← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 162

Sashe 151

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wata biyu rabia ce tsaye tana rike da yaran biyu Dr kuma na rike da biyu, bakin gate suke suna mashi bye bye, alaman tafiya zaiyi, ajiye na hannun shi yayi suka koma wajen mahaifiyar su, kallonta yayi yace
"wai kema daga nan zaki koma?.. "yafada kaman zaiyi kuka, Dan dariya tayi tace
"AI gani nayi ga motarka nan tsaye. In kuma kanason in kara raka Just say it..."
"eh inason ki k'ara rakani..."yafada mata, kafa daya ta sako waje yayi saurin cewa
"no... Ki maida su gida.. Ke kadai zaki rakani.. "babu musu ta kira wata sister dinta ta shiga da yaran ciki, fita tayi ta rakashi har cikin motar ya shiga tana tsaye waje, ahankali ya leko yace ta shigo babu musu ta shiga, kallon ta yayi yace
"kinsan ina missing dinku especially you sosai... Wallahi kaman in maidaku chan gidan inda zandinga ganin ku kullum haka nake ji... " yafada looking at her kaman he's seeing her for the First time,
"lallai yaya.. Ka so kanka da yawa... Duk weekend fa muna ganin juna... "
"yea I know...amma at that time kullum muna tare AI... " ya fada mata, shuru tayi just wearing a smile, shuru yayi for a moment sannan yace
"hmmm yanzu an San dadin yara.. Nasan ko tafiya bazaki so yi ki barsu ba... "yafada calmly,
"nikam inama zani balle in barsu... Ai ina gida always... "ta amsa mashi.
"ai tafiya na iya kamaki Wanda zai zama dole ki barsu... " da sauri tace
"kam yaya kenan.. Nikam ina zani?... "
"misali gidan miji fa? " Yw tanbayeta looking at her reaction, shuru tayi for a moment duk yanayin ta ya sauya, ajiyan zuciya ta saki tace
"yaya aure fa... Hmmm"ta amsa Kai tsaye cikij sanyimurya
"eh mana... Bakison aure ne?.. "ya tambayeta
"yaya you know haka nan kake zolayata da wannan maganar aure... Ni yanzu yaya who will marry me... Who will give someone like me a second chance... Wa zai bani daman samun wannan ladan... " tafada kawai sai hawaye, ita da gaske gani take nata ta kare and nobody will want to be with her as wife anymore Kai ya girgiza tare da lumshe idanuwa yace
"baby you're not that bad..."rufe face dinta tayi tana hawaye tana cewa
"aa... Nawa ya kare.. I have no second chance.. No body will give... "bata k'arasa ba yace
"I will... "yafada cikin sanyimurya, shuru tayi Don taji abinda yace
"yes I will give you a second chance... Zan aureki if you find me worthy of being with someone as special as you're.... " sakr kulle face dinta tayi gam tare dacewa
"pls yaya ka daina... Wannan wasan babu dadi... Pls.."tafada cikin hawaye,
"no baby ba wasa nake ba... Tun ranar dana fara ganinki na yaba da halinki.... I was like wow wish she wasn't knocked by another man... Amma still because you're special hakan bai sauya komai daga son da nake maki ba... Pls am serious.. It's not out of pity nakeson ki... It's out of love... "yafada in a sweet tune da bai taba mata amfani dashi ba, kuka kawai take tana kara volume din kukanta tana sauraronshi da wannan kalamai masu dadi da bata taba tunanin zataji su daga bakin wani namiji ba balle a unique and cute person like Dr salim bello tanimu,
"baby I love you... Pls... "ya sake fad'a mata yana kama hannunta dake face dinta, kissing hannunta yayi yace
"pls princess marry me... "yafada cikin whisper,
"Dan Allah... Da gaske kake?.. "ta tambayeshi, da sauri ya daga mata kai yana cewa
"yes my angel... "
"you will marry for real?.. "ta fad'a without any pride na yanmatan zamani
"yes I will marry you... Ke zaki aureni?. "ya tambayeta sounding so sweet
"yes..zan aureki.. You're among my joy and happiness... Seeing you give me total satisfaction..." yafada hannunwanta biyu cikin nashi
"pls don't joke with such thing... "tafad'a cikin hawaye sosai,
"Nima ba wasa nake ba... "
"nagode... "da sauri ya dora hannu kan bakinta, hannunshi ta zare daga bakinta tace
"na fidda rai ga rana irin ta yau... Allah have given me a second chance... Nima na yafewa safwan... "yafada cikin kuka, idanuwa ya lumshe wearing a smile sannan yace
"Allah bless you for your golden heart....naji dadin wannan statement.... Allah ya biyaki da kika San komai na da silah nor matter how good or bad.. Komai da zai faru yana da reasons... " yafada cikin calmness,
"na yarda... Komai na da reason...i met someone special because of him... Someone da bani da dream din gani a rayuwa... "dariya yayi yace
"am I really special da zaki ce baki da hope din ganina? "murmushi ta saki with wet face dinta sannan tace
"yes you're... Ba kowa zai samu daman ganin mutum irinka ba... Ta Kowacce fuska you're extra special... "tafada tana rufe face dinta, murmushi yayi ta kara dacewa
"thank you... " ta fad'a sounding so happy
"another reason why j love you... You're straight forward and always say everything straight from your heart... But stop thanking me because bani nake maki favor ba ke kike min favor because without you I won't be complete...so nake Nima ki jera min yan hudu... "yafada yana daria, haka suka dinga hira har lokacin b'ata bar mamakin abinda ke faruwa, gani take kaman she's dreaming Don kawai ji take kaman ta ruga cikin gida ta fad'a masu abinda ke faruwa. Sun fi hour suna hira sannan ya tafi yana cewa
"Bari inje in rarrshi uwar gida... " yafada looking so happy, Dan marairacewa rabia tayi before saying
"Allah yasa ta yarda... Wallahi zanyi mata biyayya... Kome tace inyi zanyi.. Nima in samu ladan aure pls... "tafada kaman zatayi mashi kuka, dariya kawai yake looking si excited, at least Allah yasa rabia b'ata da abinda ya tsana most a rayuwar yanmata, that's rashin yanga da boye feeling,
"Karki damu... Amma Nima fa kome nace kiyi zakiyi... Babu gardama... " yafada yana lumshe idanuwanshi, da sauri ta boye face dinta tana dariya.

Yanzu kam safwan yayi wata biyu da sanin bai Haihuwa, Mai cutar HIV MA ya fishi Kyauwun gani, ya rame ya kare tas, meeting na farko da akayi baije ba shigabansu yayi Warning kan in baizo ba next gidanshi zasuyi meeting, hakan yasa yaje na wannan watan, he was happy mutane biyu data ciza are dead, kawai yana kallon yanda zai iya kashe wannan shugaban amma ko kadan bai da halin hakan, bai iya zuwa da wuka ya kasheshi, kawai he's so mad and yasan it's meant to be, ya gaji da shiga hakkin matanshi dayake, he needs to tell them shine baj Haihuwa, kawai he's afraid kar Nana ta barshi, baisan yanda komai zai kasance ba if she left, he's not enjoying he's wealth and he's a little bit happy because of her, in ya ganta nan take yake mance da pain dinshi, last month tayi kuka sosai dataga period dinta, saboda tsoron kar ta rabu dashi yasa ya kasa fadawa baraka he can't have a child, yasan if she knows Nana zata sani, yau kam he will come to term, he will tell them the truth, gabanshi na faduwa sosai but dole ya ajiye selfishness gefe guda, he really have to face he's fear, ko kadan bayason tayi kuka wannan wata because her period is coming soon, sanye yake cikin jallabiya looking so tired and lean, kaman bashi ba, wani Mai HIV din yafishi kyau da cika, duk ya zaizaye kaman bashi ba, a hakan MA it's because he have Nana to reduce he's pain. Ahankali yana tafiya kanshi kasa ya nufi part din baraka, falo ya tardata Tana kokarin tashi ya shigo, gaidashi tayi ya amsa mata yana zama, abun sha ta dauko mashi ya amsa ya ajiye gefe guda ya zauna ya natsu ya fad'a mata Dr sunce bai haihuwa, tana jin wannan statement din rashin Haihuwa tace
"tab... Ashe kaine Mai matsala...to da sauki AI tunda bamu bane masu matsala... " tafad'a ahankli,
"yes.. Congratulations... It's not you... Don haka nazo if har you want to go zan. Sauwake maki yanzu without delay. It's not because I don't csre but it's because banason in shiga hakkinki... In kuma zaki zauna saboda luxury life shikenan.. I will give you all in my power... "yafada cikin sanyimurya,
"kam lallai... Gaskiya gani nake there's no about of lurury Da mutum zaiyi comparing da Haihuwa... Kaman ni yanzu inason Allah ya bani baby da zan kira da aisha... Don haka bazan zabi luxury kan yara ba... "wannan statement yasa safwan kwalla, tunawa yayi da yanda ya Kasheta,
"am so sorry... "tafada ganin yana kuka
"aa.. Nine zance sorry... Nine mugu Kuma ko kukan jinj zanyi ko ace wuta zai fito daga idanuwa na bai isa ba.... Pls am sorry... Na sake ki saki daya.. Biyu... Uku... Go and find happiness baraka... Thank you for putting up with a monster like me... "da sauri ta rungume shi, Shes so happy about it, dukda tasan she will miss him but she don't really care if he dies, kawai wannan tsana da tayi mashi for no reason is in her and yana damunta, she tries so much to love him amma Allah baisa ba, yana cewa ya saketa taji wani irin iska all over her body, bayan kaman minti ashirin ya Mike ya fita yana goge face dinshi ya fita ya Kama part din Nana gabanshi na muguwar faduwa, bai San how long ya roki Allah yayi mashi wani abu ba but yau he prayed that Allah ya dauke komai daya mallaka amma kar Nana ta barshi.

Jamaa ina wayanda basu sayi rain soul ba, pls I urge you to give it a try, rain soul it's a whole health in a sarchet, duk wata ciwo Insha Allah tana healing in har kana da halin sha yanda ya kamata, in short har cancer yana healing da yardan Allah, har dasu infection dayayi yawa a jikin mata, I can't list abubuwan da rain soul keyi because suna da yawa. For info contact 08063328903

Thanks61🧡❤💚💜💙
Sirrin wasu gayun
❤💚🧡💜💙

®Zuwairat (ummumaryam)

6⃣1⃣
Chapter 151 · 0% Book details