← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 162

Sashe 135

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Karfe takwas daidai yana kofar gidan su Nana, daman one thing about safwan is he's not the type of person that give up, yana da total determination, duk inda ya sa gaba bai maidawa baya. Aikawa yayi wai ana sallama da Mai gidan, bayan kaman minti biyar malam isa ya fito, yana ganin safwan ya hada sama da kasa yana cewa
""you again... Nace ka tafi... What do you want... "yafada sounding so tensed amma in a low voice kar aji abinda yake cewa, safwan dake sanye da Jean da riga ya sadda kai kasa yana ceaa
"kayi hakuri... Dan Allah ka bani izinin in bata hakuri da kaina.. Pls.."
"aa.. Ni zan bata hakuri... Zata yafe maka... Amma baka shigar min gida... "malam isa ya fada mashi
"nidai ka yafemin. Nasan you're still mad ta me.. Kuma am not a son to you.. But pls let me speak to her... "yafada voice dinshi narawa,
:"wallahi zan sa ayi maka duka.. Leave now... "ya daka. Mashi tsawa, aikam sai safwan yayi kneeling nan kasa yana cewa
"I won't go until you let me see her... "yafada yana nan durkushe, dukda lungu ne baa rasa mutane masu wucewa kuma da akwai nepa Don haka the area is illuminated in their own way, goshi malam isa ya dafa not knowing what to do with safwan, he's indeed a pain in the ass
"hope you're not expecting in bar ka ka shiga gidana da wanna daren ba..."
"AI ba wani abu zanyi ba... Kawai hakuri zan bata da mahaifiyar ta... "yafada cikin respect, ajiyan zuciya malam isa ya saki sannan yace
"Kawai ka tafi... Zan kiraka..."da sauri safwan yace.
"baka da number ta... Kawai ka fadamin ranar da zan dawo... "yafada while still kneeling,
"tashi... "malam isa ya umarceshi, da sauri ya Mike tsaye,
"ka tafi gobe ka dawo..."
Karfe nawa... "safwan ya tambayeshi,
"da asr... "ya fad'a mashi,
"nagode... Nagode... "yafada ya juya sai sauri yake, malam isa tsayawa yayi yakurawa bayanshi ido
"Anya kanshi daya?.. Kilan ma mahauci ne..."yafada cikin ranshi, cikon gida ya shiga ya kira mahaifiyar Nana dakinshi nan ya fad'a mata exactly what happened, shuru tayi for a moment sannan tace
"ai sai mu godewa Allah dayasa ya dawo Don neman yafiyarta... Don nasan da akwai mutane da dama da akayiwa haka ko sannu basu dawowa suyi masu balle su basu hakuri.. Dukda a zahirin magana Nana ita ta kai kanta... Itace da laifi.. Don haka babu komai.. In MA munce bazamu hakura ba babu abinda zai kara mana.. Aikin gama ya riga ya gama... Kawai mu dauka haka nata kaddara yake... " mahaifiyar ta ta amsa mashi cikin sanyimurya,
"ki kira Nana... "ya fad'a mata, mikewa tayi ta shiga dakin Nana dake kudundune cikin zanin gado ta kirata, mikewa tayi ta fito, dakin shi ta shiga ta zauna gefe guda.
"tsakanin ki da Allah kan abinda ya sameki wa kike ganin yana da laifi..a tunanin ki.. Wa kike ganin ya chanchanci ya hukunta? "ya tambayeta, kuka ta farayi tana cewa
"nice baba... "
"good... Kece da laifi.. Ko kasheki akayi ke kika kai kanki... Ke kika saida rayuwarki kan abun duniya... "kuka Nana ta farayi sosai Don tunda ta samu matsala vai taba maganar ba, bai taba zaunar daita kan wannan zancen ba sai yau, she wonders what gingers it, dayake mata such issues at this time, she's wondering wanene ya kira mahaifinta waje, ko kadan she never thought of safwan ne Don tana ganin he can't Stand before her father,
"yaron yazo gareni ya nemi yafiya.. Kuma kowanne irin zunubi ka aikata muddin ba shirka kayi ba Allah gafurun rahim ne...balle mu Dan Adam sannan ke da kika kai kanki... Zan kawoshi gareki... "ai bai k'arasa ba ta dinga ihu tana cewa ba sai ya zo ba.. Wallahi na yafe mashi.. Na yafe mashi duniya da lahira..kar yazo.. Basai ya zo ba... "tafad'a cikin matsanacin tashin hankali, duk idanuwanta waje kaman ana maganar ghost,
"ke rufa min baki.. Banason jin word daya daga gareki.. Tashi bani waje... "mahaifiyar ta tadaka mata tsawa, tana kuka ta Mike jikinta na rawa, she don't know me safwan yayiwa iyayenta da har zasu bashi daman shiga cikin gidan su. It hurt her so much but bata da choice, in a real sense tasan she's at fault amma ko kadan batason ganinshi. Safwan kam was so eager garin Allah ya waye Don ya ga Nana, she's a Young girl with the highest package he have ever seen, komai nata loaded.
Karfe uku da rabi ya iso area din yayi zaune cikin mota, yana kallo mahaifin ta ya wuce kan mashin daga wajen aiki, yasan kilan ya ganshi saboda he's car. Bai fita daga cikin mota ba sai four daidai. Yana zuwa yasa akayi mashi sallama gidan, sanye yake cikin shadda kaman mutumin kirki, baka taba ganinshi kace he have hands in any Evil things, he looks so decent and handsome. Malam musa mikewa yayi ya fito compound ya fadawa Nana ta shirya zai shigo, ji tayi gabanta na faduwa sosai, nobody will understand what she's feeling, ita kadai tasan irin azaban datasha hannunshi, da sauri ta dauko hijab ta saka ta zauna nan dakinta tana kuka tare rufe bakinta da hannunta. Daddaure face malam isa yayi ya fito waje tare dace mashi
"bisimilllah ..."jikin na rawa Safwan ya shiga gidan da sallama, mahaifiyar Nana dake gefe daya sanye da doguwar hijab ta amsa kanta kasa, Dan satan kallonshi tayi Don last time tashin hankali bai Bari ta ganshi sosai ba, she can't believe young boy kaman shi can be that wicked, ahankali ya durkusa har kasa yana cewa
"mamana... Dan Allah ki yafemin saboda kuka da bakinciki dana saki... Sharrin shaidan ne... Ba halina bane... Ki yafemin... "yafada trying not to cry, Maman Nana ji tayi hawaye ya taru a idanuwanta,
"Allah ya yafe mana gabaki daya ya rabamu da mummunar kaddara..."tafad'a cikin calmness, hannu biyu safwan ya hada waje daya ya farayi mata godiya, Nana dake daki rufe bakinta tayi gam while ta rike gaban rigarta, voice dinshi kawai dataji yasa gabanta ya fara motsi kaman he's trying to go in again, she's having a weird feeling,
"wai ina kike.. Come out now.. "dad dinta ya fad'a sounding angry, da sauri ta fito idanuwanta sharkaf da hawaye, hannunta biyu kan bakinta, juyawa safwan yayi gareta yayi kneeling on he's two knees yayi kokarin crawling zuwa gabanta aikam da ihu da gudu nana ta koma bayan mom dinta tare da boyewa tana rike waist din mahaifiyar ta, kuka safwan yafarayi yana cewa
"Nana kiyi hakuri...na dauki alkawari maganin duk ya macen da ta amshi kudi tabi namiji amma abinda nayi maki is deadly and wicked... Ki yafemin ki gafarta min... Ni ba kowa bane da zan dauki vengeance a hannuna... Nayi kuskure dana dauki hukunci a hannuna... "yafada voice dinshi na rawa saboda kuka,
"na yafe... Go.. "shine abinda Nana dake labe bayan mahaifiyar ta tafad'a mashi atakaice jikinta na rawa,
"nagode...Allah ya saka da alkhairi... One last thing...pls.. Zan tambayeki a gaban iyayen ki... Marry me..."wani irin kuka Nana ta farayi tana kara damke waist din mahaifiyar ta, cikin kuka ta fara cewa
"daman.. Nasan bai gama Dani ba...shiyasa ya biyoni... Baba.. Ka fad'a mashi ya tafi... "tafad'a kaman zata sike saboda kuka, safwan zai bude baki yayi magana malam isa yace
"tashi ka tafi... Tace ta yafe... " da sauri safwan ya juya gareshi yana cewa
"wallahi bani da wata manufa kanta... Nasan ni na cuceta.. Kuma ni na chanchanceta.."bai k'arasa ba malam isa yace
"shut up and leave... Nayi maka abinda ban taba tunanin zanyiwa Wanda ya zalunci yata ba.. Amma you want to cross your limit... Bar min gida this instant... "yafada cikin bacin rai, abinka da stubborn person duk ihun da malam isa keyi crawling yayi ya kama legs dinshi yana cewa
"wallahi inason Nana... "
"nace leave!!!! "malam musa ya daka mashi tsawa, ba Don ya tsorata ba amma yamike saboda respect, juyawa yayi ya kalli mahaifiyar Nana dake tsaye tana kuka yace
"pls ku taimaka min.."yafada yana fita daga gidan.

Thanks53💜💙💚💛🧡
Sirrin wasu gayun
💙💜💚💛🧡❤

®Zuwairat (ummumaryam)

5⃣3⃣
Chapter 135 · 0% Book details