← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 157

Sashe 96

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk babu mai ƙwarin gwiwa a cikin su haka dai suka ciki dan tun a motar Dr Maher yake ta kiraye kirayen jami'n tsaro ya damƙa masu case ɗin bayan ya masu bayanin komai,bayan sun firfito daga motar dan a bakin gate ma motocin suka ja burki yayin da motar su Bilal yayi ciki,parking yayi ya fito Lukman ma fitowa yayi suka tsatsaya suna jiran shigowar iyayen nasu har dai suka kammala tattaunawar da zasu yi suka shigo chan ɓangaren su Hajiya Madina ma sun shige cikin gidan su da yarjejeniyar zasu koma police station bayan sun canza kayan su..

Bilal ne a gaba yayin da Lukman ke biye da shi a baya sai su Hajiya Zeenat da Prof dan kasa taɓuka komai ta yi sai da ya tallafo ta duk bata a hayyacin ta haka dai suka ƙarasa ciki tunanin su ta ina zasu fara neman ƴaƴan nasu daga abin farinciki sai a ƙare da damuwa haka...

ÆŠakin su ya kai ta tana shiga ta hau rusa mai kuka kamar an aiko mata da mummunar abu marar daÉ—in ji duk ta bi ta É—agawa prof hankali ya rasa da wanne zai ji da rashin É—iyar sa haÉ—e da rashin É—an sa É—an aminin sa ko da rigimar Hajiya Zeenat sam ya kasa sukuni kan sa yayi zafi but dole ya rarrashe ta konzai sami ragim wani zafin.
Zama yayi kusa da ita haÉ—e da kwanto da kan ta saman kafaÉ—ar sa ya shiga rarrashin ta yana bata assurance É—in inshaAllah zasu ga Æ´aÆ´an su babu abin da zai same su,jin sa kawai take amma ta saka abin a ran ta ba kaÉ—an ba..
Yana cikin rarrashin ta ne suka ji muryar Bilal yana faman ƙwala masu kira
"Umma.....Umma ina kuke.."!!!gaban ta ne ya faÉ—i dan yadda ta ji yana kwada masu kira babu inda hankalin ta ya tafi sai wani mugun abu ne ya faru tana jin ya kuma kiran ta ta tashi daga jikin sa tana jan hanci murya a disashe ta ce
"Bilal gani nan shigo mana me ya faru kake kira na haka"!!?sai ya ce
"Umma come out please ba abin a shigo bane"sai ta ji rass kan ta ya amsa
Shikenan an sace masu yara,,haka ta rinƙa ayyanawa a ran ta har ma ta koma ta zauna ta kasa fitan sai shi prof ne ya fito yana tambayar me ya faru a nan Bilal ya riƙo hannun sa yayi hanyar ɗakin Bilkisu.
Suna zuwa ya ga ɗakin buɗe ga su Jamil nan da matar sa har ma da nannyn baby Zarah duk sun yi cirko cirko gefen ɗakin kuma Lukman ne tsaye yana waya da alama dai da Abban su Dr Maher yake wayar dan a ƙarshe ya ce
'Eh Abba gata nan tana bacci'
Jan sa cikin É—akin Bilal yayi yana ce mai
"Abba ka gan ta nan,,ka ga Bilkisu bata ɓace ba basu ɓace ba"..abin mamaki abin al'ajabi
Me zai gani haka?dama yaran nan ba ɓacewa suka yi ba kuma ba sace su aka yi ba?toh me ya faru har haka da ta zo nan gidan?me ya sa ita kaɗai ce a nan ɗin kuma har bacci take yi comfortably..

Takowa yayi har gadon ya taɓa goshin ta ya ji lafiya ƙalau babu alamun rashin lafiya bare fever..but why what happened why is she here and not with her husband kafin nan ma ina shi Zaid ɗin yake?..

ÆŠaga kan sa yayi ya kalli Bilal haÉ—e da ce mai
"Bilal tafi ka kirawo Umman ku"ya amsa da toh sannan ya fita ya nufi sashen Umman sa yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin haɗe da sallama.
A razane ta É—ago ta kalle sa hankali tashe ta ce
"Bilal an lahanta mana su ko"?sai ya girgiza mata kai ya ce
"Abba ya ce ki zo let's go Umma stop all these talks"sai ta mai shiru ta tashi jiki a sanyaye ta bi bayan sa suka nufi sashen Bilkisu sai abin ya É—aure mata kai me kuma zasu yi a sashen Bilkisu..
Tiryan tiryan suka iso sai ya matsa ya bata hanya ta shige shi kuma ya bi bayan ta..
Ko da ta shiga ɗakin bata lura da Bilkisun ba hankalin ta na kan ƴaƴan ta da ke cike a ɗakin sai ta gama sadauƙarwa akan abin da take hasashe ne ya faru dan haka ta kalli prof ta ce
"Me ya faru"?sai ya girgiza kai ya nuna mata gadon da fuskar sa sai ta bi direction É—in tana son ganin ko menene.
Daɗa girman idanun ta tayi yayin da tayi arba da Bilkisu dake kwance tana sharar bacci ai tun kafin su ƙifta ido ta nufi kan gadon babu wata wata ta shiga girgiza ta tana kiran sunan ta
"Bilkisu...baby...baby tashi...tashi"!!duk kallon ta ake yi tausayin ta ne ya kama prof uwa da É—a kenan.
Tana kiran sunan ta a karo na uku kenan sai ta É—an buÉ—e idanun ta sai ta mayar ta rufe tsawon seconds uku sannan ta kuma buÉ—e idon ta sauke kan Umman ta a hankali ta shiga bin jama'an É—akin da ido har ta sauke kan Abban ta da ke shirin matsowa kusa da ita ganin ta farka..
Kafin Hajiya Zeenat tayi magana wayar prof yayi ringing dubawa yayi ya ga mai kiran sai ya ga Dr Maher ne É—agawa yayi ya kara a kunnen sa basu ji me aka ce da shi ba but sun ji yana hamdala daga bisani ya datse kiran sai suka maido da duban su kan sa
"An ga Zaid"iya abin da ya iya furtawa kenan sai aka shiga yin hamdala ana sauke ajiyar zuciya.
Ita da ke rungume jikin Umman ta tana sauraron su jin an kira sunan Zaid har ma da wai an gan sa sai abin ya bata mamaki dama ɓacewa yayi ake neman sa?.
Dawo da hankalin su suka yi gare ta umma ce ta jefo mata tambaya
"Baby ina kika shiga?ina kuka tafi?what happened?why are you all alone ba tare da mijin ki ba?me kike yi a nan?what happened we have been calling your line but you weren't picking me ya faru baby?please say something"!!duk a hargitse take mata waɗannan tambayoyi sai ta rasa abin cewa dan ita sai yanzu take ma tuno dargar da suka kwasa jiya ita da Zaid har zuwa yanzu toh wai ɓacewa yayi ne ko me.
Jin muryar Umman ta tayi tana ce mata
"Baby kin yi shiru"sai ta ɗan ɗago kan ta daga kafaɗar Umman ta kalle ta sai ta kuma komawa ta kwantar da kan ta tana ƙara tuno cin fuskar da Zaid ya mata a jiya how could he do that to her?..
Before she knows hawaye har ya fara gangaro mata sai ta saka hannu ta share su dai na su ido ne suna jiran jin ƙarin bayani daga gare ta.
Kallon su ta kuma yi ta ja hanci ta ce
"Umma am alright am fine....ki daina É—aga hankalin ki"!!sai sauran suka zazzauna ita kuma Umma ta kai hannun ta saman kan ta tana shafawa kafin ta ce
"Baby me ya faru me ya sa baku tafi gidan ku ba kuka dawo separately"??sai ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce
"Umma i can't"!!!shiru É—akin ya É—auka sai aka zubo mata idanu cikin tashin hankali Hajiya Zeenat ta ce.
"Baby ban fahimce ki ba you can't?what is it that you can't"??sai kawai ta saka masu kuka duk ta saka su cikin duhu É—ago ta Umman tayi ta fara girgiza ta tana tambayar ta
"Me kika yi baby?ɓata masa rai kika yi?rashin kunya kika mai ya maki faɗa shine kike ganin baki iya zama tare da shi"?..
Abin mamaki wai ita ma ake ba wa laifin all the good credits goes tio him shine gentile and good guy or what?
"Yi magana mana baby"?kukan ta cigaba da yi kafin ta ce
"Umma i can't..i just can't..Zaid ba ni yake so ba...he...he..heee..."sai ta kasa ƙarasawa dan kukan da ya ci ƙarfin sai Umma ta ce
"He what"??ko kafin jama'an ɗakin su ankara Bilkisu ta fara tsagewa Umman ta maganar Asma'u da Zaid ya rinƙa yi mata a jiyan abin da ta ɓoye shine sirrin su amma duk rashin mutuncin da ya mata sai da ta mayar a ƙarshe ta ce.
"I asked him to leave me alone if not i will kill him and he went ahead to come close to me"!!! ...sai ta yi shiru a lokacin kamar ruwa ya gama cinye ƴan ɗakin sai Umma tayi ƙarfin halin tambayar ta me kuma ya faru tana tsoron ba daiugun aiki Bilkisun ta aikatawa ɗan mutani ba..
"Da ya zo kusa da ke....me kika mai"???da tsoro cikin muryar ta tayi tambayar
Bata yi wani tunani ba ta ce
"Na mare sa na kuma ce mai yi warning nasa kar ya kuma nema ta and this morning i left all alone na bar sa a chan"...ko da ta kawo ƙarshen zancen ta sai mutani ɗakin suka bi ta da kallon mamaki yayin da Hajiya Zeenat ta ce da ita ta kuma maimaita abin da ta faɗa without thinking of the outcome ta maimaita.
Bata kai ga ƙarasawa ba ta ga fuskar Umman ta ya chanza kamanni ran ta a matuƙar ɓace last thing she can remember shine,cikin ɓacin rai da rage Umman ta ɗaga hannun ta a zuciye ganin haka ya sa ita kuma ta rumtse idanun ta dan ta san hannun nan a kan fuskar ta zai yi landing,sosai ta rumtse idanun ta tana jiran jin saukar marin saman fuskar ta...

*, S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

👄 °°° °°°👄
°°
°

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

31
The blame games
Chapter 96 · 0% Book details