← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 162

Sashe 27

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Number Immediate younger sister dinshi ya fara dialing sai akayi sallama Kofar gida, da sauri ya katse ya leko waje, alhaji labaran da Maigadi alhaji Ibrahim né tsaye waje,
"Yauwa sannunku dazuwa..." Yafada masu,
"meye dalilin da yasa zaka saida gidan nan?.." Alhaji dake tsohon abokin dake tsohon abokin abban Habib ya tambayeshi cikin  girmamawa yace
"jalli san ja da kudin...zamu koma kauye ni kuma in dinga zuwa kasuwanci cikin birni..."dukda yasan nan da sati biyu in har bai aikata abinda aka Sashi ba mutuwa zaiyi,
"Eh gaskiya Kayi dabara...hakan ma yayi...Allah yasa hakan shi yafi alkhairi..." Alhaji
Labaran ya fada mashi
"Ameen..." Habib ya amsa mashi
"Tou mu shigo mu duba kou?.." Inji maigadin alhaji Ibrahim,
"Eh bisimillah ..ku shigo.." Ya fada yana komawa ciki, sum binshi sukayi har cikin gidan habib yace
"Mamanmu Anzo duba gidan..." Yafada mata da karfi, mamanmu dake ciki Tana shirya yan kayanta ta saita voice dinta before saying
"Tou ba damuwa..." Ta amsa mashi Tana cikin Daki, alhaji labaran bai wani duba gidan sosai ba saboda yasan gidan in and out,
"Gaskiya gidan nan zaiyi dubu Dari bakwai..." Yafadawa maigadin alhaji Ibrahim,
"Tou muje mu fadawa alhaji..." Inji maigadin  fada yana juyawa
"Tou shikenan..." Habib ya fada yana bin bayan shi, habib sai zufa yake yana firgita Don ji yake kaman Ana binshi a baya, suna zuwa maigadin da Alhaji labaran da habib suka shiga wurin alhaji Ibrahim, nan maigadin ya fada mashi nawa akayiwa gidan kudi, ashar ya saki Sannan yace
"Lallai ma...cikin wannan lungun ta baya za'a samu gidan dubu Dari bakwai?.. Haba bazai yuwu..gidan da dabbobi zan zuba ciki?.." Yafada sounding so angry,
"Haba alhaji..ai wannan kudin fili né...nan fa ba kauye bane..." Alhaji labaran ya fara fada mashi amma bai saurareshi ba yace
"Tou meye bambamcin gidaje su Dana kauyen?.. A ba wuri né kauye ba...yanda gidan da mutanen ciki suke shine ke determining in waje kauye né ko birni...for as long as am concerned duk gidajen nan baya gidajen kauye né..so to cut it short zan bashi dubu dari biyar shima don yace jalli zaija...in yayi in shiga ciki in dauko..in kuma baiyi maka shikenan,.." Ya fada atakaice, alhaji labaran zai bude baki yayi magana habib yay saurin cewa
"Ka bada..Allah yasa masu albarka..." Yafada mashi, alhaji Ibrahim mikewa yayi ya shiga ciki bayan kaman minti biyar ya fito da mint din 1k guda biyar sai  ya wullawa habib su sai kuma dubu biyar ya mikawa alhaji labaran na dilalanci, da sauri habib ya Mike ya tura kudin cikin aljihunshi yana tunanin Yanzu wannan Mutumin yana da irin wannan kudin a gida amma sai da suka dinga zuwa ya taimakesu ya rufe Ido ya nuna baisan zancen ba, tunAwa yayi da yanda safwan ke shaawan daukan fansa kanshi and he's sure in har safwan ya shiga wannan cult din zaiyi maganin alhaji Ibrahim because he knows Safwan sosai,
"You will get what is coming to you..."Habib ya fada yana barin gidan, yana kan hanya ya fiddo wayarshi yayi dailing number sister dinshi, bayan tayi piçking ya fada mata ya saida gida zasu koma kauye da su mamanmu Sannan ya fada mata zai bar dubu ashirin a bata a neighbor kuma yaja mata kunnen kar ta kuskura ta fadawa kowa inda zasuje, yace ko su safwan yazo néman shi kar ta fada masu, haka dai sukayi sallama ya Kira ta biyun data ukun duk ya yayi masu wannan kashedin kuma ya ajiye masu 20k each, gida ya koma ya tarda mamanmu ta fiddo yan Kayan su har da katifa,
"Mamanmu Dan Allah kar ku dauki duk wani Abu cikin Kayan da na kawo gidan kwanan nan..Dan Allah har Kayan sanaar da kika fara ki barsu..." Yafada kaman Wanda ke néman zarewa, mamanmu batayi mashi gardama ba ta ajiye duk Kayan da yayi magana a Kai, shima cikin dakinshi ya shiga Don tattara yan kayanshi, the most important thing da yake dashi a dakin shine certificate dinshi, cikin bag dinshu ya shiga don fidda kayan da ya saya da kudjn jini. to hes surprise sai yaga wannan yadin da aka bashi da anambra, the last thing he remembered was that ya bar shi a cikin motar alhaji idris, ko fita baiyi dashi ba amma sai ga yadin cikin bag dinshi, ihu ya saki yana cewa
"Leave me alone..." Yafada da karfi yana fitowa da yadin a hannunshi, mamanmu dake niyyan shiga dakin ja dayi da baya Tana kallon abinda ke hannunshi, direct bathroom dinsu ya shiga ya tura Kayan cikin toilet,
"Na shiga uku...Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Mamanmu Tafada Tana kallon habib dake néman zarewa,
"Menene Dan Allah modibbo?.. Ni mahaifiyar kace..ka fadamin abinda ke faruwa...bazan taba juya maka baya ba..." Tafada Tana kallon habib dake tsaye gefe daya yana nishi kaman Wanda yayi race,
"Mamanmu ki kwantar da hankalinki.." Bai karasa ba tace
"kar ka Kara cewa in kwantar da hankalina....ni ba mahaukaciya bace...Yanzu ka fadamin abinda Ke faruwa?.. Ina kukaje?.." Ta fada zata zauce saboda tasan danta is hiding something very huge from her, kuka Habib ya farayi yana tausayinta Sannan yana tausayin kanshi, kawai danasanin bin instinct dinshi kawai yake, yasan inda yabi feeling dinshi tun farkon haduwansu da alhaji idris da Yanzu bai shiga wannan matsalar ba,
"Mamanmu ban iya fada maki...in na fada maki mutuwa Zanyi ..." Yafada cikin matsanacin kuka Wanda yasa sisters dinshi kuka suma, sai da yayi Mai isanshi Sannan ya bawa sister dinshi dubu sittin ya umarceta data shiga neighbor wayanda suke mutunci Ta fada masu su ajiyewa su salaha Sannan ya ja mata kunnenta kar ta fada masu zasu koina, bayan ta dawo suka fidda kayansu duk mutane sai tambayansu suje inda zasu amma habib ko kallon su baiyi ba balle ya amsa masu kawai burinshi ya bar unguwar.

Su safwan kam bacci suka dingayi all through the way saboda sun kwana aiki, alhaji idris kam kurawa titi Ido yayi yana tuki hankalinshi kwance, sai da sukazo Abuja suka bukaci suci abinci, tsayawa alhaji yayi a best restaurants by road side suka ci Sannan suka cigaba da tafiya,

Karfe hudu habib da family dinshi suka isa wata har karamar kauye wato kauyen su Fatima Mai sayar da awara, daman Fatima cousin sister din habib ce, baban habib Shine wan baban Fatima, lokacin da mahaifin Habib ya rasu sunyi iya kokarin su do in su dawo kauye amma habib ya rufe idonyace baisan zancen ba, hakan yasan abban Fatima ya rabu dasu, gidan Iyayensu na nan kusa gidan abban Fatima Wanda Yanzu babu kowa ciki sai kakarsu mace. lokacin Fatima ta dawo daga tallanta ta hangi mota daya shigo garin, abinka da yar kauye tsayawa tayi yana kallon motar Sannan Tana kallon Kayan dake saman motar Sam habib bai gane ita bace Sannan mamanmu dake cikin tashin hankali bata daga idanuwa ba balle taganta, motar na wucewa taga kaman habib tayi saurin cewa
"Yaya modibbo..." Ta kirashi da karfi lokacin motar da sukayi chata daga park na néman tsayawa, Dan juyawa yayi ya ganta, murmushi ya saki yana kokarin fitowa daga cikin motar, da gudu ta taho zuwa kusa da motar Tana kallon su happiness rubuce kan faces dinta,
"kam ke wane irin girma kike haka?.." Yafada yana kallon how grown she is, rabonshi da kauyen haifi shekara ba amma she has changed, Fatima bata tsaya ta kansu ba ta ajiye robar awarar ta daya rage Dan kadan ta shige gidansu da gudu Tana kiran abbanta da mamanta su fito ga su yaya modibbo, da gudu suka fito suna kallon su, baifi minti uku ba wurin ya cika da yan kauyen suna masu Sannu da zuwa, abban Fatima look so excited that family din wanshi sun dawo gida, kakar shi fitowa tayi da sandan ta Tana dogarawa ta nufosu, mamanmu kam dariya kawai take wa mutane amma deep inside she's so full of sorrow, a wannan moment din kam habib mancewa yayi da matsalar rayuwar shi Don the people are so welcoming, duk Wanda ya gan habib sai yayi maganar mahaifin shi wai suna Kama dayawa, ahaka aka shige da kayansu gidan kakarsu sai maraba ake masu, maman Fatima bata b'ata  lokaci ba ta shige gidan ta ta fara hada masu abinda zasu ci, mutane cika gidan tsohuwar sukayi suna tambayan su wai da gaske shikenan sun dawo kauye da zama?. In Habib ya amsa masu da eh sai su fara murna, kunsan yan kauye da Kara da kuma hadin Kai, before 5 na maraice an kawo abinci kala kala, daman  rabon habib da abinci tun Wanda yaci a restaurant din da alhaji ya kaisu before ya gane ko shi waye, Abincin da Fatima ta kawo ya jawo gabanshi yaci ya koshi, duk yana Lura da mamanmu da duk ta fita hayyacinta, he wish he can tell exactly what happened, amma that will not help matters saboda yasan yana furta word daya zai mutu, yasan rai a hannun Allah yake amma those people are dangerous beyond words, he remembers yanda ogan ya dinga amayo zobe daga cikin bakinshi yana mika masu, and yanda wannan abun daya basu ya dinga tahowa from no where yana appearing a hannunshi.
"Mamanmu dan Allah kici abinci..." Yafadawa mamanmu data sha tagumi, ko kallon inda take batayi ba balle Ta amsa mashi, abban Fatima ne ya shigo gidan ya samu wuri ya zauna tare da kiran habib.
Chapter 27 · 0% Book details