← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 162

Sashe 149

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

spoon, budewa tayi kamshin pepper soup din ya bugi hanshinshi, Dan murmushi ya saki tare dacewa "it scent nice... Ashe kin iya girki... "Dan baki ta turo tare dacewa "ba Kai bane baka yarda muyi'... " "ai banason ki wahalal da kanki... Tunda Allah yasa ina dashi... Ranar da ban dashi kuma sai kiyi ko ba haka ba?.." "Hakane... "ta amsa mashi sannan ta sake cewa "baby dan Allah what happened?.." "pls don't ask me... Banason yin maganar... "yafada kanshi kasa, zata bude baki ta sake magana aka bude kofar falon,afra ce ta shigo tana tafiya kaman batason taka kasa, tunda ya bar gidan bai k'ara saka a ido ba sai yau, tayi kal sosai sai rike gaban jallabiyar dake jikinta take, the other side taje ta zauna tana b'ata face, kafa daya ta dora kan daya ita kuma Nana ta maida marfin food warmer din ta rufe tare da ajiyewa gefe guda, cikin isa da takama ta gaidashi ya amsa kaman baison magana, "pls feed me... "yafadawa Nana, babu musu ta dauko ta bude, da sauri afra ta rufe bakinta ta tashi da gudu ta kama hanyar bed room dinshi, kallon juna Nana da safwan sukayi safwan ya Mike ahankali yabi bayanta, kanta kan sink sai amai take, bayanta ta dinga shafawa har ta gama sannan ta daga Kai sharkaf da hawaye tana kuka "what's wrong with you..."ya tambayeta yana kallon face dinta but he could not read her mind, cikin nishi tace "ban sani ba... "tafad'a tana kuka, in da kaman last week ya ganta haka zai durkusa ya godewa Allah yace she's pregnant ne saboda yanda ta sauya amma tunda he knows the truth about himself yasan it's not possible anymore, kawai she's having fever yayi tunani because he never thought she's sleeping most of night in hes securities bedroom, "kije hospital mana.. You look pale... "ya fad'a yana dafa goshinta, tana nishi tace. "kamshin wannan naman ne danaji... Shi ya tadamin zuciya.. Sannan this days da fever nake kwana... "tafada cikin shagwaba da farin ciki hankalin safwan zai dawo kanta, "am sorry baby... So sorry... Just try and see the doctor.. Ko na kirashi yazo?.. "ya tambayeta, "OK... "tafada kaman numfashinta zai tsinke, tafiya tayi daya biyu ta koma ta zauna bakin gado tana cewa "I can't walk.. Wallahi I feel weak... "tafad'a mashi "then ki kwanta ki huta... AI wannan kakarin amai da kikayi yasa kika gaji... Go and rest.. Zan koma falo inci abinci..."babu musu ta kwanta ya ja mata blanket ta fice, inda lokacin da yake da third eye ne da ya gano abinda ke faruwa amma yanzu nothing, hakan vai wani dameshi ba because he's tired of the whole thing called cultism, falo ya koma Nana ta tambayeshi abinda ya sameta ya fad'a mata, nan take jikinta yayi sanyi because tana tunanin kilan she's pregnant, kawai wani irin kishi Taji from nowhere but one thing about her is she's good in pretending, kaman babu abinda ke damunta tayi feeding dinshi yaci kadan ta dauko mashi fruit yasha ya kwanta tare da dora kanshi kan kafarta, baraka MA ta shigo suka dinga labari da Nana while shi yana kwance idanuwanshi lumshe amma ba bacci yake ba, kawai he's thinking yanda zai fad'a masu shi bai Haihuwa su tafi, tunawa yayi da rashin Nana da kuma yanda life will be without her, but he had been so selfish he don't want to be anymore, kawai he will ket her go taje ta samu miji tayi aure ta haihu, Dan bude ido yayi ya kalleta ta Dan kalleshi ta cigaba da magana tana shafa kanshi, baraka kam ko a jikinta, in da zaa auna safwan a jinin ta bai da wani big position a zuciyar ta, ita kawai tana ibada da kuma bin umarnin Iyaye that's all and nothing more, safwan daya lumshe ido Sam ya mance da batun afra balle ya kira mata Dr, kawai all he remember IE he's own situation. Karfe shida aka shigo da lunch as safwan ya bukata yana kwance inda yake babu abinda ke tadashi sai sallah, dayayi sai ya koma ya kwanta, ana kawo abinci ya tuna da zancen kiran Dr, da sauri ya kira Dr. Suna zaune kan dining wajen karfe bakwai Dr yazo, babu afra cikinsu tana kwance har lokacin, tare suka shiga da Dr ya dubata yana tambayar ta abubuwan dake damunta ita kuma tana fad'a mashi kaman b'ata son magana, bayan ya gama ya kalli safwan tare dacewa "sir I think amarya tana da ciki.. Dukda it's not official tana dauke da signs and symptoms na masu ciki..."Dr yafada mashi, shuru safwan yayi ya rike waist dinshi, kawai yana tunanin inda kafin suje meeting aka fad'a mashi wannan maganar har kyauta sai yayi nashi amma Sam yanzu ba haka bane, "pls check her and stop making assumptions... Dr don't make assumptions... " "sir ina amfani da symptoms din ne... "bai karasa ba ya daga mashi hannu yace "kar kayi amfani da symptoms... I want facts... " "OK sir..zan dauki jininta yanzu... Zan auna....i will call you... "yafada yana bude briefcase dinshi, safwan ba tsaye ya dauki jininta ya fita, begging dinta yayi ta fito taci abinc tace b'ata iyawa, haka ya fita ya kyaleta, fita yayi ya Kama hanyar part din inna yana kallon yanayin gidanshi, kawai he's imaganinig yanzu in ya mutu bashi da magaji. He regrets making money, he will do anything to be poor and have dozens of children, tunawa yayi da ranar da rabia ta kirashi tace she's pregnant, kawai he wish he can bring back hands of time, he wish zai iya daga murya da karfi y fadawa duk wani Mai shan wahala out there not to do bad things for money, zai fadawa mace ko namiji suyi managing kansu yanda suke kar su Kai kansu inda Allah bai kaisu ba, kar Wanda ya nemi kudi by fire by force, he wish yana iya fadawa duniya abinda ya faru a rayuwarshi, da wannan tunanin ya isa wajen inna, zama yayi asiya tayi mashi ya jiki ya amsa mata, nan take fad'a mashi wani yace zai turo, tambayar waye yayi nan ta fad'a mashi komai about him, he decided in Mai kudi ne sai yayi bincike Mai karfi sosai kafin ya aura mashi kanwar Amma luckily sai asiya ta fad'a mashi maaikacin makarantar boko ne, he was so happy about it har inna tayi mamaki "Allah yayi ma aikinshi albarka... "ya fad'a feeling inama shine. Haka suka dinga hira har wajen karfe tara ya koma part dinshi.dr ne ya kirashi wayar na falo bai daga ba. Wace gari bayan yaga wannan calls din ya kira doctor Don yaji why all the calls, "congratulations... Your wife is few weeks pregnant... "shine abinda yaji Dr yafada mashi, blowing kunnenshi yayi ya daga wayar yaga confrim da Dr yake magana sai kuma ya maida wayar kunnenshi yaji yana cewa "yanzu it's with prove not assumptions... "Dr yafada cikin murna saboda yasan all he's wives suna zuwa auna lafiyarsu so he expected this to be a good news amna sai wayar ya fadi daga hannun safwan, wani irin ihu ya saki tare da jin duniyarshi coming to an end.
Chapter 149 · 0% Book details