← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 157

Sashe 90

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

_8 hours later_
Daga ita sai kayan jikin ta da gadgets ɗin ta,,zuciyar ta a bushe yake dan duk wani abin da zata yiwa rayuwar ta ta gama yi already babu wani alamun sauƙi a kan fuskar ta takalmin ta ne ya saka sa tabbatar da zargin sa dan ya daɗe yana jin ana ta kai kawo tsakanin ɗakin ta da waje.
Fitowar sa kenan ya ga har ta kai bakin ƙofar falon zata yi tafiyar ta.cimin sauri ya ƙarasa bakin ƙofar ya riƙo ta yana mata magana a ruɗe cikin ɗimuwa
"Bilkisu ina zaki tafi,,,huhh?me kike shirin yin haka ne wai?why are you acting likw someone that has been possessed ko kin manta baki da lafiya ne?ina zaki tafi cikin wannan yanayi"???..motsi ko É—aya bata yi ba sai ta natsu har ya kammala maganar sa sannan a hankali cikin slow motion ta cire hannun sa daga jikin ta a hankali ta juyo da fara'a saman fuskar ta.
Riƙo hannun sa tayi cikin nata hannun tana murzawa kamar babu wani abin da ya faru ta shigar da idanun ta cikin nasa,tsagwaron son sa ne tsantsa a ƙwayar idanunta sai dai dole ta hukunta sa dan ya san ita ɗin mai daraja ce kuma tana son dawowa da martabar ta a idanun sa sam ba zata ɗauki defeat ba hukunci dole ta hukunta sa dan irin tsanar yarinyar nan da ya ƙaru a ran ta ba kamar da ba ya daɗu fiye da na da chan da bata auri Zaid ba..

"Zan tafi Zaid saboda baka buƙata ta a nan akwai wacce ta fini a gare ka wacce ina ga in har ka kawo ta nan ko ma cikin rayuwar ka zai fiye maka than zama tare da ni,"numfashi ta sauke kafin ta ce da shi
"But ka san wani abu?....barin ka da nayi ba yana nufin zan bar ka ka ji daɗin rayuwar ka bane..nooo.. I will be your...obsession Zaid Maher Muhammad i promise you....sai ka zo da gwiwowin ka biyu crying for my love but it will be too late for you dan kayi wasa da babbar damar da ka samu daga gare ni,you toyed with me you toyed with my heart for that zan na yi maka addu'ar rasa samin soyayyar ko wace ɗiya mace kuma idanun ka rufe zaka rinƙa craving ma do amma ba zaka taɓa samu ba"cikin ruwan sanyi ta mai maganar tana kaiwa aya ta wurgar mai da hannun sa ta saka kai tayi gaba abin ta..

Ko da ta kai airport kasa controlling kan ta tayi sai kuka take kamar ran ta zai fita ta rasa irin son da take mai wanda yake ƙara mata son sa a duk lokacin da ta tuno sa wannan punishment da take da niyar yi mai ba shi kaɗai ke ɗaukar raɗaɗin ba ita nata raɗaɗin har ya fi nasa..
Ko awa basu ƙara ba jirgin su ya tashi dan dama jirgin rana zasu bi amma ta san yadda tayi ta sami morning flight,sarai tana ta ganin kiraye kirayen iyayen su na shigowa wayar ta amma ta ƙi ɗagawa....

*_Few hours later at the airport_*

Bai san abin da ke masa daÉ—i ba sam ya kasa ganewa kan sa,bai san me ya mata da ya saka ta yi masa irin wannan abin ba amma ko ma dai menene ya san in suka yi landing dole iyayen su zasu saka ta gaba dan ta masu bayanin abin da ya faru da ita dan bai san abin da yayi zafi har haka ba ya saka ta cursing nasa haka ba..
Jirgin ta da nasa banbancin awa biyu ne dan haka landing É—in su ba wani tazara a tsakani...

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

*_Beautiful IYA RUWA FIDDA KAI fans this page is for u where ever u are i luv u xoxo 💋💋_*
_Mamansadeeq i can't luv u less ur last comment shakes me off seriously i laughed,I really luv that comment tnx alot_
  *28*

*_A little bit flash back to koma's village[waiwaye adon tafiya]_*

  Zaune take a tsakar gidan su ta rafka tagumi kamar wacce duniyar ta mata atishawar tsaki duk ta fita kamannin ta babu kyawun bare hasken duniyar ta mata zafi ta mata tsanani ba kaɗan ba a baya ko wani ya buɗi baki ya ce da ita wata ran zaki dawo abin tausayi ba zata taɓa gasgata maganar ba sai dai a yanzu da take tsundum cikin zafin rayuwa,juyawa tayi ta kalli ɗakin su inda ta jiyo tari mai ɗauke da amai wanda ta tabbatar da ba wata bace face mahaifiyar ta,hawaye ne ya sauko mata daga idanun ta sai ta shiga tari itama dan ba isashiyar lafiyar ce da ita ba sha'ani kawai ake yi dan rayuwar ta mata juyin masa cikin tanda,..
Tunabi mai zurfi ta shiga yi wanda ya zame mata abin kumallo tun daga buɗewar rana har faɗuwar sa,bata da abin da ya wuce mata zama ita ɗaya kamar marainiyar da tayi rashin gata a rayuwar ta tunanin baƙin aibun halin da tayi a ɗan wata ɗaya da ɗoriya take tunowa ita kanta ta san ta tafka babbar asara da mugun aiki dan abin da ta yi ta san duk mai hankali wanda ya san karamci ba zai kalle ta a matsayin ƴar halas ba sai dai ma ya bita da Allah ya tsine.wani hawayen ne ya bi kuncin ta ta saka bayan hannun ta ta share ita dai yarinya ce bata san me ya kamata da me bai kamata tayi ba dan duk abin da ta ke yi gani take kamar daidai ne shi yasa har rana mai kamar ta yau ko ta fita an nuna ta da baki ko yatsa bata iya ƙyalewa sai ta mayar da martani ƙarshe ma daina fitan tayi kullum tana gida tana faman jinyar maman ta dan shi ya fiye mata..

*_Wata É—aya a baya_*

A hanyar ta ta dawowa daga aiken da maman ta ta mata ne ta hangi motar su Zaid dan ko ba'a sanar da ita ba ta san ɗan birnin ta ne dan shi kaɗai ta sani mai mota a ƙauyen nasu shi yasa cikin azama ta nufi hanyar gidan nasu sai dai ko kafin ta ƙarasa shiga ta ji an damƙo ta an yi gefe da ita haɗe da rufe mata baki,mutsu mutsu ta shiga yi tana son yin ihu sai dai fuskar wanda ta gani ne ya saka ta natsuwa ta kasa yin ihun tayi shiru.
Cire hannun sa yayi daga bakin ta,bin sa da kallo ta yi kamar ta ga abin ƙi dan ta daɗe rabon ta da shi sai ta shiga ja da baya dan kar ya illata ta amma wani tsawar da ya daka mata ne ya sakata tsayawa cak ta juyar da kanta gefe amma ya saka hannun sa da ƙarfi ya juyo da fuskar ta suna fuskantar juna abin da yake mata gabaɗaya sun zo mata a banbaraƙwai.
Cikin isa da dakiya ya fara yi mata razanannun maganganu kamar haka
"Na lura wannan banzan ɗan nasaran ya zo ya juya maki tunani har kika iya kwana kika tashi ba tare da kin bibbiyi lafiya ta ba,na ce ba zaki yi karatun ƴan boko ba amma da yake yana da ƙarfin nasara ya zo ya juya maki hankali da tunani har kika iya tsallake sharaɗin da na saka maki,ni...niiiii....Asma'u...ni Mudan kike son juyawa baya ko ba haka ba....hahhh...ni na hankali hurɗa da yaron nan amma kika ƙi jin magana ta ko ba haka ba?iyeee?har kike gudu na kike ɓoye min takun ƙafar ki ko ba haka ba?ni Mudan ɗaya maganin dubu...in ce ki fita harkar yaron nan amma ki ɗauki ƙafa ki bi sa har gidan mai gari kina koyon fitsara da rashin kunya haɗe da nasaranci ko ba haka ba?toh bari ki ji in gaya maki a yau,,,ba gobe ba,a yanzu,ba anjima ba,zaki kai ni har inda wannan tsagerin yaron yake in gama da shi in shafe tarihin sa a doron ƙasar nan da hannun ki zaki taya ni kashe shi dan ko na kashe sa na kashe banza wofi bai da amfani a duniya dan tun da ya shigo mana gari shi ke hana mu rawar gaban hantsi shi ga shi wakilin masu kula da lafiya eyyee?na gama kaiwa bango dan bai taɓa shigowa gona ta ba sai yanzu da na ga yake ƙoƙarin wuce gona da iri dole in ja masa kunne amma tunda ba shi kaɗai yake abin ba har da ke kina taya sa dole in share sa a duniyar nan alƙawari na kenan dan haka kizo mu je tun muna mu biyu mu gama da shi in ba haka ba rayuka da dama zasu salwanta na maki alƙawari"..
Chapter 90 · 0% Book details