← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 162

Sashe 14

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai adaidaita shiga erea din duk sukayi shuru suna kallon mutane da dama suke zaune a Kofar gate dake nesa dasu, Mai adaidaitar na zuwa kusa da gate din yayi parking, "Ya akayi ka tsaya?.." Sufwan ya tambayeshi, "Ga gate din estate din chan?.." Mai adaidaita ya fada yana nuna gate dake cike da mutane, basu Kara cewa komai ba sufwan ya saka hannu a aljihunshi ya fiddo dubu daya ya bashi tare da tsayawa yana jiran change, ganin Mai adaidaita bai Kara kallon inda yake ba yasa sufwan cewa "Malam bani chanzi mana.." Kallon shi Mai adaidaita yayi from head to toe Sannan yace "Duk wannan uban in zan Baku chanzi?.. Lallai ka cika son banza..." Bai karasa ba sufwan yace "Haba malam...Yanzu nan cikin garin Kano zaka daukemu 1k?.. Gaskiya kayi tsada dayawa..." Sufwan ya fada cikn bacin rai, usman da habib basu ko kallon inda sufwan da Mai adaidaita suke drama ba saboda hankalinsu na kan mutanen da cike da bakin gate din, their wondering abinda mutanen suke nan zaune, da ganinsu you know they're beggars, ajiyan zuciya habib ya saki yana takawa ahankali, sufwan né ya taka zuwa kusa da usman da habib da suka nufi gate, knock sukayi Mai gadi ya Dan bude Dan karamin wuri dake bakin gate din ya kallesu tare dacewa "Wa kuke nema?.." Ya tambayesu, "Alhaji muke nema..." Sufwan ya amsa mashi "Yasan da zuwan ku?.." Mai gadi ya sake tambayan su looking at them through the hole, "Eh ya sani..." Usman ya amsa mash, maigadin bai Kara cewa komai ba ya bude gate suka shigo, dukkan su feel so breathtaking saboda yanayin gidajen dake cikin wannan wurin, gidajen sunfi goma kala daya, fadin yanda tsarin gidan yake is a waste of time, amma ko wucewa kayi ta wajen gidan kasan gidan babban mutum ne, Don ko makaho ya shafa zai sani, gefe daya suka tsaya suna kalle2, dukkan su are so speechless by the ta e of their heart beat, kallon juna sukayi amma basu ce komai ba, Mai gadi maida gate yayi ya kulle Sannan ya kallesu yace "Ku jira nan..." Yafada masu Sannan ya Kama hanyar daya daga cikn gidajen, yana barin wajen habib ya dafa chest dinshi yace "Am scared..." Yafada yana nishi kaman anyi asthmatic patient "Me too..." Usman da sufwan suka fada atare, "This house is so quiet.."Sufwan yafada, "Nidai am having a very weird feeling..." Habib ya fada yana juye juye, daya daga cin bangaren gidan aka bude wata kofa wasu sexy girls guda biyu suka fito sanye da gown blue sai kansu dauke da rolling din pink vail, da ganinsu kaga twiins, ajiyan zuciya sufwan ya saki yana cewa "At least da akwai wasu mutane gidan...Yanzu hankali na ya kwanta..." Yafada sounding calm, yanmatan takawa sukayi zuwa inda motocin gidan ke jere suka bude daya suka shiga ko inda su sufwan suke basu kalla ba, suna zuwa wajen gate Mai tuki ta fara horning da karfi, da sauri sufwan yaje bakin gate ya bude gate, yarinyar da take tuki bata wuce 19 years ba ta kalleshi from head to toe Sannan ta fice while maigadin ya taho da sauri, "Nagode.." Maigadi ya fadawa sufwan dake kokarin maida gate ya rufe, "Yace ku shigo ciki..." Maigadi Yafada masu, sakin gate din sufwan yayi Sannan ya taka zuwa wajensu habib suka fara takawa zuwa par din da Maigadi ya fito, "Pls mu nutsu Dan Allah...kar wannan tsoron kudi n muyiwa kanmu yawa.." Sufwan yafada cikin shawara, . Shoes dake kafar suka cire Sannan suka hau kan staid a zai sadasu da hanyar falo, jiki na kyarma sufwan dake gaba yay sallama, cikin natsuwa aka amsa mashi, ahankali suka shige aljannar duniya da tunda suke basu Tana ganin ba balle shiga, wani irin iskar ac ya bugesu duk suka lumshe idanuwa, da sauri suka zube kasa suna gaida shi, amsawa yaya wearing a very friendly smile, "Pls ku zauna...feel at home..." Yafada masu kaman wasu mate dinshi yana kallon yanda duk suke durkushe kasa, still suna inda suke basu zauna ba "Cewa nayi ku zauna .." Ya sake fada masu Sannan suka zauna manne da jikin juna kaman wasu chewing gum, idanuwa suka lumshe suna Jin yanda sanyin ac ke ratsar system dinsu, "Dan Allah ku saki jikinku..." Ya fada masu yana dariya saboda yanda sukayi gumming junansu, ahankali suka Dan matsa daga jikin junansu "Barkan ku da zuwa..." Yafada yana daukan wani Abu dake kusa dashi, duk daga Kai sukayi suna kallon shi, kowannensu sai da yaji tsigan jikinshi na tashi, sufwan kam babu abinda yake mamaki sai yanda he's having the same feeling for the second time shima habib da sufwan same thing sukeji, basusan suna Jin exactly yanda dabba keji idan yaga mahauci ba, duk Dan Adam daya taba cin naman mutum one look you will have a strange. my friends when ever you look at someone and feel strange there's something wrong with the person, so be careful and be warned, bayan kaman minti daya aka shigo da tray din abinci Mai raI da lafiya aka jera a dining, "Ku tashi kuci abinci..." Ya umarce su, duk daga Kai sukayi suka sake kalli junansu suka sadda Kai kasa, dariya alhaji yayi Sannan yace "Aa wannan Abu haka kaman ba maza ba?... Kar dai kuyi disappointing Dina...Don kallon Maza nayi maku shiyasa nakeson Baku chance...in kuma ba mazan bane the tou in hakura..." Bai karasa ba suka Mike da sauri kaman wasu yara, dariya ya zauna yana yi cikin ranshi yana in tunanin if This guys are capable of what he have in mind for them, zama sukayi zuciyar su na dar dar suka fara zuba Abincin da tunda suke basu taba ganin abinci Mai kyau a face kaman shi ba Sannan kamshinta ma is making them salivating, "Ku saki jiki kuci ku koshi..." Alhaji idris Yafada masu, daya daga cikin masu aiki ta dauko plate ta zuba masu white rice sai ta bi da miyan dayasha Nama followed by coslow sai a wata karamar bowl ta zubawa kowannensu chicken pepper sauce, cup ya dauko ta zubawa kowannensu juice Sannan ta ajiye robar ruwa Mai sanyi da cup gefe, fita tayi ya bar falon shima alhaji idris ya mike yana cewa "Bari in watsa ruwa...and remember to feel at home Don Yanzu mun zama daya..." Yafada yana Kama hanyar daya daga cikin kofofin dake nan falon, yana barin dakin suka fara waigawa Sannan habib yace "Ni Wallahi kamshin Abincin nan ya cika min ciki..." Yafada in form of whisper, "Amma mutane suna hutawa mu kuma we're struggling for survival.." Sufwan yafada yana kallon pepper soup dake gabanshi yana tururi, "Ai Wallahi ko daga yau bazan Kara samun irin wannan Abincin ba sai na cinye tas..." Inji usman dake daukan spoon, "Yanzu hankalina ya fara kwantawa compared to before..." Inji habib "Nima tunda na fara ganin mutane a gidan naji saurki...sai dai the feeling..." Sufwan bai karasa ba usman ya Dora mashi hannu a baki yana cewa "He might be listening...kunsan irin wannan gidan have lots of securities..kilan ma da akwai camera kan dining din nan bamu sani ba..." Usman ya fada cikin rada, da sauri suka fara kallon dining dake salki "You may be right..." Habib ya fada. Sannan ya Kara da cewa "Eat in silence..." Yafada yana daukan spoon din, coslow dake saman Abincin ya maida gefe yana cewa " am not going to eat this..." Yafada yana dariya kasa kasa, sufwan kallon shi yay yace "Wallahi dukda ban taba ci ba ban barin komai...ai da koyo ake zama perfect..." Yafada yana deban rice da coslow, yana kaiwa baki ya tauna yana sauraron taste din, idanuwa ya lumshe yana cewa "Kai Alhamdulillah...dadi yayi Wallahi..." Yafada cikin santi, dariya sukayi duk Wanda ya Kai Abincin nan baki sai ya saki santi Jin abinda bai taba ji ba, ahaka suka cinye Abincin tas,kowannensu jingina yayi da kujeran dining yana lumshe idanuwa kaman zasuyi bacci, ya sanyi ac dake ratsa su. Alhaji idris na shiga dakinshi ya saki dariya, dariya Wanda bansan meaning dinshi ba, bakin gado ya zauna yana lumshe idanuwa yana tunani, he's thoughts are so hard to read, sai da ya gama tunanin da yake ya Mike ya shiga bathroom yayi wanka ya fito daure da towel, kwantawa yayi kan gado ya cigaba da tunani, "There's nothing to regret about it...no regrets no going backwards..." Yafada yana Shafa zoben dake hannunshi, kwantawa yayi still saying "No regrets no going backwards..." Ya sake chanting kaman yanda sukeyi a chan cult. Sai da ya tabbatar sun cinye sun huta ya Mike ya saka jallabiya ya fito falo, tun daga nesa yaga duk sun Dora Kai a table din dining da alaman zasuyi bacci ko sun fara bacci, sallama yayi in a calm manner sukayi saurin daga Kai, idanuwansu da suka Chanza kala ya kalla ya Dan saki dariya yace "Da alaman bacci zakuyi..." Mikewa sukayi tsaye sufwan yace "No sir..." Bai karasa ba alhaji yace "No you're free in zakuyi bacci da akwai wurin da za'a kaiku ku huta Ai..." "Aa sir...we're alright..." Habib ya fada mashi cikn biyayya, zama alhaji yayi suma suka dawo falon suka zauna kasar dakin a gabanshi, "Alhaji mungode...Allah ya biyaka..." Usman Yafada mashi, hannu alhaji ya daga mashi Sannan yace "Haba Banda godiya pls...now inason ku bani tarihin rayuwar ku..." Ya tambaye su, sufwan né ya fara da bashi labarin rayuwar shi bai boye mashi komai ba, ahankali alhaji ya girgiza Kai cikin ban tausayi Sannan ya juya ga habib shima habib ya bashi nashi tarihin in details shima he sai da alhaji ya tausaya mashi Sannan ya koma ga usman Shima ya bada nashi in details sai da ya Kai aya Sannan alhaji yace "Kungani haka rayuwar take...babu Mai taimakonka sai ka tashi ka taimaki kanka...ko ni nan inda ban taimaki Kaina ba da kilan Ina cikin masu yawon maula...mutane Yanzu basu taimakon kowa sai kansu...one have to be strong and strong heartened before you can make it...ni Yanzu tambayan da zanyi maku shine how ready are you to make it?.." Ya tambayesu idanuwanshi kansu..." "Very ready..." Usman Yafada Sannan sufwan da habib suka ce "We're ready to make it sir..." Cikin Jin dadi ya kada Kai
Chapter 14 · 0% Book details