← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 162

Sashe 127

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har wajen karfe 12 Adam bai kwanta ba, kishi ya rufe mashi ido yana zaune yana jiran mutanen gidan suyi bacci sannan ya shiga part din amra, he's heart was as strong as stone da bai tsoron dauke ran yar uwarshi. After 12 ya fito ya shiga part dinta, lokacin amra that have been having sleepless night for something was fast asleep, yana shiga dakinta ya dauki pillow ya danna kanta dashi, duk harbe harben da take bai sa ya Bari ba har sai da yaji ta bar motsi sannan ya ajiye pillow gefe daya ya bar dakin, she looks as if she's sleeping but she's no more.
Baa gane amra is dead ba sai da aka zo breakfast aka tardata lifeless, afra data fara ganinta ihu tayi ta yanke jiki ta fadi, Mai saa kam hospital aka kaishi Don kasa numfashi yayi, he can't believe this is happening to him, yana farfadowa Safwan ya kira yana ihun what have done to amra that killed her, Safwan kuka ya farayi ya San Adam ne, yaga that intention in him amma he never knew he will do it. Daga gida direct gidan yazo yaga mutane cike babu inda zaa saka kafa abunka da Mai kudi. Mai saa na hospital aka Kai amra makwancinta, yana shiga gidan ya sulale da red eyes dinshi ya shiga part din Adam, har lokacin Mai. Saa na hospital, direct ya shiga bed room din Adam ya dinga hadashi da bango yana cewa
"how could you... How could you... "kawai yake maimaitawa yana dukanshi, Adam na kuka yana cewa
"I don't know what came over me... Wallahi I couldn't help it... Am regretting... "yafada cikin matsanacin kuka, safwan zama yayi kasan dakin yana kuka, kawai yasan wannan mutuwa shi akayiwa, yasan he loves amra Don bai taba tunanin yarinya kaman yanda yake tunanin rayuwa daita ba, yayi danasanin saduwa da Adam.
Saida Mai saa yayu sati guda a hospital ya dawo gida shima ba Don ya samu lafiya ba, he felt the best part of him is gone, before ya zargi Safwan amma kullum safwan sai yaje wajen shi kuma yanda ya nuna damuwa kan mutuwar amra yasa ha yarda babu wanda ya Kasheta.

Yau sati biyu da mutuwar amra Safwan na zaune a office so lost in thought, kullum sai yayI tunanin amra, secretary dinshi ne ya shigo tare dacewa someone wants to see him, bai nemi yaji suna ba yace
:"let them in... "ya fad'a atakaice yana tagumi, bayan secretary ya koma afra ta shigo, he was surprise by her visit, never knew it was her, kanta kasa tazo ta zauna tare da gaisheshi, he have read her thought already and he was surprised
"me zaa kawo maki..."was abinda ya fada mata bayan ya amsa gaisuwanta,
"nothing... "ta amsa mashi kaman she's afraid,
"alright then.. How may I help you... "ya tambayeta, shuru tayi har saida ya sake tambayan ta sannan tace
"pls kayi hakuri...wani abune cikin raina.. I have tried to hide it since the demise of amra anma na kasa... "sai kuma tayi shuru, he knows everything but wants to hear her say it
"go on... "ya fad'a mata,
"nace tinda muna kama da amra.... And you... Love amra... Can you pls... Love me... Too?.. "ta fiddo maganar seperately, shuru yayi yana kallon ta, da gaske suna kama amma she's nothing like amra, ganin baiyi magana ba yasa ta daga kanta da idanuwanta full of tears tace
"pls..walahi sonka nake... "tafad'a Tana fashewa da kuka,
"pls ki daina kuka... You're a lovely lady.. Babu namijin da zai k'iki..saidai kinsan matsalar da muka samu da mahaifinki kafin ya amince da maganar amra...i don't have Time for any trouble now...kije kiyi magana da mahaifinki.. In ya amince I will marry you... "ya fada mata atakaice, murmushi ta saki da wet face dinta Tana biting lips dinta. Wayarta ta fiddo ta ajiye mashi tare dcewa
"bani digits dinka... "ta fad'a mashi, babu musu ya dauki phone dinta ya saka mata number sannan ta Mike ta bar wajen Tana tunanin how she's going to battle her dad har ya amince, Safwan relaxing yyi yana tunanin halin yanmatan yanzu, kawai har ya hango yanda Mai. Saa zaiyi in afra ta Kai mashi such issue. He will really want to have her as a Wife because she's classy fierce as he wants he's lady tobe, tunawa yayi da baraka sai ya daure face dinshi, yanzu satinsu biyu and some days amma bai kara sakata a ido ba as baj kara zuwa part dinta ba,
"kawai tazo ta mamayemin wajen mata na hudu.. Dole uku zan kara bayanta.. Zaki ci ubanki ne... "yafada sounding angry.

Mai saa da tunda amra ta mutu bai dawo daidai ba yana zaune yayi tagumi sai hawaye yake, hannun shi dauke da cannula Don har lokacin he's still on medication, kullum sai anyu mashi Karin ruwa Don shine abincinshi, he looks so pale and disturb, har yau baisan aihanin reason behind amras Death ba, sallama akayi afra ta shigo, daga Kai yayi ya kalleta tare da sakin murmushi, itama murmushi ta saki sannan ta zauna kusa dashi tana cewa
"Daddy ya jikin?.. "ta tambayeshi cikn so da kauna,
"alhamdulillah... "ya amsa mata cikin sanyimurya da duk wnada zai ganshi sai yaji tausayin shi sboda halin da yake ciki,
"dad I have something I want to tell you.. Kayi hakuri kar kaga rashin hakurina... "ta fad'a mashi Kai tsaye, kura mata ido yayi not knowing inda ta dosa
"baby baki ganin bani da lafiya... If kinsan abinda zai bata min rai ne pls don't say it... "ya fad'a calmly,
"daddy ni mutuwa zanyi if ban fad'a ba... Kawai do the listening while I do the talking... "ta fad'a Kai tsaye, daman attitude dinsu yasa yafison amra cikin yaranshi duka, bata taba yi mashi gardama ba sai a zamanin Safwan, amra is the opposite of afra,
"nikam menene wannan abu that if baki fad'a ba zaki mutu?.. "ya tambayeta yana kallon face dinta, Dan boye face tayi tace
"ni daddy.. Tunda Allah bai amince amra ta auri safwan ba... Dan Allah ka amince ya aurenj..."AI alhaji na jin sunan Safwan cikin zancen ya fara coughing da karfi jini na fita daga bakinshi, wani irin bugawa yaji heart dinshi yayi da jin Safwan, da sauri afra ta dauko ruwa ta na bashi amma bai amsa, hannunshi kan zuciyar shi, sai gudan gudan jini ke fita daga bakinshi, da sauri ta dauko tissue ta bashi sai yamuste face take da alaman Tana jin kyarmar aman jinin dayake, ko maganar ta kira mashi doctor batayi ba tayi tsaye kanshi har sai da ya Gama amai yana sakin ajiyan zuciya ta sake cewa
"daddy kaji...baka ce komai ba.. "ta fad'a sounding carefree, cikin nishi yace
"pls later... "yafada da kyar kaman he's learning how to talk, mikewa afra tayi fa fara buga kafa kasa tana cewa
"nidai just say yes mana.. Wallahi ni in baka ce yes ba mutuwa zanyi in bi amra... "Tafad'a kaman zatayi kuka, still wani cough ya farayi ta Dan ja tsoki tare daceaa
"just for you to say yes sai tari kake... Na tafi later zan dawo... "ta barshi yana vomming din jini har a jikinshi, da kyar ya samu ya kira doctor.
The following day bayan ya Dan samu sukuni kadan ya kira Safwan kan ya sameshi a hospital. Safwan yasan abunda ke nan kuma with confidence ya zo, lokacin doctor ya gama fadawa mai saa dole yaje kasar waje a dubashi sosai a bashi what he needs. Safwan na shiga Mai saa ya daga weak eyes dinshi ya kalle shi tare dacewa
"me nayi maka That zaka biyani da haka... "yafada ahankali saboda an hanashi magana da karfi,
"me nayi again.. If it's about afra kayi hakuri.. Ita da kanta ta sameni da magana.. Don haka na fad'a mata ta nemi amincewarka.. That's all... "yafada sounding truthful, hawaye Mai saa ya farayi yanacewa
"wannan wave irin jarabawace...na killace yarana... Komai lafiya lau.. Tunda nake rayuwata van taba samun kalubale haka ba... The only mistake I make was making you out into the real world.. Amma bayan duk taimako danayi maka da haka zaka saka min... "yafada yana hawaue hannunshi kan kirjinshi,,
Tofa... laifina zaka gani kenan... Why are you seeing me as a mistake?.. Hmmm babu komai.. Tell your daughter to stay away from me... "Safwan ya fad'a yana mikewa,
"she's threatening to kill herself...i can't loose another daughter.. Don haka kawai ka aureta.." bai karasa ba Safwan yace
"aa... Ni ban aurenta... Kawai Allah ya bata wani. Banason in zama silar wata problem again... nidai kaga tafiyata..."yafada ya kada bayan rigarsshi,
"Dan Allah just marry her.. Kawai nasan I have made a mistakes and nemesis is catching up with me. Dan Allah ka kula daita. I love my children so. Much... I don't know abinda yasa Allah ya jarabceni da son yarana da yawa haka, Ashe Don ya hukunta nine..."yafada cikin hawaye, safwan kauda Kai gefe guda yayi ya tabe baki.

A gurguje dai bayan wata biyu aka daura auren Safwan da afra, ko kadan afra ta hana sick father dinta breathing space, kullum sai tace zata kashe kanta if baayi bikin da wuri ba, kawai she wants to be in the arm of Safwan, ko kadan vabu zancen tausayin situation din mahaifin ta balle ta raga mashi, irin yanda ta nace yasa akayi bikin babu wasting of time, ko kadan babu abinda ya taba shiga tsakanin su har akayi bikinsu. Dukda Mai saa was sad to the extreme bai hana kashe Millions of naira wajen sayawa afra kaya ba, irin kayan da aka zuba mata da wuya a samesu a yaran Nigeria ko da kuwa na yan sarki ne. Afra itace first daughter daya aurar, Don haka mutae kaman kirashi wajen bikinsu, daman yan biyu ne first daughter dinshi sai elder brothers dinsu guda biyu dake abroad suna karatu, shima Adam yana rubuta weac dinshi zai bisu abroad.

Sadwan na shiga part din afra baki ya bude Don duk yawonshi he has never seen anything like that.
Chapter 127 · 0% Book details