← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 162

Sashe 90

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hospital kam Yanzu satin habib biyu da some days, har Yanzu bai magana ko wani Abu but ya kan bude idoshin ya dinga kallon mutane for some time Sannan ya maida su ya rufe gam, daga inda yake kwance alhaji bello ke bashi liquid abu kaman yanda Doctor ya bukata, at times zai amshi kadan Sai kuma ya fara kauda Kai alaman he's ok, he's healing very fast sabida irin drugs da ake bashi through injections, Yanzu babu wannan Kayan na mahaukaci jikinshi, yana sanye pure white cloth da hospital din suke bawa patients dinsu Sannan an ansake mashi wannan hairy face dinshi Wanda ya bayyana slim face dinshi, yau alhaji bello na bashi wani Abu cikin cup mufida ta shigo hospital din rike da basket na abinci, gaisa dad dinta tayi Sannan ta bukaci yaci abinci,
"Dear don't worry zanci if ya gama Shan custard din nan..." Alhaji bello ya amsawa mufida, bakin gadon mufida ta dawo Sannan tace
"Daddy kawo in bashi Kai sai kaci abinci..." Tafada Tana kokarin amsar cup
Dake hannunshi, babu gardama ya sakar mata ya Mike ita ta zauna da cup din hannunta, driver dinsu ya dauki basket din abincinshi suka fita dashi zuwa dakin Doctor da yake cin abinci. Ahankali mufida ta dinga feeding dinshi yana kwace duk wmada ya zuba ko a chest disnhi ko a kayanshi, bayan kaman minti talatin Doctor ya shigo, lokacin mufida ta gama feeding dinshi, kallon shi Doctor dake rike da wani Abu na observation yayi yana cewa
"Malam how are you today?.."ya tambayeshi ahankali Don kullum kokarin su yayi magana amma  he's not saying a word, idanuwa habib ya daga ya kalleshi  before saying
"Fine." Ya fada cikin low voice, idanuwa mufida ta zaro tare dacewa
"Doctor he talked kou?.." Ta tambayeshi out of excitement, murmushi kawai Doctor yayi without looking at her,
"Good...now tell me inane ke maka ciwo?.." Ya tambayeshi ahankali habib ya daga hannu ya nuna kanshi,
"Ok ..." Doctor ya fada Sannan ya rubuta wani Abu ya sake kallonshi yace
"Can you sit up?.." Ya tambayeshi, habib shuru yayi ya rike bedsheets gam da both hands dinshi yana sauke legs dinshi ahankali, mufida mikewa tayi tsaye Tana kallon shi face dinta dauke da farinciki, habib dagewa yayi har saida ya sauke legs disnhi kasa ya Mike zaune, sai biting small lips dinshi yake da gani he's feeling pain, kofa aka bude alhaji bello ya shigo, surprise look né kwance kan face Dinshi, babu Wanda yake kallo sai habib dake zaune, tunda yake bai zama saidai ayi positioning gadon in zaa bashi abinci,
"Wa ya zaunar dashi?.." Shine tambayan da alhaji bello yayi masu, da sauri mufida tace
"Daddy da kanshi ya zauna.. Can you believe that?.." tafada har da jumping saboda Jin dadi, Kai alhaji bello ya daga sama yace
"Alhamdulillah...alhamdulillah..." Yafada kaman zaiyi kuka,
"Now kana Jin duk Abunda nake cewa?.."  Doctor ya tambayi habib,
"Eh.." Habib ya amsa mashi, Banda bakinshi  da yayi motsi ba'a ganewa yayi magana sabida he's voice is not coming out, yanda mufida da alhaji bello ke kallonshi ko mirror albarka, it's as if suna ganin wani strange abu for the very first time,
" tell me meye sunan ka?.." Doctor ya sake tambayan shi yana kallon bakinshi saboda kar yayi magana baiji ba, shuru habib yayi trying to remember he's name amma noway, Idanuwa ya lumshe ya Dora hannunshi Mai cannula a Kai,
"Malam tell me your name..." Ya tambayeshi,
"My name?.." Habib yafada cikin low tune,
"Yes your name..." Doctor yayi repeating, alhaji bello rike waist yayi yana tunanin Yanzu he's educated amma he was mad, only Allah knows number of educated people wasting on the road, idanuwa ya lumshe yana sake godewa Allah daya bashi ikon haduwa da Just one of them,
"Tell me your name?.." Doctor yayi repeating,
"I...can't...remember..." Habib yayi counting words din, mufida was speechless sabida yanda yayi turanci, baki ta rike Tana kallonshi,
"Do you remember daga inda kake?.." Doctor ya sake asking, shuru habib yayi for a moment Sannan yace
"no..." Ya amsa idanuwanshi lumshe,
"Ok...relax..you will be alright..." Doctor ya fada mashi, ahankali ya maida legs dinshi kan gado ya ya koma ya kwanta, temporary memory lost Doctor ya rubuta sannan ya fita wata nurse that has been standing there tabi bayanshi, ahankali alhaji bello ya taka zuwa bakin gadon ya kalli habib, shima habib daga idanuwanshi yayi ya kalleshi, alhaji bello ji yayi ya mugun bashi tausayi,
"Sannu kaji..." Alhaji bello ya fada mashi,
"Yauwa..." Habib ya amsa idauwanshi cikin na alhaji,
"Am sorry...I have put you through a lot...insha Allah I will make you you're alright..." Ya fada mashi, ahankali habib ya saki kasaitacen murmushi da despite he's head is so tied up in bandage da kuma duk ramar da yayi sai da ainahin handsomeness dinshi ya bayyana, murmushi itama mufida ta saki tare dacewa
"Sannu Dan uwa..Allah ya Baka lafiya..." Ta fada cikin matsanacin farin ciki dake rubuce a face dinta,
"Nagode.." Ya fada ahankali,

Finally dr salim ya samowa rabia wata mata dake kula daita and shima dukda he's busy yana Dan samun time yana zuwa ya duba lafiyarta Dana Abunda ke cikinta, ba karamin wahala rabia ke sha ba Don tun cikin bai Kai koina ba ta fita hayyacinta ta rame tayi baki kaman baita ba, despite wahala da ciki ke bata bai hanata kukan nadama da kuma tsinewa safwan ba, she curse him morning afternoon and night, har matar dake kula daita taja mata fada kan she should have a forgiving heart that duk nauyin zunubin mutum indai zai nemi gafara zaa yafe mashi, Don haka itama ta nemi tuba ba tsinewa wani ba, itadai rabia bata dainawa saboda yanda zuciyar ta ke radadi, in matar Ta tambayeta abinda yasa take wannan tsinuwa haka sai ta yi shuru without saying a word Don matar bata San ba matar Doctor bace ita, yauma Doctor ya shigo gidan wajen karfe 4 na yamma da Kayan fruits da yawa cikin Leda daya Sai kuma Kayan magani da drips cikin Dayan leda  kasancewan kullum sai yayi mata Karin ruwa saboda bata cin abinci, Mai aiki ya mikewa Ledan fruit Sannan shi ya shiga dakin da rabia take kwance face dinta sharkfa da hawaye, Kai Doctor ya girgiza tare dacewa
"Ke baki Jin magana kou?.. I have told you several times banason kina kuka..it's not good for your health da kuma na baby..amma duk Sanda zanzo sai na tardaki kina kuka..gaskiya zamu bata dake if baki daina ba..." Yafada yana zama bakin gadon da take, ahankali rabia ta Mike ta zauna Tana goge hawayenta
,am sorry..  " Ta fada ahankali,
"Stop saying sorry..kawai,ki daina kuka..." Ya fada mata atakaice,
" tou..." Ta amsa mashi,
"Good..tell me how is you and your baby..." Ya tambayeta, shuru tayi Tana goge face dinta, murmushi ya saki yana kallon cikinta, yana mama kin how it's growing fast, from calculations din da sukayi daita, it seems tun first sex da sukayi da safwan ta samu ciki and duk baifi 2 months and few days ba amma cikin kaman ya Kai 4 months Sannan kuma yanda it's her first pregnancy bai kamata ace ya fita da wuri haka ba, kawai sai ya danganta cikin da kuma ramarta, kawai he's thinking cikin is coming out fast saboda ita uwa ta rame da yawa,
"I think we should have our first scan ..ko ya kika gani?" Ya tambayeta, dukda da wuya suyi scanning at the early stages amma haka nan kawai he wants to know why,
"Duk yanda kace.." Ta fada ahankali,
"Gobe Insha Allah zanzo in daukeki..sai in kaiki hospital..Yanzu dai let me give you your food..." Yafada yana mikewa with a smile on he's face, Leda daya kawo ya bude ya dauki drip ya ajiye a inda yake ajiye mata Sannan yayi mata fixing ya koma gefe yana jiran ya kare kafin ya tafi gida,

Itama Fatima nata cikin is growing in a way it should, in ba face dinta ka kalla ba you will never know she's pregnant, cikin ta is the best thing that ever happened to mamanmu, shiyasa Yanzu ta rage damuwa sosai ta maida hankali wajen kula da Fatima, Yanzu Tana fita har kasuwa Don ta samo mata Abunda taga Tana bukata, wannan kudin da habib ya bar mata take amfani dashi wajen kula daita inda har ta kashe kusan 20k. Sauran kudin ya rage masu 150k Don ciki suke cin abinci da sauran Abinda suke bukata, gani tayi if ta ajiye kudin iya hallaka kudin kuma in ya kare basu San yanda zaayi su samu wani ba, hakan yasa ta zauna ta yanke hukuncin ta fara sanaa da 100k Sai kuma ta ta ajiye 30k ayi masu Noma tunda an fara Sai kuma sauran 20k ta sayi Abunda zasu dinga ci, first Abban Fatima was the first datayiwa wannan maganar kuma ya dauki hakan as a good start, ganin Fatima is also like habib to her, dukda karancin shekarunta haka mamanmu ta zauna ta fada mata Abunda take son yi da kudin dake hannunta, bayan mamanmu ta gama fada mata komai, bata ce komai ba ta Mike ta dauko sauran 40k da habib ya bata ta mikawa mamanmu, mamanmu was surprised inda ya tambayeta where she gets the money from, nan ya fada mata cewa habib ya bata kyauta,
"Tou ki ajiye..tunda ba komai kike iya ci ba..sai ki dinga cin Abunda kikeso ciki...in Allah ya yarda in saki haihu sai a kawo saura ayi siyayyar Haihuwa..." Inji mamanmu, ahankali Fatima ta girgiza mata Kai tare dacewa
"Aa mamanmu..kawai ki Kara da jalli..." Ta fada mata. After few argument mamanmu ta amsa ta cire 10k cikin kudin ta bata, Sannan ta rike sauran 30k, shima 10k din da kyar Fatima ta amsa, saida taga ran mamanmu sai bace ta amsa.
Chapter 90 · 0% Book details