← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 157

Sashe 99

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Tafiyar ma nisa take mata dan haka ta ɗan haɗa da gudu gudu har dai ta iso ɗakin na sa ta tura ƙofar tana fatan Allah ya sa ba mafarki tame ba da in ta buɗe ƙofar zata ga wayam.
  Cikin kwanciyar hankali yake baccin sa kamar bai da damuwa dan babu wanda zai gan sa a haka yayi tsammanin baccin dole da na wahala yake yi,kamar kar ta ɗauke idanun ta a kan sa sai ta shiga takowa tana nufo sa har ta iso gab kusa da shi ta zauna saman gadon kamar mai tsoro,a lokacin da ta zaunan ne su Dr Maher da Afzal suka shigo dan Hakim baya nan ya tafi rounding up na karatun sa baya gidan Baha kuwa tsabar bala'in da ta kwaso na mutanin da ke ta surutu marasa daɗin ji a wun liyafar nan ya sa suna shiga tayi ɗakin ta ta shige bayi dan son rage zafin abin dan haka bata da masaniyar wainar da ake toyawa.
Kallon Afzal Hajiya Madina tayi ta ce
"Ya aka yi ka sami waÉ—annan bayanai daga wun mai gadi"??sai ya ce
"Ammi bayan kun shigo ne na koma dan in gyara parking har zan tafi sai Luk ya kira ni akan in yi saurin shiryawa dan mu koma station a fara yin wasu aikin dan samo inda suka tafi sai na ce da shi kar ya damu yanzu zan fito sai yake kuma sanar da ni ai ya kuma samin kira daga airport akan a dawo a duba dan wani jirgin yayi landing babu jimawa toh amsar da na bashi ne ya sa mai gadin zuwa kusa da ni ya ce min _ranka ya daɗe ai kamar ina jin baƙin jamani sun iso gida_ sai na tambaye sa dan ban fahimce sa ba sai ya warware min abin da ya faru a kan idon sa na tambaye sa ya tabbata shi idon sa idon yaya ya ce da ni ƙwarai dan shi ma ya shigar masa da kayan sa ciki kuma tun da ya shigan bai fito ba toh shine na mai godiya na dawo ciki na nufi sashen yaya na duba na hango sa yana bacci shine nayi saurin zuwa sanar da ku"!!ajiyar zuciya suka sauke su biyun saumi Dr Maher ya ce
  "Allah ya maka albarka Afzal"ya amsa da
"Amin Abba"daga haka ya bashi umarni da ya kirawo chan jami'an tsaro ya sanar da su abin da ya faru sannan ya kirawo masa Baha dan yana gudun kar wani abin take ƙullawa alhalin an gan sa ya kuma ce da shi kafin ya yi kiraye kirayen ya fara kiran Prof ya sanar da shi..
  Hakan ya aiwatar ya bar ɗakin ya aiwatar da umarnin mahaifin nasa a nan shima Prof ya sanar da shi ai an ga Bilkisu shine ya dawo ciki ya sanar da su.murna suka yi sosai sai dai suna tunanin me ya faru da suka dawo suka nufi gidaje daban daban.  
  Ita kuwa Hajiya Madina har ta fara tunanin hala kunya ce ta sa suka zaɓi dawowa nan gida basu tafi chan gidan su ba again ƙila so suke a masu bikin auren su irin a ɗauki amarya a kai ta gidan mijin ta ɗin nan,sai wani sashe na zuciyar ta ya ce a'a fah kika sani ko wata matsalar ce dan in ba wata matsala ba ya za'a yi a yi ta kiran su su ƙi ɗaga waya dole akwai dalili.yin wannan tunanin ne ya sa ta maido da duban ta ga Zaid da ke kwance kallon sa take kamar an ce da ita kwace mata shi za'a yi.
  Kasa tayar da shi tayi har sai da Dr Maher ya taɓa shi sau biyu sai ya ɗan motsa kaɗan da niyar gyara kwanciyar sa sai dai bai ida juyawar ba yayi tozali da Ammin sa da ke bin sa da kallo sai ya ɗan rumtse idanun sa sannan ya buɗe,a hankali ya tashi daga kwancen da yake ya zauna duk suna kallon sa.
Jingina zai yi da kan gadon amma ta hana sa ta janyo sa kusa da ita tana faÉ—in
"Come to momma baby"rungumo sa tayi tana jin hawayen farinciki na bin kuncin ta,saurin gogewa tayi dan kar ya gani.
   Cikin ran sa tunani ya shiga yi anya Ammi ta san abin da ya aikatawa amanar da ta ba sa kuwa?toh in ma ta sanin me yasa bata yi reacting ba har take janyo sa jiki?ko dai Bilkisu bata sanar da su abin da ya faru bane?toh in haka ne ina ta tafi dan ya san da a ce sun haɗu tabbas ba tantama da Ammi zata yi spotting abin da ya faru kuma dole zata tambayi Bilkisu dan jin ƙarin bayani and if Bilkisu responds toh da ba haka zai ga Ammin ba toh me ya faru?..
  muryar ta ne ya katse mai tunanin da yake yi
"Zaid...me ya faru baku zo nan gidan ku ba instead kuka dawo gida nan me ya faru halan"??shiru yayi yana ingesting maganganun mahaifiyar ta sa and then he began to wonder Bilkisu bata tafi chan gidan bane dama nan ta zo ko chan gidan su ko ina Ammi ta gan ta.
  Ɗago kan sa yayi ya kalle ta sai ya ƙaƙalo murmushin dole dan he feel so pathetic for himself already in har Ammi ta gano gaskiya dukan sa ne kaɗai ba zata yi ba because Ammi is a no nonsense woman she won't spare him that he can assure

"Zaid talk to me"Dr ne ya zo kusa da ita ya dafa ta kafaÉ—a yana mata magana a hankali
"Darling allow him to refresh his memory kin san yanzu ya farka"É—ago kan ta tayi ta gyaÉ—a mai kai sai ta dawo da duban ta ga Zaid É—in
"Shikenan just rest for now tunda dare yayi but gobe inshaAllah first thing in the morning zaka min bayanin abin da ya faru uhmm"??saurin amsa mata yayi sai ta tashi ta ɗan durƙuso ta manna mai good night kiss a forehead ɗin sa ta miƙe
"Zan shiga chan gidan su Umman ku dan dubo Bilkisu just sleep calm har goben ka ji my boy"?amsa mata yayi da kai yana jin tausayin kan sa dan har ta tafi gidan nan ya san komai zata ji and she will come back and vent her anger on him ba zata tsaya sauraron dalilin sa ba shi wa zai fahimce sa ne wai..
  Shafo gefen fuskar sa tayi tana murmushi sai da ta tambaye sa ko ya ci abinci ya amsa mata da eh kafin su fita su bar sa.
  Suna fita kuwa bacci ya ƙaurace wa idanun sa sam ya rasa me ya shafi Bilkisu a daren jiya daga magana kawai sai ta ja mai tsatsauran layi tsakanin sa da ita yana matsayin mijin ta me ya taɓa ta ne shin a jiyan.
  Haka ya rinƙa tunani kala kala dan ya san muddin Ammin sa ta dawo da cikakkiyar labarin abin da ya ma Bilkisu sai ta kwance mai..

  Bayan barin su ɗakin bata tsaya komawa cikin nata ɗakin ba ta yi hanyar fita sai Dr ya dakatar da ita ya ce
"Baki fah canza kayan ki ba a haka zaki tafi gidan"?ɗan ɓata fuska tayi kafin ta ce
"Kai dai kam Dr akwai ka da damuwa me ya ma waÉ—annan kayan ana ta kai wa ke ta kaya"girgiza kai yayi ya ce
"Toh mu tafi"daga haka suka fita tare suka shiga cikin gidan su Bilkisu suna tattaunawa akan al'amarin da ya faru a yau É—in...
************
  Ƙarar wurgi da pillow ta ji sai ta buɗe idanun ta a hankali duk sun yi ja ja zir tsabar kuka da ɓacin rai a ce ita aka daka an hana ta kuka sannan ɗan hawayen da zata fitar ma ta ji sauƙi shima an hana ta wannan ai son kai ne shi Zaid ɗin ba'a san abin da ya mata bane da sun sani da ba zasu tasa ta gaba haka ba har Umma na yunƙurin sauke mata mari lallai da Umma ta mare ta da tsanar da zata ƙara yi wa yarinyar nan Allah kaɗai ya sani.
  Ƙwafa ta yi ta tashi ta bar ɗakin sai a nan Zainab matar Jamil ta sami damar zuwa kusa da ita ta janyo ta ta shiga rarrashin ta dan ciwon ɗiya mace na ɗiya mace ne Bilkisu aka wa rashin adalcin amma ita ce ke jin takaicin abin.
  Daga Bilal har Lukman babu wanda ya goyi bayan Zaid laifin sa suka gani dan ita ɗin ƴar uwar su ce kuma su suka san wahalar da ta sha duk a dalilin halin da ya shiga sama da sati biyu bata san inda kan ta yake ba duk saboda shi again an haɗa ta aure da shi ba wai dan suna son juna ba but ta haƙura ta zauna da shi ta yi jinyar sa har ya warke sannan a ce ga abin da zai saka mata da shi he is too selfish to their own thinking..
Chapter 99 · 0% Book details