← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 162

Sashe 31

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safwan na dawowa daga inda aka Kai yarinyar makwancinta ya shiga dakinshi ya debo kudi masu uban yawa Sannan ya turasu cikin aljihunshi ya fita daga cikin dakin ya maida kofa ya kulle, cikin gida ya shiga ya tarda Inna na hura wuta while sister dinshi Tana wanke wanke, hannu ya saka cikin aljihunshi ya debo wannan kudin da bai sani ko nawa né ba ya mika mata, da sauri ta daga Kai tace
,"ya uwa Dan albarka...ko kaifa,.." Ta amshi kudin tana mikewa,
"Ki dafa abunci ki Kai gidan rasuwa...zan fita..." Yafada mata, bata fuska tayi tace
,in na dafa abinci cikin wannan kudin ai sun kare,.." Tafada alaman she don't want to cook from the money, idanuwa yayi rolling Sannan ya sake saka hannu cikin aljihunshi ya debo wasu kudin yace
,"ya isa ko a Kara?.." Ya tambayeta Kai tsaye, da sauri ta sake amshe kudin Tana cewa
"Nayi maneji..." Tafada kaman kudin basu isheta ba,
"yaya wannan kudin haka kaman banki?.." Kanwarshi tafada mashi, daure face yayi baice komai ba ya fice daga gidan, bai Kara cewa komai ba ya fice daga cikinshi, what he saw scares the hell out of him, habiba ce ya gani tsaye cikin dakinshi sanye da Kaya fari tas from head to toe ihu ya saki da karfi yana fita daga dakin da gudu.
Shima usman was successful wajen kiran wata cousin dinshi yayi yace tazo zai aiketa, the same thing da safwan yayiwa wannan yarinyar shima yayi mata.11💜💚💛❤️💙
Sirrin wasu gayun
💜💛💙💚❤️

® zuwairat (ummumaryam)

1️⃣1️⃣

Don't read if you didn't pay, if you do you owe me.
Karki karanta baki biya ba Don in kin karanta kin biyoni

Dedicated to my anty. May all the good things comes your way.ameen

Da ihu safwan ya shiga cikin gidansu mutane dake zaune waje kalleshi sukayi amma dayake taki daya yayi ya shiga gida babu Wanda yasan if he's really shouting ko kuma kawai kunnen su né, Inna dake zaune Tana arranging kudin da safwan ya bata Don tasan exact amount din tayi saurin daga Kai ganin mutum da gudu, da sauri itama ta Mike tana cewa
"Biyo ka akayi?.." Ta fada Tana kallon zaure ko zata ga mutum amma ba komai, safwan dake nishi saboda tashin hankali sai leka Kofar waje yake,
"Na shiga uku..." Ya fada cikin tsananin tashin hankali, sister dinshi rikeshi tayi yana tambayar
"Yaya lafiya..." Ta tambayeshi itama Tana kallon waje, Inna ma Tana gama leko zaure taga babu kowa ta juyo gareshi Tana cewa
"Nace ubanwa ya biyo ka?" Ta tambayeshi sounding so angry, nishi kawai safwan yake saboda tunda aka haifeshi he has never been this frightened,
'"Wai Dan ubanka bazaka fadi abinda ke damunka ba?.." Ta daka amshi tsawa, sister dinshi rikeshi tayi Tana cewa
"Inna ki bishi a hankali mana...baki ganin ki magana bai iyawa..." Bata karasa ba Inna ta dungureta a goshi Tana cewa
"Dalla rufemin baki ..." Ta fada Sannan ta sake juyawa ga safwan da har lokacin idanuwanshi Kofar shiga gidan yana ganin kaman zaiga habiba,
"Wai ba da kaineke ba.." Ta daka mashi tsawa, ko jinta baiyi balle ya amsa mata, nishi kawai yake, tsoki Inna taja ta koma baya ta zauna ta inda take in the first place ta cigaba da counting kudi ta hankalinta jwnace, jiki na rawa safwan ya koma ya zauna nan kasa sai sakin ajiyan zuciya kawai yake, yanda ya zaro idanuwa is a thing that calls for concern amma Inna zama tayi Tana  gyara kudin Tana counting kaman ba danta bane zaune duk ya fita hayyacinshi, ahankali sister dinshi ta durkusa ta Dora hannu a shoulder dinshi yayi saurin Jan baya yana kallon ta, alaman he's frightened of her touch
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun yaya Dan Allah me ya faru... Gamo kayi?.." Ta tambayeshi cikin kulawa, Inna daga Kai tayi ta kallesu ta saki tsoki ta maida hankali kan abinda takeyi, safwan kallon sister dinshi yayi da red eyes dinshi ya ce
"asiya..." Ya Kira sunan ta kaman bashi ba,
"Naam yaya..." Ta amsa mashi hannunta kan shoulder dinshi,
"Dan Allah dauko min wayata..." Yafada still panting,
"Yana Ina?.." Ta tambayeshi,
"Dakina..." Ya amsa mata atakaice, mikewa yarinyar tayi ta shiga ciki ta dauko hijab dinta daga cikin daki Sannan ta Kama hanyar waje, har ta Kai bakin zaure safwan ya tuna da da kudin dake dakin sai yace
"Minti daya na baki kidawo...wayar Tana kan katifata,...in kin dauko ki kullemin Kofar..." Yafada mata, Inna daga Kai tayi ta kalleshi tace
"Ko ma meke damunka kanka kadai zai kare..." Tafada mashi Tana kallon yanda ya susuce, daure fuska yayi tare da kauda kanshi gefe, bayan kaman minti daya da rabi yajita shuru,
"Asiya!!!" Yafada da karfi kar taje tayi mashi bincike, sake kallon shi Inna tayi ta Galla mashi harara ya dauke kanshi, da sauri asiya ta fito rike da wayar ta kulle Kofar ta shigo cikin gidan
"Dan uwarki me kika tsayayi cikin dakin?" Ya daka mata tsawa
"Kai dai atakaice so kake ka zageni kou?.." Inna ta fada sounding angry, ko kallon inda take baiyi ba yacigaba dacewa
"Baki jina da uwarki?.." Ya sake daka mata tsawa, rawar jiki asiya ta  farayi Don tunda take bata taba ganin yayanta haka ba, Inna kam Kama baki tayi Tana salati,
"Yaya mukullin na nema.." Asiya Ta fada jikin cracking voice, harara ya watsa mata tare da Inna Sannan ya mika mata hannu yana cewa
"Kinga kowa dakin?.." Ya tambayeta, sauri ta girgiza mashi Kai Tana takowa ta ajiye wayar da makullin dakin a hannunshi Sannan ta juya, har lokacin bata daina tunanin halin safwan ba, tunda suke dashi bai taba zaginta ba sai yau, Sannan bai yarda ayi zagi a inda yake amma yau sau gashi yana Burma  mata zagi, Dan juyowa tayi ta kalleshi suka hada Ido ya zaro mata idanuwa tare dacewa
"What?.." Ya sake daka mata tsawa, bata San yana da manyan idanuwa ba sai yau, yanda ya zaro idanwaun tamkar zasu fito waje, da sauri ta dauke kanta gabanta na faduwa, Inna girgiza Kai tayi Tana watsa mashi kallon haushi da takaici, number alhaji idris yayi dailing yana mikewa domin shiga dakin Inna, yana kaiwa bakin Kofar ta tayi saurin cewa
"Wallahi kar ka sake ka shigar min dakin Dan ubanka..." Ta fada a fusace, baki ya tabe ya juya ya shiga dakin su asiya ya zauna kasa yana jiran alhaji idris yayi piçking calls dinshi, har ta tsinke bai daga ba, tsoki safwan yaja yana cewa
"Dalla banza pick up..you just got me messed up..." Ya fada yana sake dailing number dinshi, saida ta kusa tsinkewa Sannan alhaji idris yayi piçking
"Alhaji I saw the girl I used..." Ya fada voice dinshi na rawa, dariya alhaji idris yayi Sannan yace
"Relax..wannan ba wani Abu bane...dole tayi hunting Dinka..."
"Inna lillahi...you have finished me,,,.you know spirit will hunt me amma you don't bother to tell me...now what am I going to do..." Yafada cikin tsananin tashin hankali Sannan yana maganar a cikin harshen turanci don kar kowa yaji,
"I said you should relax..." Alhaji idris ya fada sufwan bai Bari ya karasa ba ya daka mashi tsawa dacewa
"The hell I should relax...am telling you i saw a ghost and busy telling me to relax..." Yafada cikin ihu Wanda yasa Inna da asiya kallon junansu,
"Kai stop shouting at me...kar ka Kara..." Alhaji idris Yafada sounding angry, idanuwa safwan yayi rolling Sannan yace
"Sorry..am disturbed that why..."
"then ka jira kaji abinda zance maka...she will go away...but if you keep on getting scared you might run mad..." Idanuwa safwan ya zaro Jin an ambaci madness
"You have finished me,,," Safwan Yafada yana kokarin kuka,
"Haba just relax..." Harara safwan ya watsawa wayar yana kokarin maida hawaye dake neman zubo mashi
"Show you don't care about her...It's what will show you're ready to be in the brotherhood,...ba'a bukatar matsoraci..it's meant for real men..so just act as if you don't care about her,..." Inji alhaji idris
"We're talking about ghosts here...how can I be a man with a ghost..." Yafada yana Danasanin yin Abunda yayi
"If you're not scared of her she will go away...remember the enjoyment with money in our possession...remember the classy things you can do with money...and on the other side remember where you will be sleeping if you run mad...so the choice is yours..." Yafada mash yana kokarin katse wayarshi safwan yayi saurin. Cewa
"Anymore surprise?.." Ya tambayeshi
"No...it's only the first one...daga ita no one will hunt you ever again..."
"ok...then when will you send a driver..." Safwan ya tambayeshi
"Later in the night..." Ya amsa mashi atakaice Sannan ya katse wayarshi, safwan lumshe sai hawaye, at a moment sai yaji kaman an cire mashi yanar face dinshi, he was reflecting on abinda yayiwa habiba, then the other second the thinking was over, goge face dinshi yayi yana cewa
"No to poverty..I absolutely no to poverty...i will never again go backwards..." Yafada face dinshi kaman bai taba dariya ba, sai da ya tabbatar ya goge face dinshi, Sannan ya Mike yau fita daga dakin,. A compound kam ko kallon fuskar kowa baiyi ba balle yaga irin kallon da Inna take mashi, Dakinshi ya koma yana faduwar gaba amma he has promised himself never to be scared again with confidence ya bude Kofar ya shiga ciki she was still there, ko faduwar gaba baiyi ba ya dake ya nufi inda daya daga cikin bag daya saka kudi yaje ya dauki daya, spirit din habiba was still standing by wishing she can revenge what he did to her, ficewa yayi daga cikin dakin ya maida Kofa ya kulle, hanyar gidansu usman yaje ya tardashi zaune yayi tagumi yana jiran shima ya fara ganin alert, yana ganin safwan yayi saurin cewa
"Ina zaka..." Ya tambayeshi,
"hutawa..." Ya amsa mashi atakaice,
"Muje tare...nidai nayi da murja tun dazun Ina jira babu alert..." Dariya safwan yayi yace
"Muje tare mana..." Da sauri usman ya Mike ya sake Kaya suka fita daga unguwar.
Chapter 31 · 0% Book details