Sashe 157
Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri safwan ya juya ya kulle kofa yana tunanin imagination dinshi ne ke gane mashi habib likewise habib juyawa yayi ya kalli alhji bello sannan ya sake juyawa still suka hada ido, da sauri safwan murza tired eyes dinshi yace "habib.. "yafada jikinshi na rawa, ahankali jiki na rawa habib daya sha suit ya Mike tsaye yana cewa "safwan... " yafada sounding unbelievable, step daya safwan ya dauka zuwa cikin office din yana cewa "habib pls kai ne ko am day dreaming... " yafada yana kallon habib from head to toe, da sauri habib ya kalli alhaji ya sake kallon Safwan daga kai zuwa kasa yace "it's me.. Nine nan habib... " yafada yana takowa zuwa kusa da safwan, "habib you made it... " bai k'arasa ba suka rungume juna, banda jujjuya juna babu abinda suke, alhaji folding hannunshi yayi yana kallon su, he feels like crying saboda yanda sukewa juna, da sauri safwan ya saki habib ya koma baya yana kallon habib that look so handsome, elegant, cute and classy, kayan jikinshi ya kalla zuwa takalmin kafarshi, hannun habib ya rike ya juyashi shima habib ya juya mashi saboda ya ganshi da kyau "habib wai da gaske kaine?..habib so you made it... "yafada voice dinshi na rawa, ajiyan zuciya habib ya saki before saying "yes... With prayers... Patience.. Here I am I made it... " yafada yana ware mashi hannu tare da sake juyawa, kawai sai safwan ya fashe da kuka,. Yana cewa "habib congratulations... Habib ka godewa Allah... " yafada cikin kuka, kai alhaji ya sadda kasa saboda yanda yaji hawaye nataruwa idonshi, jin kalaman safwan breaks he's heart, hannun habib ya rike yana shaking dinshi yana cewa "congratulations... Congratulations habib... Habib ina maka congratulations... You have made it.... " yafada cikin matsanacin kuka kawai sai ya zame ya zauna kasa, hada Kai da gwiwa yayi ya fara kuka sosai yana cewa congratulations, idanuwan habib cikowa sukayi da kwalla durkusawa yayi gaban safwan ya rasa abinda zai ce mashi, juyawa yayi GA alhaji sai yaga har ya fara hawaye, babu abinda ya gani tattare da safwan sai nadama, yaga total regrets, hannu habib ya dora a shoulder dinshi yace "safwan wannan kukan da kake na meye?..don't tell me you did what you where asked to do... Don't tell me you killed the virgins.... " yafada kaman baisan abinda ke faruwa ba, Kai safwan ya daga ya kalleshi for Just a second sannan yace "kunyar kallon ka nake habib... Am so. Ashamed of myself... Bazan iya cewa komai ba sai dai inyi maka barka... Allah is own your side... Allah na kaunar ka... Pls kullum ka godewa mashi countless time... " yafada cikin kuka sosai, alhji bello was weeping uncontrollably kaman baby, " tashi... " habib ya fad'a mashi, "pls Just let me seat here... Barni kawai nan... Duniya ta koya min hankali habib... Amma tunda Kai Allah ya baka dama... Tell the whole world abinda ke faruwa... Pls announce it... Tell our youth both mata da maza abinda ke faruwa... Ka gani da idonka... Ka fad'a masu duk halin da suka shiga kar subi duk wanda yace zai taimaka masu without good reasons... Pls do... Many will lost " yafada matsanacin kuka, alhaji bello was just looking at them and at the same time he's weeping, bai taba tunanin safwan wato limitless zai zauna yana kuka hakan ba, kawai he was expecting to see a stubborn person with high ego and pride, dukda he saw him once bai samu daman magana ko kebewa dashi ba "wannan ya zama jihadinka...ba haka nan Allah ya kubutar da Kai ba... There's a reason... So help other kafin su shiga halin da muka shiga... " yafada sounding so tired and fed up, hawaye ne yafara zuba daga idanuwan habib, Kama safwan yayi suka Mike tsaye, murmushi safwan ya saki yana kallon face din habib, shima habib murmushi ya saki duk fuskokin su dauke da hawaye, " I miss you so much... I can't wait to telk usman you're a life and the luckiest among us... "yafada ahankali, "I miss you all too... Na rasa inda zan ganku.. Naje old Unguwar mu akace baku nan.. I miss you sosai my besty... " habib ya fad'a yana kallon idanuwan safwan, "wait a minute what are you doing here... " safwan ya tambayeshi, juyawa habib ya yi ya kalli alhaji sannan yace " I work here... " sai lokacin safwan ya tuna da why he's here sannan ya tuna basu kadai bane, kallon alhaji bello yayi ya gaidashi cikin respect, amsawa mashi yayi yana goge face dinshi cikin dabara kaman wani abu ya fad'a mashi a ido, "what are you doing here... " habib ya tambayeshi in return, ajiyan zuciya ya saki sannan yace "it's a long story...amma let me cut it short.. Na zo ne in roke alhji ya bani daman ganin yarana.." yafada cikin sanyimurya , surprise look habib yayi mashi sannan ya juya GA alhaji shima ya kalleshi because ko kadan bai San abinda safwan is talking about ba, "yara kuma?.. "habib ya fad'a sounding confused, ahankali safwan ya taka zuwa gaban desk din alhaji sannan yayi kneeling tare da harde hannun shi biyu waje guda ya fara cewa "sir nasan ka haifeni... Dan. Allah na zo neman alafarman ganin yara na... Wallahi su kadai ne rabona a duniya... Ban kara Haihuwa daga su.. Pls deny me everything in the world amma banda ganinsu Dan Allah..." yafada cikin hawaye again, habib dake tsaye bayanshi looking confused yace. "wai sir what is he talking about... ".inji habib hannu alhaji yayi masu alaman su zauna, habib zama yayi amam safwan yana nan kan gwiwanshi looking so pitiful, "pls seat... " alhji ya umarceshi, ahankali ya Mike ya zauna kan kujera, " I heard something like kace su kadai ne baka kara Haihuwa... What does that mean?. " alhaji ya tambayeshi, shuru safwan yayi yana hawaye, baisan yanda zai fad'a mashi cewa garin zaluntar wasu ya zalunci kanshi, "sir pls kar muyi wannan maganr...one wrong word from me mutuwa zanyi... "safwan yafada kanshi kasa "pls what are you people talking about... " habib yayi magana sounding out of place, ajiyan zuciya safwan ya saki sannan ya Ya fad'a mashi komai daya faru tsakaninshi da rabia, bai boye komai ba, cikin jimami habib yace "Inna lillahi... safwan... so you are responsible for he's death... Safwan sai da ka cika burinka na ganin kayi Maganjn alhji Ibrahim... Dukda koda zai bamu billion a lokacin bai hana mushiga halin da kowannenmu ya shiga... Saboda komai rubuce yake...nobody can make us poor or rich sai by the will of Allah ..." cikin matsanacin kuka safwan yace "I was angry... You don't know what we hace seen... Duk na mance da hukuncin ubangiji.... Gashi yaran ne kawai the only children that I will ever beget... " yafasa still crying out loud " pls me kake nufi da baka kara Haihuwa?.. "habib ya tambayeshi, shuru yayi yana hawaye, duk jikin alhaji bello ya mutu, ua rasa abinda zai fad'a mashi, ajiyan zuciya ya saki sannan yace "son... I know how everything went... But komai sai da yardan Allah... Arziki na Allah ne likewise talauci na Allah ne... Did you know that you will give account for every dime and how it comes?... " Yafada yana kallon yanda safwan ke hawaye, "did you know that komin dadin arzikin duniya ta lahira ta linka shi thousands time?... Did you know da akwai kwanciyar kabari... Did you know da akwai kwanciyar kabari... Dana wanna duniyar babu komai cinknta da mutum zai kauce hanyar saboda dashi... Bawa bai kamata ya nemi dadin duniya ya mance da inda zai dauwama ba... Saboda na nan is for a short period of time and na chan is for ever... Mutum da arzikin halak yaya ya kare balle Mai na Haram... It's better ka mutu cikin talauci da Kaci kobo ba Haram Don duk tsoka da Haram ya gina sai yaci wuta... " safwan na sauraronshi yana kuka sosai, he's heart is boiling, "wayyo ni... " yafada cikin matsanacin kuka, "Nashiga uku... " ya sake fad'a kaman zai sike saboda yanda yake kuka, habib ma was crying yanda safwan ke kuka babu Wanda zai ganshi bai zubda hawaye ba, yasan what awaits him in Allah ya dauki ranshi, "tawa ta kare... Way out... The only way is the one in... Duk Wanda yashiga..." kawai sai ya fara tari sosai da karfi, rike throat dinshi yayi Wanda yasa alhaji saurin mikewa shima habib rikeshi yayi while he was fallen from the chair da yake zaune, da sauri alhaji ya dauko ruwa ya bashi, yafi minti biyar yana wannan tarin idanuwanshi sun fito waje sannan ya daidaita, kawai yana cikin wannan maganar yaji an rike mashi wani abu cikin throat dinshi, da kyar ya samu yasha ruwa sannan ya samu sauki, yasan what happened, shuru kowa yayi for a moment sannan yace "sir pls.. Ka bani daman ganin yarana... " shine abinda ya fad'a this time sounding firm, "am sorry to say..but Meye amfanin ganinsu.. Perhaps baka dace a bakasu ba... " da sauri safwan yace "why... " yafada idanuwnashi duk waje, "because under my watch bazaka ciyar dasu da Haram ba... " alhaji ya amsa mashi atakaice, "if har zaka ji tsoron Allah ka daina ka dawo normal person zan baka su... " inji alhaji, "sir you know I can't... " yafada jikinshi na rawa "yes you can... Habib did it and Hes here alive,... " alhaji ya amsa mashi "sir habib yana da miracle nikam me nake dashi?.. Wa zai tsayamin cikin dare yayi min adua?.. " "kana da Allah... Kana da mu... " habib ya fad'a mashi, "son it's better ka mutu da ka rayu da wannan rayuwar...." "I. Don't want to die... " yafada yana fashewa da kuka, Kai alhaji ya girgiza yace "da mutuwa da rai duk hannun Allah yake... Babu Wanda yaisa ya kasheka sai at appointed time da Allah ya rubuta maka ...babu Mai iko da Rayuiwar ka sai Allah... " Kai safwan ya dinga girgizawa yana cewa "sir you won't understand....i only nasan abinda ke faruwa.... Pls ka bani daman ganin yarana... Zan biya anything to be with them... Pls... " yafada