← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 162

Sashe 76

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safwan tisa kansu yayi yana. Baya suna gabanshi, yanda yan kidnappers ke saka mutane gaba su korasu without complaining haka shima ya sa su gaba ko magana basuyi, Inna bata San gwarjini ba sai kan safwan m Yanzu ko kallon idanuwanshi bata iyayi balle tayi complaining, a da yanda ya shigo gidan babu sallama ba karamin fada zatayi mashi ba amma Yanzu he's presence scares her, bata iya bude baki a gabanshi balle tayi mashi fada, yana bayansu yana latsa wayar hannunshi suka USA bakin titi inda motarshi take, daman basu San ya sayi mota ba Don haka koda yazo daidai motar ya bude motar Inna couldn't hide her surprise anymore
"Kana nufin wannan motar naka né?.." Ta tambayeshi Tana kallon face dinshi cikin duhu,
"Eh..." Ya amsa mata atakaice, asiya kam ji tayi duk jinin jikinta ya kafe, batasan abinda ke damunta ba amma batason zama kusa da safwan, sai sata kallon shi kawai take Tana tsoron kar su hada Ido, haka nan Tana ji a jikinta yayanta is not that good person anymore, tasan something bad has happened amma bazata iya cewa ga abinda ya faru ba, baya ya bude masu without saying a word but he knows they t
Understand abinda yake nufi, tsaye sukayi babu Wanda ya samu courage din shiga motar,
"Dan Allah ku shiga dare nayi..." Ya fada sounding so fed up. Sa sauri asiya ta shiga followed by Inna sai sauran kannenshi,maidawa yayi ya kulle Sannan ya zagaya ya shiga yaja motar ya bar wajen, Inna sai kallon cikin motar take not knowing what to say, asiya kam ta rasa abinda ke mata dadi, tuki ya dingayi ahankali kaman babu komawa cikin motar sai shi sabida they're so quiet, bayan kaman minti goma Inna tace
"Safwan Wai yaushe ka iya tukin mota?.." Ta tambayeshi, he can hear her fear from where he's sitting,
"Ya akayi né Inna...kina tsoron kar in zubdaku né?.." Ya tambayeta yana kallon ta tamirror,
"Aa..kawai Ina...mamaki né..." Ta fada voice dinta na rawa,
"Inna kenan...ai ke baki lura da komai..shiyasa bakisan na iya tukin mota ba..."  Ya amsa mata, bata Kara cewa komai ba, tuki ya dingayi ya iso wata snack joint yayi parki ya fita daga cikin mota, kaman asiya Tana jira tayi saurin cewa
"Inna inajin tsoro...yaya yana bani tsoro..." Tafada jikinta na rawa, ajiyan zuciya Inna ta saki Sannan tace
"Kar ki damu in mun je gidan in baiyi mana ba sai mu dawo.." Tafada sounding out of point,  idanuwa asiya ta zaro tace
"Yanzu Inna tunanin da kike kenan?.. Baki tunanin ina yaya ya samu kudi ya sayi run wannan katuwar mota Sannan har ya sayi gida?.. Inna bakijin wani iri in kin kalleshi?..Inna tsoron yaya nake ji..,da kyar in San iya zaman gidanshi..." Tafada kaman zatayi kuka,
"Wai ke mene tunanin ki...kina tunanin yana sata né kou wani Abu?..kullum aduar mu Allah ya yaye mana wannan bakin talauci...Yanzu Allah ya rufa mana asiri amma shine kike son kawo wata maganar banza?... Tou ki sani muddin baki zama gidan safwan sai ki nemi wata uwa bani ba..." Inna ta fada mata cikin bacin rai, safwan na daf da shiga ciki ya tsaya yana Jin Abunda asiya take cewa, yayi taki kusan 15  but he can hear her loud and clear, wani irin tamke fuska yayi yana cewa
"Don't let me hurt you...asiya I love you so don't let me hurt you.." Yafada sounding angry,
"Inna Don muna néman arziki bazaisa yaya ya samu kudi rana tsaka mu kiyin bincike ba...ya Kama ta mu bincika aikin da yaya keyi har yayi kudi haka cikin kankanin lokaci..." Asiya ta cigaba da fadawa Inna while safwan na sauraron su,
"Amma wannan yarinyar anyi mayya...Wallahi sai naci ubanki kika Kara magana...ko me ya keyi Ina ruwanki,..ke baki godewa Allah da ba namiji  bace ke?.. Kina gida zaa kawo kici...amma din bakin Hali irin naki zaki fara maganar da bai da amfani..shiyasa har Yanzu bakiyi aure ba...duk saaninki sunyi aure suna gidan mazaajen su...to Wallahi ayir dinki...ubanki zanci matsiyaciyar banza..." Inna ta fada cikin matsanacin fada, fashewa da kuka asiya tayi Tana cewa
"Wallahi Inna kiyi bincike...tun ranar da yaya ya dawo daga tafiya ya koma kaman am sauyashi...ya Chanza min sosai...Inna har Mari na yayi kwana kin baya..yaya da bai yarda wani Abu ya taba ni....Inna na rasa ya akayi bakijin abinda nake ji...wannan ba yaya bane...in kuma yaya né to an cire mashi wani Abu Mai amfani..." Bata karasa ba taji sauka. Mari, safwan dake tsaye waje yana Jin su yaji face dinshi da damshi, yana tabawa yaji hawaye, da sauri yasa hannu ya goge, he's so surprised yanda akayi asiya ta gane he's changed tun ranar daya dawo saga tafiya while it's hard for he's own mother to see, he's heart hurts so much yayin da yake Jin asiya Tana cewa bayason abinda zai Taba ta amma just now he's thinking of killing her if har bata daina prying ba, Kai UN
"What the fuck have they done to us..." Yafada new tears na fita idanuwanshi, da sauri ya sake goge su, cikin kuka asiya ta juya ga autarsu Mai suna shamsiya tace
"Yaya bai baki tsoro?.." Ta tambayi yarinyar wacce bata wuce 12 years,
"Nima Ina tsoron shi...." Yar yarinyar ta amsa mata , safwan sake fashewa yayi da kuka, yana ji Inna ta bugi shamsiya Tana cewa
"Wallahi sai kunci ubanku..kar kuja bakinku kuyi shuru..." Tafada masu sounding so pissed off,
"Wai yara basu son karuwar Dan uwar su?.. Lallai ma...", safwan lumshe idanuwa yayi, UVahankali ya sake goge face dinshi Sannan ya taka ya shiga ciki, wasu yanmata né zaune suna Shan ice cream yana shiga suka bishi da kallo,  bai ko kalli inda suke ba ya sayi ice creams da pies da sauran su ya fito, daya daga cikin babe din mikewa tayi tabi bayanshi, Tana hi, sai Kara sauri kawai yake saboda baison magana, Tana ganin bai juyo ba ta koma ciki
"You're lucky am in a good mood..." Yafada yana bude motarshi, yana shiga ciki asiya tayi saurin goge face dinta, ajiye ledar yayi ya juya baya tare da kunna hasken motar, asiya boye face dinta tayi Don kar ya ga face dinta,
"Asiya ..." Ya Kira sunan ta,
"Naam..." Ta amsa mashi,
"Kishiga hankalinki...." Yafada mata atakaice Wanda yasa tsoro Kara Kama asiya
"Me akayi?.." Inna ta tambayeshi sounding so surprised Don inadauwnata duka waje,
"Kawai sai ta shiga hankalinta...." Yafada atakaice yana tada motar, Inna kasa motsi tayi saboda yanda yayi maganar ya tabbatar mata yaji komai, hakan ba karamin bata tsoro yayi ba, tasan ko a jikin mota ya tsaya bai kamata yaji abinda suka ce ba, asiya Kara volume din kukanta tayi saboda ko minti daya bata son karawa kusa da safwan, saga inda yake zaune tsoron shi Kara shiga cikinta. Basu isa gidan ba sai wajen karfi 9, har Inna tsoro ya kamata da taga inda ya dosa a wajen gari, kawai sai take tunanin he can never harm them ita kam asiya har ta fidda rai ga rayuwa Don gani take saidasu zaiyi, yana zuwa wajen wannan gidan ya sauka ya bude gate sai leke suke, dawowa yayi ya shiga dasu cikin gidan dake haske kaman ba dare ba saboda solar, komawa yayi ya kulle gate ya dawo ya bude motar yayi tsaye alaman su fito, jiki na rawa Inna ta fito shamsiya ta fito, asiya kam Tana zaune bata da alaman fitowa ta hada Kai da gwiwa sai hawaye take, a fusace ya zagaya ya bude ya fixgo ta waje ya maida Kofar ya rufe, Inna kam baki ta bude Tana kallon inda suke tsaye
"Safwan..." Takira shi kaman Wanda yayi race saboda yanda take nishi, ba Don komai na sai Don shock din abinda ta gani,
"Ku biyoni..." Yafada yana Kama hanyar part dinsu, Inna data rungume hannunta a chest dinta Tana kalle kalle ta fara takawa kaman Ana ingizata, asiya ma  daina kuka tayi duk idanuwanta waje Tana kallon wannan gidan, duk jikinta yayi sanyi ta bishi, tasan dole yayanta ya shiga wani mugun Abu da zai samu kudi haka cikin kankanin lokaci, ko kadan bata kawo cultism kanta ba, kawai abinda take tunani is fashi da makamo ko kuma kidnapping tunda su suka fi yawa, yana zuwa bakin Kofar dakin ya bude ya shiga cikin falon daya sha gyara kaman bazaka mutu ba juyowa yayi yaga babu Inna ke kallo sai Italian bulb dake tsakiyar dakin, duk reaction dinsu ya tsaya yana kallon har cikin heart dinsu, kannenshi are happy but Banda asiya, Inna is now scared ya ga hakan a heart dinta,
"Nan né bangaren ku...da akwai dakunan bacci guda hudu kowanne da kewaye ciki, Inna ki dauki daya, asiya ta dauki daya shamsiya da bilki su dauki daya dayan kuma a barwa baki..." Yafada yana kallon face dinsu,
"Inna wannan gidan yayi ko a nemi Wanda yafi wannan?.." Ya tambayeta idanuwanshi kanta, Inna kasa magana tayi balle ta amsa mashi,
"Inna kiyi magana in baiyi maki ba zaa samu wani...Sam banason kina kirana matsiyaci,...Sannan inason in dinga samun aduraki " Yafada kaman zaiyi kuka amma  he's face look strong,
"Safwan wannan gidan waye?.." Ta tambayeshi sounding so scared
,"gidana né..." Ya amsa mata atakaice,
"Ina ka samu kudin sayan wannan gida?.." Ta tambayeshi duk idanuwanta waje, murmushi ya saki yana cewa
"Inna. Yanzu ba lokacin tambaya bane...lokacin shagali né...Don haka kiji dadin rayuwa kaman yanda kike bukata...Don ke na zage damtse har nayi kudi haka..." Yafada yana dariyar da bai Kai ko throat dinshi ba, Inna kasa magana tayi Sannan ta kasa moving ko kafarta, fita yayi ya koma cikin mota ya dauko ledar Kayan daya sayo ya dawo ya ajiye masu Sannan yace
"Gashi ...kowa yasha...gobe zan kaiku kasuwa ku sayi duk abinda kuke bukata na abinci ko sawa..." Yafada Sannan ya juya ya bar su nan tsaye,  yana kulle Kofar asiya tayi saurin lekawa taga ya nufi makeken part dinshi da sai yayi ukun Wanda suke ciki, sai da ta tabbatar ya shige tace
"Inna mu gudu...Inna mu tafi kafin gobe da safe..Inna Dan Allah kar mu zauna nan..." Ta fada cikin matsanacin tashin hankali, ko kallon ta Inna batayi ba ta dinga takawa ahankali Tana duba falon, ta taba kujerun ta taba kayan kallo,
Chapter 76 · 0% Book details