← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 162

Sashe 13

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mahaifiyar nana ce zaune a gaban mijinta face dinta Sam babu walwala Tana cewa
"Ni Wallahi abba bakayi min adalci ba...ya zaayi ka amince nana ta zauna hostel?.. Ai hakan bamutuncin mu bane..." Tafada sounding so pissed off,
"Ki kwantar da hankalinki munyi deal da ita kan if results dinta baiyi kyau ba a first semester zata dawo day...duk da a Zahirin gaskiya hostel din shi ya fi ta zauna saboda da akwai nisa tsakanin mu da buk...ko kadan banason yawan zariyarta a titi..it's better ta zauna chan hostel sai ta dinga dawowa gida duk weekend..."Yafada mata cikin sanyinmurya, Kai ta girgiza tace
"Nidai gaskiya abba ba haka nasoba...ko kadan banason yata ta zauna Ida babu idanuwana sai a gidan mijinta...Yanzu da yaran banza sunyi yawa sai ka saki yarka Baka San halin da take ciki ba har tsawon kwana biyar?.. Gaskiya abba ka sake shawara..."
"Dan Allah ki kwantar da hankalinki...ai zamu dinga monitoring dinta...Sannan Ai kinsan mun baa tarbiya Mai kyau..." Bai karasa ba ta katse shi dacewa
"Ka ma bar wannan zancen...ai babu yarinyar banza da ba'a bawa tarbiya ba...kawai Ana iya rushe maka tarbiyar daka shekara da shekaru kana ginawa..har ga Allah hankalina bazai kwanta ba muddin bana bacci under the same roof da nana...duk abinda yaje ya dawo Kaina kadai zai kare saboda nice mahaifiyar ta..." Bata karasa ba yace
"Haba asiya... Pls kiyi mata fatan alkhairi and not the other way around mana..." Ya daka mata tsawa, shuru tayi Tana magana kasa kasa alaman she's not ok,
"In kuma saboda aikin gidane ki samu almajiri..." Bai karasa ba Tay saurin cewa
"Aa Wallahi abba...kafin nana tazo duniya wake kula da gidan?..duk nice..har yau ba'a yuk aikin da sai gagareni cikin gidan nan ba....Wallahi babu aikin...nidai kawai banason yata ta zauna cikin wasu...azo a koya mata wata tarbiyar banza..kaji problem Dina..." Ta fada mashi atakaice, ahankali ya kwantar da murya Sannan yace
"Ki kwantar da hankalinki...ba kanmu farau barin yara a hostel ba...so nothing bad will happen...kawai pray for her...kinji kou?.." Ya fada mata cikn sanyinmurya, shuru tayi bata ce mashi kala ba still not happy about he's decision. Ahankali ta mike Tana cewa
"Bari in dauko maka abinci..."Tafada sounding still angry, nana dake labe Tana sauraron abinda suke cewa tayi saurin fadawa dakinta da gudu,
"Munafuka...zakici ubanki né..." Mahaifiyar ta tafada Tana kaman hanyar kitchen, nana dake zaune bakin katifar ta ta turo baki tare dacewa
"Oho dai,,,you won't succeed..." Tafada kasa kasa yanda babu Wanda zaiji abinda tace.

Bacci suka sha har wajen 1 Sannan suka tashi sukayi alwallah suka tafi masjid sallah bayan sun dawo sufwan ya dauki waya yana saka daya daga cikin number dake cikin card din, sai da ya gama sakawa yaki dailing ya zauna kaman Mai tunani, ahankali ya mikawa habib waya yana cewa
"Kai kayi magana dashi..." Da sauri habib ya tue wayar yana cewa
"Lallai ma...Kai kayi magana dashi...." Ya fada tare da juya mashi baya, sufwan mikawa usman wayar yayi yana cewa
"Dan Allah Kai kayi magana dashi please..." Harara usman ya watsa mashi Sannan yace
"Aa Kai kayi ..ai ka girmemu." Yafada yana dariya, dariya sufwan yayi
"Wai kiran nan dole né?.. We should just forget about calling him mana tunda we're having bad feeling about it..." Inji habib,
"Babu wannan zancen..." Inji usman, sufwan bai Kara cewa komai ba yayi dailing number ya Dora a hansfree , wayar na fara ringing sukaji gabansu na faduwa especially habib, har wayar ta gama ringing ba'a daga ba,  sake dailing yayi still ba'a daga ba, wata number ya sake dailing ringing kaman uku aka daga da sallama, da sauri sufwan ya amsa yana cewa
"Ina wuni alhaji..." Ya fada voice dinshi na rawa sosai, usman da habib idanuwa suka zubawa sufwan suna kallon shi Sannan suna sauraron muryar alhaji idris dake cewa
"Lafiya lau..."
"Alhaji mune wayanda jiya ka bamu card kace mu kiraka...." Yafada mashi,
"Oh I remember..I have been expecting your calls....kuna lafiya ?..." Ya tambayeshi cikin muryar yan hutu,
"Sorry sir...munce kar mu dame ka da waya tunda sassafe shiyasa..."
"Babu damuwa Ai....wannan card Dana Baku is my direct line...ba kowa nake bawa wannan card ba...so Yanzu kuna Ina?.." Yafada kaman bashi né wannan popular Mai kudi that is known all over ba,
"Muna unguwar mu..." Sufwan ya fada mashi,
"Alright...Yanzu ku samu abin hawa ya kawo ku saa estate...duk Mai abun hawa yasan wajen..."
"ok sir.." Sufwan ya fada mashi, alhaji idris bai Kara cewa komai ba ya katse wayar shi, ajiye wayar sufwan yayi ya kalli su habib da suka zaro idanuwa suna kallon shi, hannu ya daga kaman zai tsone masu Ido sukayi saurin blinking
"Gaskiya I don't think there's anything to worry about..." Usman Yafada
"Me too..." Sufwan ya amsa mashi, ajiyan zuciya kawai habib ya saki without saying a word,
"Gaskiya muje Yanzu kar ya tsaya jiran mu..." Usman ya fada, jiki babu kwari habib ya Mike
"Duk wahalal da mukasha is coming to an end...am so happy Wallahi...duk masu kudin garin nan sunki su taimaka mana sai gashi Allah ya hadamu da Wanda yafisu..." Sufwan ya fada cikin farin ciki, shidai habib bai ce komai ba ya fita usman yabi bayanshi sai sufwan daya fito ya saka shoes dinshi ya jawo Kofar ya kulle, yanason shiga cikin gida yayi wa Inna sallama amma yasan he will not get what will please him, haka ya hakura suka fita zuwa bakin titi suka tsaida adaidaita suka fada mashi inda zasu, shidai habib was so quiet.

Plssss share.5💜💛❤️💙💚
Sirrin wasu gayun..
💜💙❤️💚💛

® zuwairat (ummumaryam)

5️⃣

Free page
Chapter 13 · 0% Book details