← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 162

Sashe 128

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Thanks.
Kuyi hakuri kar kuce ina rushing, ko kadan I don't like bulky stories, I prefer hitting the nail at the head.49💛🧡💚❤💙
Sirrin wasu gayun
💛💜🧡💚💙❤

®Zuwairat (ummumaryam)

4⃣9⃣

Kawai kallon wannan kudin da aka zuba yake, amma kuma sanin origin of the wealth yasa kayan basu wani burgeshi ba sosai, from foot carpet dinta zuwa curtains da sauran kaya babu na gida Nigeria, komai na manyan company ne na waje, relaxing yayi kan kujera yana sakin ajiyan zuciya kawai he wish it's amra, da bai san irin farin cikin da zaayi ba amma he's not That excited, mikewa yayi ya cire babban riga dake jikinshi ya kama hanyar daya daga cikin bedroom dinta, wani irin round bed ne babu kowa dakin sai kayan masu daukan ido, wulla babban rigar yayi kan gadon yaga gadon ta fara motsi ahankali, tsayawa yayi ya saki baki yana kallon yanda gadon ke gaba da baya,
"if ba Don naira ba.. I wouldn't be here..."yafada ahankali yana juyawa. Hanyar wata bedroom ya bude luckily amarya ta data gagara taji hannun limitless a jikinta na zaune tsakiya gadon da har curtain gareta, murmushi ya saki ya hau kan gado yana cewa
"amarya baki laifi..."yafada yana matsawa kusa daita, itama murmushi ta saki kanta kasa, ahankali ya sa hannu ya daga jaw dinta yana kallon face dinta,
"baby we didn't get to know each other better. "yafada idanuwanshi cikin nata, shuru tayi bata ce komai ba,
"pls be an obedient wife..."ya fad'a reading mind dinta, babu abinda take cewa a cikin heart dinta sai pls touch me, murmushi ya saki yana Kai bakinshi saitin nata kaman zaiyi kissing dinta, miko baki tayi idanuwanta lumshe sai kuma ya dauke Kai yana cewa
"let me take my bath... " ya fad'a yana mikewa daga kan gadon. Haka Safwan ya dinga yi mata kwalele and he's doing it intentionally Don yaga bata da kunya kaman amra. Yau kwanar su biyar afra ga shiga damuwa bA kadan bA kawai he wants to have her amma yaga kawai she's so mad over he's touch shi kuma ganin hakan yasa yake ja mata aji. Afra tasan su biyu ne and she's thinking kilan baraka ke dauke mashi hankali shiyasa bai damu daita ba. Har tambayan kewayenta suke if ana haka wai ango ya kauracewa matar shi har tsawon kwanaki biyar. Yau dai bayan sallah ishai afra na zaune a falo babu make up, ta rungume pillow Tana tunanin ya zatayi ta samu hadin kan Safwan. Da sallama ya shigo looking more handsome than ever,
"amarsu... "yafada yana shafa kanta, bata ce komai ba kanta kasa Tana wasa da yatsunta, zama yayi kusa daita yana cewa
"fix my water zanyi wanka..." ya fad'a mata, ahankali ta Mike ta shiga bathroom ta hada mashi ruwan wanka, ta fito without saying a word, mikewa yayi ya kama hannunta tareda dacewa
"muje kiyimin wanka.. "ya rada mata, ahankali ta zare hannunta Tana cewa
"ni da baka sona?.. "
"why zakice bansonki... In banasonki I wont marry you... "yafada cikin whisper,
"nidai nasan bakasona...i could remember Kai da late sister na yanda kukeyi amma ni you don't care to touch me.. "ta fad'a babu kunya, shuru yayi ya Kama waist dinta tare dacewa
"I want to be a perfect gentle man... "
"ba wani gentle man.. Kawai baka sona... "ta fad'a Tana turo bani, kama bakin yayi yace
"let me show you... "yafada yana daukanta, that night was their first night har kuka ta dingayi mashi shima yasan he have missed a lot because she's quite different from the others, abunka da amarya da aka kashewa kudi sosai wajen gyara, He wished tun ranar da aka kawota yayi digging in because Shes so hot that he loose control of himself and do what he does best, the following day bai je aiki ba yana hutun, ko kadan bai ragawa afra ba, saida yaga zata mutu ya barta, ko abincin kirki bata iya ci duk idabuwanta sun kumbura, it feels so good having halal sex for once in he's entire life. Baraka kam bata dauka cewa Tana da miji ba because yanda dodo yake haka ta dauki Safwan, Allah ya bude mata ido taga lot about him a dream, and she's lucky bai wani damu da harkokonta ba, kaman bata gidan and ko yanzu tafi sati uku rabon data ganshi, zancen aurenshi bai dameta ba because bata damu dashi ba, kawai tabi umarnin iyayenta amna ko. Mutuwa bata tsoro yanda take tsoron Safwan. Farin cikinta daya su inna da asiya suna gidan, Batasn irin yanda zata rayu babu su cikin gidan ba, Inna na bata shawara sosai Don dukda Safwan bai taba Kai kararta ba tasan irin zaman da suke gidan. Daman safwan ya fadawa Inna a part dinta zai ajiyeta sai kuma Allah yasa ya sake gida. Ita dai baraka abunda take fadawa Inna is she's scared of him, bata fad'a masu abinda take gani kanshi ba but ta fad'a masu ita dai batason shi sannan she's afraid of him, asiya kam is 100% behind her while ita inna Tana bata shawara kan hukuncin dake kan mace Mai kauracewa mijinta. Jinta kawai take amna ko shekara dubu zatayi bata ga dalilin da zaisa ta amince da dodo irin safwan ba. She don't lack anything as Tana dafa abinci ta kawo part din Inna duk suci tare, tunda afra ta shigo gidan duknbasu San ta ba because bata damu da harkar kowa ba gjdan, tunda aka kawota bata taba fita ba balle ta shiga inda inna take, yaran daman are afraid of her tunda sun san yaran Wanda yayi holding dinsu captive ne, duk Inna tafi kowa tsoron afra because she thinks she might be as evil as her dad.

Two weeks later

Mufida ce zaune gaban hajiyarta face dinta babu walwala, she look so sad sai magana take kasa kasa kanta kasa,
"wai Meye kikewa mutane guguni?.. "mahaifiyar ta tafad'a Tana kallon yanda take turo baki,
"nothing... "ta amsa mata cikin calmness,
"in ba komai ki tashi kici abincinki.."
"am not hungry... "ta amsa ahankali,
"then ki bani waje... "inji mom dinta, zama tayi ta ki tashi,
"mummy... "ta kira mahaifiyar ta,
"Naam.. "ta amsa mata
"Dan Allah ki fadawa Muhammad... "sai kuma tayi shuru, zama hajiya ta gyara Tana kallonta
"am alk hears... "ta fad'a cikin surprise
"kawai ya dinga kulani..."ta fad'a kaman Shes shy, salati hajiya ta farayi Tana clapping hannu
"ban gane ya dinga kulaki ba,..what sort of kulawa."ta tambayeta,
"yo mummy.. In ina mashi magana bai damuwa Dani.. "
"ke dalla rufemin baki before I decend on you... Wallahi you're shameless... In ba rashin hankali ba mutum da baki San daga inda yake ba.. Bakisan asalinshi ba... Bakisan me yayi ya haukace ba.. Bakisan ko yana da iyalan shi kafin ya haukace ba shine har kike wani maganar ya dinga kulaki?.. Wallahi kar in sake ji... In har Kinga na kara bin ta kan wannan maganar sai ya samu memory dinshi ya dawo daidai mun San asalinshi,..am I clear.. "ta taka mata birki Don ta ga take takenta na shisshigewa habib da take yi, ahankali ta daga mata kai,
'"good.. Now bani waje... "ta fad'a mata, babu musu ta Mike ta bar falon jiki babu kwari. Kwamtawa tayi tana tunanin abinda mahaifiyar ta Tace,
"what if da gaske yana da family dinshi... Tab.. I. Can't be a second. "tafad'a out of pride.
Shi kam habib the more yana zaune da alhahi bello the more alhaji bello na Kara kaunarshi, dukda post din da alhji ya bashi har yau shine ke daukar bag dinshi, shi yake bude mashi mota da sauransu,
Haka na sa alhaji kara kaunar shi, he loves and values him so much, yau suna office yana zaune gaban alhaji yana yi mashi bayanin expenses dinsu na last month, ji yayi kanshi yayi mashi nauyi har ya daina magana, alhaji zama yayi yana kallonshi, few seconds later ya cigaba da calculations kuma bayan kaman minti biyar yayi shuru tare da dafa goshinshi yana cewa
"wayyo.. My head... Kai na... Mamanmu..."maganar ta fita daga bakinshi step by Step sai kara danne goshinshi yake idanuwanshi rufe gam,
"subhanallah... What's wrong with you... " alhaji ya tambayeshi cikin tashin hankali yana mikewa tsaye saboda yanda habib ya Chanza in a minute kaman bashi ne ke magana ba few seconds back ba, habib dora both hands yayi a goshinshi yana ihu tare da cewa
"kaina zai fashe.. Mamanmu... Wayyo mamanmu...mamanmu... Nashiga uku... "yafada yana faduwa daga kan chair dayake zaune zuwa kasan office din, cikin tashin hankali alhaji ya kira secretary dinshi yace ya kira company doctor dinsu, da sauri ta fita shi kuma ya dawo kan habib dake kwance ya rikeshi yana kiran
"Muhammad what's wrong with you " Kawai yake tambayan shi cikin damuwa,
"wayyo kaina.. Mamanmu.. Ki ta ceceni... "yafada yana jujjuya kanshi while holding he's head very tight,
"mamanmu?. "alhaji yayi murmuring ahankali,
"mamanmu!.. Habib.... "habib ya sake maimaitawa, jin sunan da yake kira yasa alhaji gane he's getting some hint about he's previous life,
"habib... "alhaji ya fad'a sai habib dake kwance yace
"Naam... Sir my head... " ya amsa mashi, murmushi alhaji ya saki yana cewa
"habib sannu.. The doctor is coming... "alhaji ya fad'a cikin excitement,
"Mamanmu... "ya sake maimaitawa cikinzafin Nama, alhaji dake durkushe kusa dashi sannu ya dingayi mashi har doctor ya shigo.
Chapter 128 · 0% Book details