← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 162

Sashe 153

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Rabia ta fadawa iyayenta yanda sukayi da salim and farin ciki wajenau bai misaltuwa,  ance Zakara da Allah ya nufa da Shara babu abinda ke hanashi,  da akwai yanmata da dama da basu samu daman da Allah ya bawa rabia ba,  mahaifiyar ta could not hide her happiness,  rabia Kuna farin ciki ya sa babu abinda take sai kuka,  she almost cried her eyes out, sai da aka fara yi mata fada sosai sannan ta daina,  har cikin ranta ta ji haushi da tsanar safwan ya fita ranta,  Allah gave her a second chance with the man da ba kowacce mace ta isa taje inda yake ba,  so shima safwan deserve her forgiveness,  kallon yaranta dake zaune kasan suna wasa tayi ta saki murmushi,. "Allah yayi maku albarka farin cikina... I have come to love you all...nasan zina bashi ne amma Allah kar ya sakawa wasu da ku.. "tafada hawaye na gangarowa daga idonta,  duk sanda ta tuna her children might be object of molestation sai taji gabanta na mugun faduwa,  tasan Allah ba azzalumin sarki bane and she's scared of what might happened,  a da bata damu da yaran ba amma with time sun shiga jininta sosai,  abun da ke b'ata tsoro shine tasan ba ita kadai ce victim din Safwan ba, tasan da akwai wasu da dama chan wani wajen crying for vengeance kaman yanda itama tayi kukan Allah ya saka mata
"rabbi ka tausaya masu... "shine abinda ta fad'a cikin hawaye,  yaran kam basu San abinda take fadi ba Sai wasan su kawai suke suna dariya looking so adorable,.

Dr tun kafin yazo wajen ya rabia yayi mata maganar aure ya fadawa dad da mom dinshi,  babu abinda suke sai  sa Mashi albarka for yanda Allah ya bashi zuciya Mai kyau,  sun bashi hadin kai dari bisa dari,  Don haka yasan wannan is a side sai Kuma matarshi.wajen asuba tana zaune kan wani Italian bed wanda ko makaho ya shafa yasan an zuba millions wajen siyansu, ta hada kai da gwiwa sai kuka take,  Dr zaune kusa daita sanye da kayan bacci yana magana ahankali bakajin abinda yake cewa, b'ata daga kai ba sai shessheka kawai take,  rarrashinta kawai yake with sweet and lovely words da ya kamata miji yayiwa matarshi in Allah ya kaddara zai karo aure ba munana mata ba,  he's telling her she's more precious than anything and auren da zai karo is bisa kaddara, ahankali ta daga kai ta rungumshi tana kuka,  she's so beautiful and perfect,  shafa bayan ta kawai yake yana cewa
"kiyi min Allah yaisa in har ba shiga hakkin ki in any way ..."yafada kaman zaiyi mata kuka too, 
"I won't... Nasan you will do the right thing... "tafad'a cikin kuka,  kiss yyi kan silky night gown dake jikinta tare dacewa
"thank you for trusting me... "ya rada mata, Cikin kuka tace.
"Dan Allah zan nemi alfarma daya... "
"pls say it what ever you  want is all yours... " yafada mata calmly,  cikin kuka tace
"pls... Nasan gidan is well enough for mata har hudu... Amma pls ka rufamin asiri kar ka kawo ta nan... Wallahi I cant watch you go into another woman's apartment... "tafada cikin kuka sosai,  silky head dinta ya shafa yace
"no problem..  Bazan kawo ta nan ba... Zan kaita gida na biyar on the street... Hakan yayi maki?.. Banason kaita nesa saboda yaran... Inason family dina su zama daya especially yarana... Kaman yanda step mom dina ta zamemin uwa haka nakeson yarana suyi mom biyu at both side... "kai ta daga mashi alaman ta yarda. He was so happy,  maryam tana da kishi sosai amma with he's prayers it come easy sannan  Allah yaga zuciyar shi and he made he's worst fear simple.

Yau sati guda kenan da safwan da Nana sukayi maganar zuwa gidan su rabia  tare,  amma bai Kara maganar ba Don he's afraid taje aci mata mutunci,  yau da asuba bayan sunyi sallah tace
"baby pls yau muje gidan nan... "
"wane gida... "ya tambayeta with he's eyes closed,
"gidansu rabia... "
"baby are you sure you want to go?.. Banason aje a fada maki magana Don kinzo neman rabia... "
"kome zaa fad'a min zan dauka indai zamu samu inda take... Pls don't say no... "tafada mashi
"I won't say no... Kawai dai banson Ranki ya baci ne... "
"pls don't say that... Nidai in munyi breakfast muje daga nan ka wuce office... "
"baby breakfast AI safiya ce..why not bayan lunch... "kai ta girgiza mashi tace
"aa kawai zuwa 10 muje... Pls... "
"OK shikenan.."ya amsa mata. Dukda baison zuwa haka ya shirya wajen karfe 11suka shiga part din  Inna sukayi mata sallama ta fito cikin Arabian gown Wanda in ta Dan ratsa cikin rana sai jikinta yayi walkiya saboda expensive stones dake jiki,  safwan na sanye da expensive gezner looking dull.
Shi da kanshi ke tuki yana shiga Unguwar old life dinshi ba dawo mashi,  kaman ya fad'a mata this is where he grew up amma yasan hakan will cause lot of questions which answering them will be equal to he's death,  har bakin gate dinsu ya zo yayi parking, yasan in har ya fita zaa samu wayanda zasuyi mashi magana Don duk yanda zaKa sauya  wayanda suka San yarintar will always recognize you,  nuna mata gidan yayi tazo fita yayi saurin riketa tare dacewa
"pls... In sunce basu San inda take ba don't stress it... Kawai ki fito kinji kou... "yafada cikin sanyimurya
"pls relax... Insha Allah sai na gano inda take... Don haka kawai ka kwantar da hankalin ka... " bai saketa ba yace
"baby they're angry parent,children ,wives who lost their husband, father as a results of abinda nayi mata.. Ba lallai su saurareki ba... So pls don't force them kinji babyna?. "ahankali ta daga mashi kai tare dacewa
"shikenan.. I will do as you said... So don't worry... "tafada tana sauka daga motar, ahankali ta taka tazo bakin gate din ta tura taga it's open ta shiga, abinda ta fara cinkaro dashi yasa jininta tsinkewa Don Muhammad ne tsaye da kwallo hannunshi, dukda batasan who own the child ba remarkable resemblance dinsu da safwan is out that kallon daya zaka mashi ka gane danshi ne ko kuma he's family, kasa tafiya tayi ta tsaya Tana kallonshi, alhankli yake tafiya kaman he's afraid of touching ground, Nana kasa tafiya tayi ta tsaya tana kallon yaron daya juya mata baya yana shigaciki, kaman ta gudu ta daukeshi ta kaiwa safwan haka take ji, amma that won't make good impression. Ajiyan zuciya ta saki tabi bayan Muhammad tare da yin sallama.
Chapter 153 · 0% Book details