← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 162

Sashe 93

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokacin da safwan ya bar dakin Inna, Inna zama tayi Tana kallon shi har ya fita, Tana ganin maigadi ya maida gate ya rufe ta fito da sauri ta Kama hanyar part din safwan, Kofar parlor ta isa Tana kokarin budewa taji shi kulle gam, tsayawa tayi ya rasa yanda zatayi ta bude, maigadi na zaune yana kallonta har ta juya zata fita maigadi yace
"Hajiya ki gwada Kofar baya mana..." Ya fada mata,
"Da akwai Kofar baya né?.." Ta tambayeshi,
"Eh mana...yanda naki yake da wata kofa ta wajen kitchen haka wannan am yana da wata Kofar..." Ya fada mata, cikin ranshi yana aduar ta shiga Don taga if da akwai abinda yake boyewa saboda shima tsoron safwan yake kallon daya yake mashi bai Kara samun karfin halin kallon shi, Sannan shi yana sane da duk yan Matan da yake kawowa gidan,
"Ta wajen Ina zanbi?.." Inna dake zaro Idanuwa Ta tambayeshi, nuna mata yayi yana inda yake zaune yanda ko da safwan ya dawo unexpected ba sai shafe shi ba, jiki na rawa Inna ta zagaya ta inda maigadi ya nuna mata sai sauri take gabanta na faduwa, tasan something is fishy about safwan and tanason ganin ko meye da idanuwanta, wannan ihun dataji jiya ya tsaya mata a rai, Tana zagayawa taga kofa ta saka hannu Tana murdawa ya bude, ji tayi gabanta ya mugun faduwa, ahankali ta shiga ciki Tana waige waige, jikinta sai rawa kawai yake, Kai da danka amma kana fargaban shiga inda yake sabida tashin hankali, kitchen ta fara shiga Sannan ta shiga zuwa falonshi, she was surprised da yanayin falonshi kasancewan bata taba shiga falon shi ba sai a ranar in short bata taba shiga part disnhi ba, the last time datayi knocking ya bude bai barta ta shiga ba ya tare bakin Kofar din kar ta shiga ciki,
"Safwan...safwan..safwan...wannan arziki yayi yawa..." Tafada Tana kallon yanda saki shi ke cike da Kayan duniya kala kala,  kullum Tana tunanin cikin daula take amma Ashe Wanda safwan ke ciki ya linka nata sau goma,
"wannan yaron ka fara bani tsoro..." Tafada Tana tsaye Tana kallon makeken falon, sai wayar dake kan table, ahankali ta nufi wata kofa ta bude taga gadone amma da gani ba'a taba kwanciya samanshi ba, it looks so new and neat, rufewa tayi Tana Jin sanyi na kamata from no where, ahankali ta Kai bakin Kofar da yake ajiye yadi da bag din kudin shi, kafa daya ta saka a dakin taji kaman an daure mata kafa, lokaci guda taji her blood is on her finger tip, wani irin tsoro né da bata San ko na meye ba ya mamaye zuciyar ta, ji take kaman ta gudu sabida tashin hankali, babu kowa dakin amma it seem so full of people, waige waige ta farayi tayi saurin maida Kofar ta rufe, tunda take bata taba Jin abunda taji ba, her whole body was trembling with fear, she's feeling shivering running down her spine, tamkar Tana mayanka haka take ji, daya Kofar ya sake budewa kudin da ta gani yasa taja baya da sauri har tana faduwa kasa, hannunta Dora kan chest dinta idanuwanta duk waje Tana kallo mint din dake gabanta, kudin ya mugun bata tsoro, daga kan gado har kasar tiles duk kudi né, salati ta farayi Tana mikewa tsaye.
Idanuwa duk waje Tana kallon wannan uban kudin da suka amshe koina na dakin, ko kadan bata kawo wa ranta kudin tsafi bane, kawai ta dauka kilan fashi da makami yake ko kuma kidnapping kasancewan su sukayi yawa Yanzun, bata taba tunanin safwan zai salwantar da rayuwar wani ko wata sabida kudi ba, ko kadan hankalinta bai Kai nan ba, jikinta sai rawa yake saboda yanda dakin shi kanshi na tsoratarwa, ahankali ta maida Kofar ta rufe da hannunta kan chest dinta, sai kalle kalle take Tana juyawa da sauri kaman da akwai wani bayanta.  A firgice taso barin dakin ta Kama hanyar kitchen sai wayar dake kan table ya dau ringing, karar wayAr yasa ta Kara firgita ahankali ta juyo ga wayar dake faman Kara, to her surprise sai picture Aisha datayi saving as her screen saver, she was stunned Don har bending tayi Tana kallon wayar dake ringing

"Ai wannan Aisha ce..." Tafada Tana nuna phone din, gabanta né ya sake faduwa da karfi saboda she's thinking me photos din Aisha keyi cikin wannan wayar Sannan Tana tunanin who owns the phone, salati ta farayi Tana tunani kala kala, ahankali ta bar dakin not knowing exactly what to think about, Tana komawa part dinta tayi tagumi Tana tunani
"Inna meye?.. " asiya ta tambayeta , kasa amsa mata tayi Don gani take zai zama abun kunya ita asiya ta rigata gano safwan is into something bad Sannan asiya was trying to tell her amma she won't listen, tasan Yanzu it's a bit late for her amma she have to talk to her son,
Yau kam dr Salem da kanshi ya zo inda rabia take ya dauketa zuwa hospital, bayan sun isa ya dauketa zuwa dakin da ake scanning, shi da kanshi bashine keyin scanning ba sai wasu amma he decided to do it for her himself, bayan sun isa dakin ya umarceta ta kwanta kan gadon, mazurai tafarayi having a negative thoughts, murmushi ya saki yana cewa
"Pls sister relax...dubakizanyi...it won't take time..." Ya fada mata cikin natsuwa, ajiyan zuciya ta saki ta hau kan yar gadon tare da lumshe idanuwa, she regrets wearing gown Don daga rigar ya farayi, da sauri ta bude Ido ta kalleshi,
"Sorry your mistakes..don't wear gown to the scanning room..." Yafada mata, rigar ya daga har sai da yazo wajen cikinta Sannan ya Bari, iska ya fitar Sannan ya juya ga inda suke ajiye man scanning ya dauko ya zubawa cikinta ta Dan saki Kara saboda sanyin abun, maidawa yayi ya rufe Sannan ya dauki Abun scanning ya Dora aci kin yana juyawa ahankali yana juyawa while looking at the scanner, as a doctor bai gane abinda yake gani ba sabida it's too early but abinda yake gani is not one, matsawa yayi kusa da tv din yana kallo sosai har da pointing da finger dinshi trying to count, sai Yanzu ya gane why the pregnancy is coming out fast, baby dake ciki ba daya bane ko biyu, ajiyan zuciya ya saki Wanda yasa rabia bude Ido ta kalleshi Tana cewa
"Da akwai matsala kou?.." Ta tambayeshi Tana kokarin kuka, dariya yayi yace
"Matsala kuma?.. Haba babu matsala...you're alright..." Ya fada mata, Kai ta girgiza mashi daga inda  take kwance Tana cewa
"I saw the look in your face...Wallahi da akwai matsala...Dan Allah kar ka damu kanka.?daman nasan yanda nake Shan wahala kan wannan cikin da wuya ace it's normal..." Tafada hawaye na fita daga idanuwa ta, murmushi ya saki tare dacewa
"Hmmm Lallai you're funny...who told you you're in trouble...cikin fa lafiya lau né..sai dai babyn ba daya bane,..." Idanuwa ta zaro Tana cewa
"Ban gane ba..."
"Yan biyu né." Yayi mata karya Don shi kanshi yasan ba biyu ya gani ba amma he can't say the exact number, kawai he prays she made it,
"Doctor biyu fa kace?.." Tafada Tana kuka,
"Yes mana...it's a good thing..." Ya fada yana goge abin gel dake cikinta,
"Yanzu yaran biyu zai Haifa?.. Yaran wannan azzalumin biyu zan Haifa?.."ta fada cikin matsanacin kuka,
"Ki bar kuka mana...komai na rayuwa da akwai reason...ki dauki hakan as your own destiny...tashi in maidaki gida..." Yafada mata nicely, kuka rabia ta dingayi Tana Dana sanin haduwa da safwan, she hates him as much as she hates herself,
"I want to die..." Shine abinda ta fada cikin kuka, hannunta ya Kama ya zaunar daita Sannan yace
"Kinsan da akwai lots of people da suke kashe kansu batare da Allah yasa wani ya hanasu ba, if har Allah bai yarda kin kashe kanki ba then da akwai dalili..Sannan be happy you didn't commit suicide....ya zakiyi da hakkin yaran dake cikin ki...stop crying ki rungumi kadda kinji kou..." Ahankali ta daga mashi Kai,
"Nagode...Allah ya saka da alkhairi...Allah ya yi maka fiye da yanda kayimin...Allah ya jikan mahaifanka..."
"Ameen ameen sister..." Ya amsa mata, ahankali ta sauka ya maida ta gida.

Yau mamanmu ta shiga gidan Abban Fatima tun da sassafe ta mika mashi dubu talatin Wanda zaayi masu Noma daita Sannan tayi mashi sallama kan zata kasiwar Kano Don tayo siyayyar Kayan da tace zata dinga sayarwa, babu musu ya amshi kudin ya kuma yau mata aduar Allah ya maidota lafiya, fita tayi ya koma cikin gida tayi wa Fatima sallama da gwaggo Sannan suka tafi da daughter dinta yar shekara 19.
Chapter 93 · 0% Book details