← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 157

Sashe 80

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Tana nan kwancen ta ji ya turo ƙofar ɗakin dama akwai haske a ɗakin dan haka ya sami direct access na kallon ta,ƙare ma jikin ta kallo yayi sai ya ji wani abin na taso mai from nowhere sai ya haɗiye yawu haɗe da buɗe baki da nufin gaya mata abin da ya kawo sa amma sai me?kasa magana yayi dan kayan jikin ta have tempted and seduced him already.
  Tana kallon sa gaban ta na faɗi shi kuma ya ƙi cire idanun sa daga kan ta wani mugu mugun muguwar sha'awar junan su ne ya taso masu,strong desire ne ke ɗeban su but sun kasa aiwatar da komai sai idanun su da ke aikin aiken da sukewa junan su mai ɗauke da saƙonni daban daban masu girman gaske..

_*S,Ibraheem*_
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀*
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

  *25*
*_Conspicuous_*

Kamar wasa sai ga Dr Zaid ya shafe awowi sama da huɗu wanda yayi daidai da ƙarfe 1:30am na dare yana zaune yana kallon Bilkisu,idanun sa duk sun yi ja ja zir sun ƙanƙance dan bacci yake buƙata amma baya jin in yayi baccin nan zai wa kansa adalci duba da yadda ita ta tsaya ta dage a lokacin da shi bai da lafiyar ta kula da shi ta tabbatar da safety haɗe da security nasa bata bar sa ba toh me zai sa shi ya bar ta tana cikin halin nan ya je ya kwanta saboda selfishness bai jin zai iya wannan abin.
  Countless times without number yana jin hausawa na faɗin kalmar *_"IYA RUWA FIDDA KAI"_* amma bai san cikakkiyar ma'anar kalmar ba a hausance all he know shine yadda ake amfani da kalmar cikin magana dan dasawa mutum baƙa hakan ne ma ya saka sa gayawa Bilkisun a lokacin da ta nemi sanin dalilin zuwa da ita da zai yi yola dan yin outreach but apart from wannan bai san ma'ana gamsasshiya da za'a iya alaƙanta kalmar da ba..

  Ɗago kan sa yayi ya kalle ta tana bacci cikin doguwar rigar baccin ta da kaɗan ya rage ya kai mata ƙasa hular baccin ma duk ya fita daga kan ta gashi nan a gefen ta kamar dai kullum tayi twisting sumar kanta ne ta tura ciki babu robber band bare wani abin takura.
   Bayan ya gama ƙare mata kallon ne ya kai hannun sa cikin salon da ba zata ji ba bare ta tashi daga nannauyar baccin da take yi,warware mata suman yayi a hankali sannan ya shiga gyara mata cikin taka tsantsan dan kar ta farka ta kasa komawa baccin.
  Da ya gama gyara mata sumar sai ya cire hannun sa daga kan ta ya kawo ya haɗa da wanda ya riƙe hannun ta da shi ya maida idanun sa kan ta yana kallon ta shi kam bai taɓa jin tausayin mace har haka ba tun da yake a rayuwar sa yana iya cewa ko Bahajjatu dake ƙanwar sa har yake iƙirarin son da yake mata na daban ne toh har ita bai jin ya taɓa yi tausaya mata kamar yadda yake tausaya Bilkisu a halin yanzu,ya kasa tantance ɗaya abin da ke damin sa game da ita dan irin feelings da yake experiencing time to time ba tausayawa bane kawai dole akwai wani abin na daban wanda yake buƙatar ƙarin haske akai.
  Toh wai ma ya aka yi tun da chan baya bai taɓa jin irin wannan abin ba?da da suke tare a kullum da in tayi magana yayi sai dai tayi shiru kuma akan gaskiyar ta take maganar ko da kuwa yin maganar sa na nufin janyo mata babbar disappointment ne bata cigaba da magana sai dai ta yi shiru ko ma ta bar wurin highest in ya ɓata mata rai da yawa sai ta aika mai da mugun kallo ta yi tsaki tayi tafiyar ta but bai taɓa jin ɗigon tausayin ta ba sai yanzu,yanzun ma a yau a wannan halin da ya ganta.
  Dole wannan tausayin ba shi kaɗai bane akwai wani al'amari behind it ba natural bane..
  A karo na sau ba adaɗi ya kuma kallo ta tana baccin ta cikin kwanciyar hankali,mai da idanun sa yayi ga flower vase dake ɗakin sannan ya dawo da idanun sa gare ta sai kuma ya koma duniyar tunanin sa
  A halin da ake ciki yana ganin kamar muhimmancin ta a gare sa is more fragile than the flower vase,yana ji a jikin sa kamar akwai wani babbar al'amari that is yet to come his way sai dai kuma kamar akwai hindrance da zai yi forming babbr rift a tsakanin sa da ita..
  Jin faɗuwar gaba yayi ba tare da ya san dalilin hakan ba,kallon ta yayi sai ya ji faɗuwar gaban ya ƙaru ninkin yadda yake ji,shiru yayi yana son dawowa daidai sai dai abin ya ci tura dan the more thought of separation ya zo mai sai ya ji heart race nasa na ƙaruwa.
  Toh shin me ma yasa yake tunanin wataran zasu iya rabuwa alhalin gasu nan tare kuma in bai manta ba they are married so why is he thinking about separation?ko dai bai da lafiya ne bai sani ba?

  A wannan karon da ya kalle ta sai ya ji yana son kwanciya next to her maybe zai sami sauƙin raɗaɗin da yake ji a ran sa dan haka ba tare da wani doguwar tunani ba ya saki hannun ta ya tashi daga zaunen da yake ya dawo kan gadon ya kwanta a left side adjacent to her ya juyo fuskar sa daidai nata fuskar yana kallon ta.
  Akwai wani maganaɗisun da ke ingiza sa yin abubuwa da dama da bai gama yin shawara da zuciyar sa akan halascin su ba amma yana jin in bai yi abin ba toh kamar a takure zai kasance wannan ne dalilin sa ma na barin ɗakin sa ya shigo nata kenan ba tare da ya tsaya yayi doguwar tunanin abin da zai yi ba sannan yanzu da yake zaune ya tashi daga zaunen da yake ya dawo kan gadon ya kwanta next to he,kuma ikon Allah sai ya ji faɗuwar gaban da yake experiencing ya ragu kusan kashi talatin cikin ɗari,yana kallon nata ne yana tunanin zuci har bacci mai naiyin gaske ya ɗauke sa wanda bai san ba a ɗakin sa yake ba dan he feel very comfortable and free a inda yake sanadiyar samin lafiyayyiyar baccin da yayi kenan..

  _5:14am_
A daidai wannan lokacin ne ya juya da nufin gyara kwanciyar sa sai kuma ya dakata daga komawa baccin dan ya ji different scent ba kamar wanda ya saba ji ba in ya juya a ɗakin sa,a hankali ya shiga buɗe idanun sa har ya gama buɗe su duka sai a nan ya fara tuno abin da ya faru da shi a daren jiya,dafe goshin sa yayi yana mai lumshe idanun sa kusan mintoci kafin ya buɗe su ya juya ta ɗaya gefen sa sai ya ganta kwance lafiya ƙalau tana kwasar baccin ta juyawa yayi ya ɗauko remote ɗin air split na ɗakin ya rage yawan shi dan yana gudun wani abin da zai janyo mata ƙaruwar zazzaɓin da take ciki already.
  Tashi yayi daga kan gadon ya nufi hanyar fita daga ɗakin,ba sallah take ba bare ya tashe ta sai kawai yayi tafiyar sa zuwa ɗakin sa ya yi alwala ya zo yayi sallah..
  Wani baƙon lamarin da ya same sa shine yadda ya taƙarƙare ya rinƙa yi mata addu'ar samin lafuya haɗe da yi mata addu'ar tsari daga yin wani rashin lafiyar dan shi kaɗai ya san yadda ya ji a jiya da ta shiga halin nan sam baya so ya kuma witnessing..
  Sai da haske ya fara haska ɗakin nasa sannan ya tashi daga saman sallayar nasa ya dawo kan gadon sa ya kwanta daga haka ne wani session ma baccin ya kuma yin awon gaba da shi kuma a cikin wannan baccin nasa ne ya rinƙa mafarke mafarke marasa daɗi dan kaf abin da ya faru da shi ne a dajin nan ya shiga dawo mai sai ya shiga karkarwa yana haɗe jikin sa wu ɗaya at the same time yana karantar add'uar tsari da kariya bai farkan ba haka bai daina yin add'uar ba har sai da hotunan mummunar ranar takau daga baccin sa sannan ya cigaba da yin baccin duk ya gama haɗa zufa gashi ya rufe kan sa da blanket kuma ba ƙaramin zufa yake yi ba..
Chapter 80 · 0% Book details