Sashe 2
Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani saurayi né zaune cikin wata lungu sai kuka yake while wasu guys guda biyu na rarrashinshi, da wannan ya taba shoulder dinshi sai ya tureshi da wancan ya taba shi sai ya tureshi "Wai haba meye haka?.. Sai kace ba namiji ba?.." Inji daya daga cikin samarin, "Pls ku kyaleni Inyi kukan...ko na fi samun sauki azuciyata...eight years muna tare da khairat amma rana tsaya za'a rabani daita Don an gan ban da kudi..." Saurayin ya fada cikin matsanacin kuka, "Ai sai ka dauki hakuri...komai sai in Allah ya kaddara...kilan ba itace matarka ba..." Dayan saurayin, idanuwa Mai kukan ya daga ya watsawa Wanda yayi magana harara tare dacewa "Haka ma zaka ce?...tou Yanzu bani kudin néman aure in Kai in ba'a bani ba?.. Kawai talauci na yasa na rasa khairat..." Yafada still crying, "Pls safwan kayi hakuri...komai sai in Allah ya yarda ake yinshi...kar ka tada hankalinka..." Inji Dayan, "Pls ku rabu Dani...kawai ku tafi ku barni...you guys won't understand how am feeling...mutuwa ta fi mun komai a Yanzu..." Safwan ya fada cikin kuka, "Nikam nasan yanda nakeji...ba two months ago akayiwa aliya aure ba?.. Kowa yasan Ina kaunar Aliya amma haka na hakura tunda bani da Abunda zan bata in na aureta...ni saida ya kaiga in yan gidan sun ganni sai suce sun rabu da matsiyaci....kawai muyi hakuri..in Allah ya kawo aiki zamu samu wayanda zasu auremu..." Inji daya daga cikin su Mai suna usman, "Yau she zamu samu aiki?... Whole three years da gama degree babu aiki...in mutum baiyi karatu ba ace Don bai da ilimi gashi munyi hustling munyi karatu amma no body is willing to help us and give us a job...Yanzu sai Mai long leg ke samun aiki..." Habib ya fada cikin tsananin bacin rai, "Ai naka is better...tunda uncle Dinka yana da Hali..." Habib ya fadawa safwan da har lokacin bai bar kuka ba, "Kodai muje wurinshi mu rokeshi ko zai taimaka ya Baka kudin da za'a Kai gidansu khairat?.." Usman yafadawa safwan, sufwan daga red eyes dinshi yayi yace "Kawu musan da ko zamu mutu da yunwa bai taimaka mana?.. Shi zai fadawa ya bani kudin néman aure?... Gaskiya ban iya Kai Kaina in sha zagi da yamman nan..." Sufwan yafada cikn bacin rai, "Amma wannan uncle din naku baiyi ba...haba Dan Allah...bai da tausayi ko kadan..." Inji habib, "Ai ni ba tun yau ba nasan bai da mutunci..remember lokacin da ya ganmu mun dawo daga school shi kuma ya dauko yaran shi amma yaki rage mana hanya..hmmmallah dai ya kyauta...kilan yana tunanin mu muka darawa kanmu talauci..." Usman ya fada, shi dai sufwan bai Kara cewa komai ba saboda abinda ya dame shi da ban, kawai he's missing the love of his life, kawai Yanzu yana tunanin saboda bai da kudi ya rasa komai, he loose his two sisters because basu da kudin da zasu biya hospital bills dinsu. Ajiyan zuciya ya saki yana lumshe idanuwa while best friends dinshi suna magana kan habit din uncle dinshi, ahankali ya daga Kai ya kalle friends dinshi yace "Wai yasuhe wannan wahalal zata Kare?... Yasuhe muma zamuyi arziki kaman sauran mutane?... Yaushe zamu samu daraja a idon mutane..." Duk ya jero masu wannan questions din, ahankali Habib yace "Mu dai kam ya zaayi muyi arziki?... Wa zai taimaka mana?... Masu kudi kansu kawai suka sani...kalli makocinmu ko zakka bai fiddawa...last Ramadan da akwai days da bamu samun wani abun kirki muyi buden baki amma su dadinsu suke ji...Kai duniya..Wallahi am tired..." Usman yafada kaman zaiyi kuka, "I wish Ina cikin masu kudi...da na taimakawa talakawa...dana saka mutane da dama farin ciki...amma sai gashi Allah bai yoni Mai arziki ba..." Inji habib, "Ni nayi wata tunani...me zai Hana muje wurin makocinku mu fada mashi ya bamu kudi muyi sanaa in yaso sai mu biyashi with gain..." Sufwan ya fada cikin sanyinmurya, "Anya wannan Mutumin zai yarda?... Da wahala..." Usman ya amsa mashi "Kawai mu gwada mu gani..." Habib yayi adding, sufwan da har lokacin idanuwanshi is still wet ya goge tare da mikewa ya gada bombom din wandon shi fitowa sukayi saga wannan lumgun da suke,unguwar ba unguwar masu kudi bane, irin area din nan né wayanda in kana da machine sai kabi ahankali zaka iya tukata ka shiga gidanka, koina hayaniyar yara né da matasa, duk inda suka ratsa sai an kirasu, suna zuwa wurin wata yarin dake saida awara habib ya duka ya dauki daya "Wallahi yaya hamsin kenan..." Mai awarar ta fada mashi, "In ban biyaba ki kulleni..." Habib ya amsa mata yana dariya, duk matasan babu Wanda ya wuce shekara ashirin da takwas zuwa da tara, kowannensu na sanye da yadi Wanda bai wuce 500 per yard ba, Kayan jikinshi is not expensive but they look neat, "Allah yasa yau an ajiyemin abinci." Sufwan ya fada yana tafiya, "Ni rabon da a ajiye min abinci a gida har na mance....kullum fadar mama na ki samun aikin yi..Tana ganin kaman da akwai aikin nakiyi...h,mm" habib yafada, "Ai Nima haka Inna take fadan banason aiki..wai nafison in dau wanka in dinga yawo agari..." Usman Yafada yana dariya, "Allah dai ya kawo mana iyakan wannan wahalal..." Sufwan ya fada hannunshi biyu cikin aljihu, ahankali suka dinga tafiya har suka Isa wata makeken gida dake bakin titi, duk fadin unguwar babu gidan daya Kai wannan girma da kyau, babu Mai cewa a bayan wannan gidan da akwai gidan talakawa da yawa because the house is all over the place, Nikam I wonder wane Mai kudi né ya Gina wannan katon gida a wannan unguwar, kawai shi yana da access din shiga gidnshi da mota saboda a bakin titi gidan yake amma duk wayanda suke baya basu da hanyar kirki, babu komai sai gutters da sauro da hayaniyar mutane, bakin gate din sukayi knocking after like two minutes maigida ya bude, kallon su yayi from head to toe Sannan yace "Ya dai..." Ya tambayeshi kaman bai taba ganin su ba dukda he knows them, "Wurin alhaji mukazo..." Usman ya fada mashi, kallon banza maigida ya watsa mashi yace "Ka dai San alhaji bayason hayaniyar ku..." Bai karasa ba sufwan yace "Malam ba hayaniya mukazo yi ba...kawai munzo ganinshi né.." Maigida juyawa yayi gareshi yace "To Mara kunya bai nan..." Ya fada mashi, "Haba Dan Allah ka taimaka kayi mashi magana mana..nasan yana ciki.." Usman Yafada mashi cikin girmamawa, "Ikon Allah...wai meye haka?.. Na fada maku bai nan..ku tafi dan Allah ..."Inji angry maigida. Usman zai bude baki yayi magana habib yace "Mu tafi mana...wai dole né?.." Ya fada sounding pissed off, ahankali usman ya rike shoulder dinshi Wanda hakan ya danyi calming nerves dinshi, tsoki Mai gado yaja ya rufe gate din. "I suggest mu koma gefe daya mu jirashi, dole zai fito sallah magrub...lokacin ya kusa..." Sufwan ya fada masu, babu musu suka koma gefe daya suka zauna suna kallon titi then suna hira, bayan kaman minti arbain aka Kira sallah, nan bakin titi sukayi alwallah duk idanuwansu kan gate din alhaji Ibrahim, suna gamawa alhaji Ibrahim ya fito da wasu elderly people guda hudu, "Wannan maigadin bai da mutunci Wallahi..." Inji habib, yana wucewa ta inda suke suma suka bi bayanshi suka isa same masjid sukayi sallah, bayan an idar alhaji ya fito da friends suma su sufwan suka yi saurin bin bayan shi, sallama usman yayi mashi ya juyo ya kalleshi tare da amsa sallaman mashi, da sauri usman yace "Alhaji tun dazun muna bakin gate Dinka muna jira ka...Mai gadinka yacebaka nan..." Alhaji tsayawa yayi ya kalleshi Sannan yace "Tou ya akayi..." Ya tambayeshi Kai tsaye, mutane dake tare dashi tsayawa sukayi suka zuba masu idanu suna kallon su, usman rasa abinda zaice yayi, sufwan yayi saurin cewa "Alhaji so muke ka taimaka mana..." Bai karasa ba alhaji Ibrahim ya daga mashi hannu su kuma manyan mutane dake tare dashi suka saki dariya "Wai meyasa Baku da tunani?... Wai an fada maku Ina growing kudi né?...kowa ya kwaso tsiyarsa wajena yayo... Dan Allah ni ku bar tambayata taimako...Nima ta Allah na dogara...bani da bushiyar kudi...ko roki Allah shima ya baku...daga yau ki bar damuna..." Alhaji Ibrahim ya fada cikn bacin rai, da sauri habib yace "Alhaji ba kyauta mukeso ba...kawai munason ka taimaka mana da wani Abu...mu fara Sanaa sai mu biyaka da riba..." Dariyar da mutanen keyi yasa habib yin shuru "Just listen to what this boy is saying..." Alhaji Ibrahim ya fadawa friends dinshi dake dariya har da rike ciki, "Wai kaman ni zasu damfara..."Inji alhaji Ibrahim "Wallahi sir ba danfararka zamuyi ba...kawai dai ..." Sufwan Bai karasa ba wani daga cikin mutanen dake tare da alhaji Ibrahim yace "Ku kam kuje wajen government...Sannan kullum Ana fada maku kuyi karatu rashin ji bai barin ku...gashi Yanzu tun Baku Kai koina ba kun fara maula..." Habib dake girgiza Kai saboda yanda yake ji cikin ranshi yace "Alhaji munyi karatu...we have good result..." Bai karasa ba wani daga cikin su ya ce "Then good and look for a job...ku bar maula...bai kamace ku..." Mutumin ya fadayana kallon su from head to toe saboda basuyi mashi Kama da wayanda suka da ilimi ba, "Wallahi alhaji kullum muna néman aiki..samu none bamuyi ba..." Sufwan yafada cikin sanyinmurya, "then take your problems to the government...ku bar damuna...kullum unguwar na kun maida ni kaman cbn...kowa yazo ya tatsa..." Alhaji Ibrahim ya fada yana juyawa, manyan mutanen suma juyawa sukayi daya daga cikinsu yace "Ni Wallahi am still wondering yanda akayi bazaka rabu da wannan local area ba...kwata kwata bai dace da Kai ba..." Wani abokinshi ya fada mashi, "Hmmm Ai wannan wajen wuri né na iyaye da kakanni...Sannan wayan nan mutanen da kake gani they're are like securities...nothing bad can happens...so I know why am staying here..." Alhaji Ibrahim ya amsa mashi, "Lallai kam...amma dai kana kokari..." Wani ya fada mashi "Ba kadan ba...kullum cikin bara suke, iyayen su suyi...matansu suyi Sannan matasansu suyi...duk Kaina ni kadai..." Alhaji Ibrahim ya fada sounding so fed up, daya daga cikin su Mai suna alhaji yunusa da tunda su sufwan suke yi magana bai bude baki ba yace "To you should try and help mana...ai mu da Allah ya bamu ba wai Don mun fisu bane...he has a purpose for our lives..." Yafada calmly, "Ai ba wai