babu ranar shanawa saboda bakasan Wanda zaka aura ba...daga takurar iyaye zuwa miji...no freedom kenan fa..." Nana Aisha tafadawa Maryam
"Wai to in tambayeki wane irin shanawa zakiyi...hope it's not what am thinking...badai runs girl kike son komawa ba..." Bata karasa ba nana ta balla mata harara tare dacewa
"Ke kika San abinda hakan ke nufi...nidai kawai I want freedom...that's all I don't want to go from fry pan to fire..." Tafada Tana juyawa
"Allah ya huci zuciyar ki...kawai you should know what ever our parents do is for our own good..." Maryam ta fada Tana biye daita,
"Kanki akeji..." Tafada Tana tafiya da sauri sai sai wining waist dinta take in the name of walking, itama bayan ta tabi trying to keep up with her.

Share thanks 3💜💚💛💙❤️
Sirrin wasu gayun...
💜❤️💛💙💚

® zuwairat (ummumaryam)

3️⃣

Free page

Har suka hau adaidaita aka ajiye Maryam nana bata Kara ce mata komai ba,
"Sai munyi waya..." Maryam ta fada mata Tana sauka daga adaidaita amma ko inda take nana bata kalla ba balle ya amsa mata wai ita she's angry because if what she told her that's absolutely true.
Chapter 7 · 0% Book details