← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 162

Sashe 11

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Excuse me..." Sukaji an fada a bayansu, da sauri su uku suka juyo, wani mutum da arziki is written all over him suka gani ya nufosu, Mutumin na sanye da shadda dake moving with each move dayayi, shaddar kaman an zuba mata ruwa saboda yanda take salki, Mutumin bakine amma he's color is glowing, inda suka saki baki suna kallon shi ya karaso,
"Assalamun alaikum..." Yafada yana kallon faces dinsu, da sauri suka amsa suna kallon wannan Mutumin,
"Sunana alhaji idris Mai saa....ku kuma ya sunanku?.." Ya tambayesu sounding so friendly,  dukkan su baki suka bude Jin yace he's idris Mai saa because he's a very popular business man, suna Jin sunanshi sosai but never met him, mamaki sukayi me ya kawoshi shopping da kanshi,da Sauri habib yace
"Suna habib isa..." Yafada voice dinshi na cracking Sannan he's heart is jumping very fast,
"Nikuma sufwan aliyu..." Sufwan yafada ko blinking baiyi, he's also is having some sort of feeling, usman dayaji heart dinshi na néman fita yayi introducing kanshi, duk su uku dake kallon alhaji idris ji suke tsigan jikinsu na tashi,
"Nice names...naji kuna néman aiki né..." Yafada cikin muryar yan Hutu, da sauri sukace
"Eh..." Duk suka amsa tare,
"Ohhh...bakuyi karatu bane..." Cikin sauri da kuma rawar voice habib yace
"Sir munyi karatu...shekara uku kenan da muka gama muna néman abinyi bamu samu ba..." Yafada kanshi kasa
"That's bad..." Yafada cikin tausayawa but deep down he's saying
"Exactly people we need..." Yafada cikin ranshi,
"Kullum cikin yawon nema muke amma nobody is willing to help us..." Sufwan yafada kaman zaiyi kuka
"That's bad...and am sorry about all that...wannan shine reality...but today you're lucky tunda Allah ya hadani daku...," Yafada, Bai karasa ba duk suka durkusa kasa saboda farin ciki,
"No no no....ku tashi pls don't embarrass me..." Yafada wearing a smile, takawa yayi ahankali ya nufi wata Range Rover dake tsaye yana sheki ya bude, su sufwan kallon juna kawai suke, ciki ya shiga ya dauko kudi da complementary card ya fito ya maida door din ya kulle, mint din 1k dake hannunshi kawai suke kallon step biyu ya dauka zuwa inda suke tsaye ya fara mikawa sufwan roll din 1k wato 100k da card, idanuwa waje, jiki na rawa  sufwan ya mika hannu ya amsa in the process hannunsu suka hadu, ji yayi wani Abu yayi yawo from he's head to toe,
"Nagode alhaji..." Sufwan yafada cikin rawar jiki,
"Stop thanking me...it's just the beginning..., "Alhaji idris ya fada mashi Sannan ya juya ha habib da ya kasa numfashi saboda kudin da yake gani Shima ya mika mashi 100k da card, yana amsa ya durkusa nan kasa yana gode mashi, dariya kawai yayi ya mika usman shima 100k da card dinshi, sai da suka gama godiya ya ce
"Yanzu you have my cards...you can give me a call..." Ya fada masu, Sannan ya juya, har lokacin basu bar godiya ba, shigewa yayi without turning back, dukkan su kallon kudin dake hannunsu suke,  they're all gasping for air saboda ji suke numfashinsu na néman daukewa,
"Ashe da akwai mutanen kirki haka?.." Habib ya fada cikin Karfin Hali,
"Ashe da akwai masu halin kirki haka shine muje ta Shan wahala cikin rana, ruwa da iska?.." Ya sake fada in so much excitement,
"Alhamdulillah...Ashe wahalal mu zai sa mu hadu da mutum irin alhaji idris Mai saa?.." Sufwan yafada yana kallon kudin dake hannunshi, da ganin kudin straight from da engine yake saboda it look so neat, ahankali usman ya Kai kudin hancinshi ya lumshe idanuwa tare dacewa
"I can't believe wannan nawa né...Dan Allah in mafarki nake kar Dan burouban daya tasheni..." Yafada sounding so funny, dariya sufwan da habib sukayi Sannan habib ya daga hannu ya falla mashi duka yace
"Tashi you're dreaming.." Habib Yafada yana dariya, dukkan su dariya suka usman yana Shafa inda habib ya dokeshi ya Dan waigar Sannan ya tura kudin cikn aljihu yana cewa
"Kar barayi su ganmu..." Yafada yana tura kudin cikin pocket dinshi, suma sauran turawa sukayi cikin aljihunsu Sannan sufwan yace
"I can't still believe this,,,sai na sayi wani Abu cikin kudin zan yarda it's mine..." Yafada yana barin su nan wajen, bayanshi suka bi suna dariya, adaidaita usman ya tsaida suka shiga ciki har suka isa unguwar su basu bar maganar Mai saa ba, suna sauka kowanne babu saurin da yake sai don ya isa gida ya fadawa iyaye shi, kowannensu hanyar gidansu ya Kama sai tafiya suke da sauri. Sallama sufwan yayi a Kofar shiga gidansu, kannenshi suka amsa mashi,
"Ina Inna taje.." Ya tambayi sister dinshi,
"Tana ciki...yaya fuskar ka dauke da annashuwa..meye labari..." Ta tambayeshi cikin excitement, idanuwa yayi rolling yana cewa
"Kanwata bazaki gane bane..." Yafada yana nufan dakin Inna, labulen ya yaye yaganta zaune gefe daya dakin da babu komai sai taburma da katifa,
"Inna inawuni?.." Ya gasheta
"Lafiya..." Ta amsa atakaice,
"Inna albishirinki.." Yafada trying to light her up, kura mashi Ido tayi for a moment Sannan ta kauda kanta gefe as if he's been talking to her, jikinshi na rawa ya fiddo kudin cikin aljihunshi ya ajiye gaban ta, da sauri ta dauki kudin Tana dubawa domin tabbatar dacewa it's real, sister dinshi dake tsaye bakin kofa baki ta bude ganin kudin dake hannun Inna,
"Yaya Ina ka Sami wannan kudin?.." Ta tambayeshi Tana shiga dakin, Inna kam kallon kudin kawai take, sai da tabbatar it's real Sannan ta kalleshi tace
"Da fatan dai ba satoshi kayi ba..."   Ta tambayeshi idanuwanta cikin nashi, idanuwa ya lumshe tare da girgiza Kai yace
"Inna ba satoshi nayi ba,,.ban taba sata ba...kuma Yanzu bazan yi ba..." Yafada mata cikin natsuwa, Inna Kara kallon kudin tayi Tana jujjuyawa sannan ta daga karkashin tabarma ta ajiye dukkan kudin without caring to know who gave him the money, or for what reason,
"Inna baki tambayeni Wanda ya bani kudin ba..." Yafada mata sounding so calm, kura mashi Ido tayi Sannan taja tsaki tace
"Ko na tambayeka Sanin ko waye zanyi?.." Ta fada hankalinta kwance,
"Tou Inna in fada maki ko waye ya bani kudin?.."
"Ka rike saninka.." Tafada atakaice, Dan sadda Kai kasa yayi with he's eyes closed, yana mamakin why she's like this, before he's thinking saboda bai taimaka mata Yanzu kuma yana Dan samu yana kawo mata amma ko a jikinta,
"Inna baki bani wani Abu ba..." Ya fada mata
"Wani Abu kaman me kuma?.." Ta tambayeshi
"Inna cikin kudin.." Bai karasa ba ta watsa mashi kallon banza Sannan tace
"Nasan nawa aka Baka?.. "
"Ai Inna iyakan abinda aka bani kenan...Wallahi dukkan su kenan..." Yafada cikin sanyinmurya
"To sai me...ko dukkan su kenan sai me?.. Ubanme zakayi da kudi?.. Nice cinka da shanka...kasan duk Sanaa ta ta lalace saboda rashin jalli...Yanzu tunda Allah ya kawo wannan sai in fara sabuwar Sanaa saboda ko na Baka ba Sanaa ka iya ba...haka kuka bude shago da makudan kudi amma ko shekara batayi ba kuka kashe ta da abokan ka na banza..." Sufwan bai ma tsaya ya sake sauraron abinda zata ce ba ya Mike ya bar dakin, yana Jin haushi amma deep down he's happy, at least yasan mom dinshi will manage the money well, dakinshi ya koma ya kwanta yana tunanin Mutumin daya basu kudi, Kawai sai ya tsinci kanshi da faduwar gaba, he remembered yanda jikinshi yayi mashi lokacin da ya ganshi, he had this undisclosed feeling,  tunda yake bai Tana Jim Abinda yaji dazun ba,
"Nervous..." Ya fadawa kanshi, da sauri kuma ya girgiza Kai yana cewa
"Ba haka nervousness yake ba...the feeling was so..." Yafada ahankali yana tunanin yanda jikinshi yayi lokacin da suka hada Ido da Mutumin, hannu yasa cikin aljihunshi ya fiddo complementary card din da ya basu, juyawa ya dingayi yana kallon card din dake dauke da sunan saa, shidai he's not excited the way he should be, kawai he feels so bad for no good reasons.
Chapter 11 · 0% Book details