← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 162

Sashe 79

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna kam Yanzu abun nema ya samu, she don't complain anymore, ko safwan da bai zuwa gaidata bai dameta ba, kullum cikin Chanza new dress take, Mai aiki ta dafa ta kawo taci ta bi lafiyar gado without thinking other wise, asiya ma Yanzu ta daina complaining, bawai ta daina Jin wannan tsoron ba  no kawai dai Don ya yarda da bai da yayanta yace Sannan tunda ta zauna gidan bata ga wani Abu da yakeyiMara kyau ba, so she's a little bit at home, Yanzu ta saki ranta Tana Jin dadin rayuwa, abinda da Mai kyauwun jiki tuni jikinta ya fara sauyawa saboda new way of life.

Nana kam koda tazo wannan weekend ta like ta nace Wai zasuyi text Don haka dole a Barta ta zauna hostel for the weekends har su gama exam. Mahaifiyar ta rufe Ido tayi tace bata yarda ba. Kuka ta dingayi sosai har dad dinta ya shiga maganar,  yanda take kuka yasa dad dinta yiwa  mahaifiyar ta magana kan a Bari ta zauna hostel har tayi exams, goshi mahaifiyar ta dafa Tana cewa
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...Yanzu barinta zakayi ta zauna a hostel har nan sa kusa sati 6?.." Tafada tana  kokarin fashewa da kuka,
"Makam Dan Allah kar Kayi haka...kawai ya dinga dawowa gida,,,bai yuwa mu bar nana a school bamu San halin da take ciki ba..." Tafada cikin tsananin tashin hankali saboda hukuncin da mijinta ya yanke, tasan the world is a dangerous place, mahaifiyar nana Tana daga cikin iyaye that suke zaune cikin gida amma sun San abinda ke faruwa waje sabida wayoyin hannunsu, tasan yanda yanmata ke lalacewa a sanadaiyar karatu ko kawayen banza, shiyasa in the first place bata so nana ta zauna a hostel ba amma ta like har mahaifin ta ya amince now kuma tanason ta Daina zuwa gida har sai da ta gama jarabawa,
"Ai zamu iya zuwa ganinta duk sanda kika bukata..." Mahaifin ta yafada cikin calm voice kasancewan babu ruwanshi he's a gentleman that always wants to give he's family the best,
"Amma malam in munje minti nawa zamuyi?.. Nidai Wallahi aa...kawai ya dinga zuwa gjda duk weekend..." Ta fada atakaice, babu abinda ke tashi sai kukan nana, kawai she's seeing wannan kudin da big mama tayi mata magana, she wants that luxury life, she's ready to do anything for the luxury,
"Wai mama baki yarda Dani ba?.. Me kike tunanin zanyi?.. Wallahi karatu nakeson in maida hankalina inyi...inason results Dina ya fi na yaya kyau..." Tafada kaman da gaske,
"Dalla rufemin baki..ke daman Kin dauki gidan nan kaman kurkuku...ni Kaina ba damuwa kukayi Dani ba...nana yanmata da daman wayanda suka San ciwon kansu basu yarda su zauna inda babu mahaifiyar su na kwana daya...amma ke kirikiri kike nunamin bakisona...kirikiri kike guduna...kike nunamin baki kaunar zama dani..nana me nayi maki?.." Ta fada Tana fashewa da kuka saboda zafin da take ji cikin zuciyar ta,
"Nana me nayi maki?..why did you hate staying with me..." Tafada cikin matsanacin kuka,
"Haba meye haka?.. Sai ki kama kuka kaman wata karamar yarinya?.." Mahaifin nana ta fada mata Tana kallon yanda take zubar hawaye,
"Wallahi malam bazaka gane bane..bazaka gane yanda nake ji cikin zuciya ta ba...nana is my flesh and blood...daga jikina ta fito...Ina bakin cikin da bata kaunar zama inuwa daya Dani....I know she don't like me..,yar gidan safiya data samu admission a bauchi cewa tayi bata zuwa...amma ga nana just in same town bata son zuwa ganina during weekend...Wallahi malam da takaici..." Tafada Tana kuka sosai, nana kallonta tayi da innocent face dinta Tana tunanin
"Ki gama kukanki ki barni in zauna hostel..,kukan ki bai hananinkomai...." Ta fada cikin ranta, duk kukan da mahaifiyar ta takeyi baisa tayi step back ba, duk Wanda Allah ya yankawa kazar wahala sai ya tsigeta tas,
"Wallahi mama karatu zanyi....I want to have first class...I want you to be proud..." Tafada cikin kuka, mahaifin nana ya rasa ya zaiyi ganin matarshi na kuka
"Kinsan wannan kukan da kuke tamkar kina tsine mata né...ba'a son hawayen uwa kan da..ajiyan zuciyarki kawai yana iya bata mata rayuwa balle kuka...ki kwantar da hankalinki...duk uwa Tana kaunar yarta so I know you mean good...but ta zauna a hostel din....in munga results dinta baiyi ba sai mu maidata gjda complete..." Inji mahaifin ta, kallon nana yayi yace
"Kindai ji Abunda na fada maki...Wallahi na samu labarin kina misbehaving Wallahi kin gama karatun gaba daya...aure zaayi maki...Don haka the ball is in your cut...." Yafada atakaice, maman nana ba haka taso ba, ita kawai taso kar a Barta ta dinga weekend hostel tayi a gida, amma tunda mijinta yayi magana ta Mike without saying another word, har lokacin she's still crying her heart hurts like crazy, compound ta koma ta zauna tayi tagumi, nana fitowa tayi daga dakin abbanta face dinta kaman ba itace take kuka few minutes back ba, she looks so happy,
"Allah na gani Ina kokari na...Allah ka kalli zuciya ta...am trying..." Mahaifiyar ta tafada da karfi,, da sauri nana ta shige daki Tana girgiza chest dinta in ko a jikina, daman wasu yaran haka suke, suna iya nuna maka they're loyal amma a bayan idonka Allah kadai yasan abinda sukeyi, wasu kuma har gaban naka babu ruwan su they misbehave anyhow, they don't care what a mother feels when she's hurt, duk Dan da bai farantawa iyaye will never find happiness, ko da sun samu happiness din bai taba lasting, amma in har kika farantawa iyayenka komin kankantar abu zaiyi maka albarka, so children be wise and be obedient, wata rana sai labari, at time ki bakayi aureba da akwai mutuwa so don't take your mothers as enemies, they're the only person that will love you from the buttom of their hearts.

Fatima the more days na shiga kwana kin cikin the more laulayi da karuwa, Yanzu fever na yawan damunta sosai amma bata fadawa kowa, ahaka zata kwanta ya rufe kanta har Allah yasa ta samu sauki, sai ramewa take sabida zazzabin dare, yau bayan kanan habib sunyi Tuwo suka kawo daki, Fatima dake zaune kusa da mamanmu dake Jan jasbaha tayi saurin mikewa tayi waje da gudu, ko compound bata Kai ba ta saki amai, mikewa mamanmu tayi tabi bayanta Tana cewa
"Wannan aman yayi yawa...kodai a kaiki asibiti..." Tafada Tana shafa bayanta, da sauri Fatima ta girgiza Kai saboda tsoron magani da allura, sai da tayi aman Mai isanta Sannan ta Mike Tana nishi, gwoggo kallonta tayi zatayi magana Sai kuma tayi shuru, daki suka koma mamanmu ta debo mata ruwa Don Tasha ta girgiza mata Kai
"Bakina babu dadi..." Tafada kaman zatayi kuka, dawowa mamanmu tayi ta zauna kusa daita tare da dafa goshi ta taji da zafi sosai,
"Kodai muje asibiti..." Mamanmu ta sake fada mata, da sauri tace
"Aa...banso..." Tafada tears na taruwa idonta, kawai bata Jin dadin rayuwarta, wani Abu ke damunta Wanda takeji kaman ta rabu da wannan abun, ta rasa abinda ke mata dadi.
"Kince bakiso tunda baki da lafiya...kawai ki shirya...sai kuje kudawo..." Mamanmu tafada mata atakaice, ahankali Fatima ta Mike ta fita daga dakin, daya daga cikin sisters din habib mamanmu ta Kira Ta fada mata ta shirya ta raka Fatima hospital, ko kadan batasan she's pregnant ba, bayan kaman minti biyar Fatima ta fito da hijab sai tafiya take kaman zata fadi kasa, itama sister habib ta shirya suka fito Don fadawa gwaggwo,
"Ina zaku!.." Ta tambayesu, nan suka fada mata,
"Ku koma ciki...." Gwoggo ta umarcesu atakaice, cikin farin ciki Fatima ta koma ciki mikewa tayi ta dauki sandarta ta shiga dakin mamanmu Tana cewa
"Wai ke Yanzu birnine ya shigeki da daga samun cikin Fatima zaa fara zarya asibiti?.." Gwaggwo ta fada mata, idanuwa Mamanmu ta zaro hawaye na taruwa tace
"Gwaggwo bam gane ba...waye Mai ciki?.." Ta fada sounding so surprised, goshi gwaggwo ta dafa Sannan tace
"Yanzu kaman ke baki gane Mai laulayi?... Allah ya sauwake maki..." Tafada atakaice tare da Barin dakin, ahankali mamanmu ta dafa chest dinta tana cewa
"Ikon Allah..." Tafada idanuwanta waje daya,
"Fatima ciki gareta?.." Ta tambayi kanta da karfi,
"Way yo Allah na modibbo..." Ta rushe da kuka da karfi,
"Modibbo..." Ta sake fada while crying out loud, kuka ta dingayi sosai kaman Yanzu habib ya samu matsala, daman ta saba kukan time to time Don haka babu Wanda ya rarrasheta, sai da tayi kukan ya isheta Sannan ya Mike ta shiga wajen Fatima dake kwance lullube da daya daga cikin zaninta, bakin gado ta zauna ita kuma Fatima tayi kokarin zama,
"Kwanta abinki..." Mamanmu ta fada mata, komawa tayi ta kwanta Cikin kasala,
"Me kike son cin?.." Ta tambayeta cikin kulawa,
"Ba komai..." Ta amsa mata ahankali, mamanmu kura mata Ido tayi Tana mamakin wannan abun, sai Yanzu ya gane in Rabo ya rantse nobody should try and stand in the way.
"Dan Allah ki fadi Abinda kikeso, daga yau kome kikeso ki fadamin kinji kou..."
"Tou mamanmu..." Fatima ta amsa mata,
"Yanzu fadamin Abunda kikeso.."
"Bakina babu dadi...ban iya cin komai,.." Tafada cikin sanyinmurya,
"Tou Bari a sayo maki kaza ayi maki ferfesu Mai yaji,,,zakiji dadin bakinki..." Mamanmu ta fada Tana mikewa, Fatima dai bata ce komai ba, she wonders why mamanmu take mata haka Yanzu alhalin itace kullum sai tayi forcing dinta taci abinci amma yau kuma ta dawo petting  dinta,
Chapter 79 · 0% Book details