← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 157

Sashe 44

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 4 min read

  Chan wuraren ƙarfe 11pm lokacin kowa ya kwanta babu ma masu taya ta kwanan dan an hana mutani saboda ana takura mata da yawa da unnecessary hirarraki kuma hakan na chaza mata brain jin hakan ya sa Hajiya Zeenat tafiya gida ita kuma Hajiya Madina ta ce babu inda zata tafi a nan zata kwana sai dai ba ta gefen ɗakin Bilkisu ba rather ta ɗakin Zaid hakan bai mata daɗi ba but ta san duk yadda za'a yi dole ne ma kawai ta gan shi yau sai dai a yi haƙuri da Bahajjatu zata tafi ma sai da ta tsaya ta gaya mata wata magana maganar da ya tsaya mata a rai
"Bilkisu you are in love but you keep on denying it kin fake da cewa damuwa da shi ne ya sa kika kasa natsuwa again ɗazu mun yi maganar Aslam and you became furious and irritated mun yi maganar Asma'u sai kika sami mood swing immediately kika yi switching and you responded my question by saying you don't wanna talk or hear anything regarding her,,,if you don't have or feel anything about my brother then why did you reacted in such manner?girl don't feel shy i guess abin da iyayen mu suka hango is finally becoming real and reality dan haka ni dai nawa shawarar shine go for it..go for what you want and follow your heart i assure you you will never regret your choice goodnight  and take care of yourself as well my brother"!!..

Tafiya tayi ta bar ta da mamakin maganar amma gaske ne wai?ko dai kawai hasashen Bahajjatu ne?but how a ce kana son mutumin da maganar kirki na tsayin mintuna biyar bai taɓa shiga tsakanin ku ba sannan har a ce so ya gitta?no. Wannan ma ba gaske ba ne weighing the distance and differences between the two of them sai kawai ta ga inaa maganganun Bahajjatu shiririta ne ba zai taɓa zama gaskiya ba dan ita ta san in banda tausayin sa da take ji sakamakon halin da yake ciki bata tunanin wani abu mai girma wai shi sunan shi so yana son kutse ya shigo tsakanin su haba a'a wannan shurmen baha ne kawai ba gaskiya ba.
  Da wannan tunanin ta lallaɓa ta saci hanya ta rinƙa ɓoye fuska har ta iso ɗakin Zaid babu kowa a wurin haka ma a ɗakin babu kowa sai shi kaɗai hasken ɗakin is very deem sai da ta kai mintuna biyu a tsaye tana wasi wasin ta shiga ko a'a shin zata iya hana kanta yin kuka in ta ga halin da yake ciki ko baza ta iya ba.ƙarshe shahada tayi ta tura ƙofar ɗakin ta yi sallama sannan ta shiga jikin ta a sanyaye duk ta ji gwiwar ta ya sage,,takawa ta fara yi kaɗan kaɗan tana jin fargaba.
His face is turned laterally ta gefen dama dan ana jujjuya mai position bayan kwana É—ai É—aya saboda a yi preventing pressure bed sore saboda is very obvious wa masu long hospitalization.
A ɗarare ta nemi kujerar kusa da gadon ta zauna tana son ganin fuskar sa a hankali ta leƙa tana fargaba har dai ta sauke idanun ta a kan fuskar sa,gaban ta ne ya faɗi haɗe da tausayin sa dan a normal basis shi ba mutum ne mai ƙazanta ba yana da tsafta he try as much as possible dan shaving excess hairs a fuskar sa but yau sai gashi almost half of his face is covered with hairs though ba a ƙazance yake ba but yana buƙatar gyara,kamar a kira sa ya amsa but babu hali,tuno da rayuwar su ta rinƙa yi tun kafin su tafi outreach har izuwa ranar da abin ya faru.
According to doctor ya ce ba zai farfaɗo ba sai nan da watanni 3-4 masu zuwa,sai ta ju kamar ruwa ruwa a kan kumatun ta sai ta kai hannu a hankali ta taɓa ta ga hawaye ne,cire hannun tayi ta shiga rera kuka kukan da ke da ma'anoni daban daban dan a ƙunshe yake da baƙin ciki,tsana,fansa da wani dalilin na daban da bata san yaya zata yi classifying ba..
Magana ta shiga yi mai tana yi tana jan hanci idanun kuwa basu daina fitar da hawaye ba dan zuciyar ta na cikin ƙunci da baƙin ciki.
"Zaid me yasa ka mana haka?ba fah ni kaÉ—ai ka saka a cikin halin damuwar nan ba.Ammi,umma su Abba,yaya jamil,yaya Afzal da Hakim ga baha ga Bilal yaya Lukman ka san kuwa ka saka kowa cikin damuwa da tashin hankali..ta ja hanci ta goge hawayen ta cigaba,dan haka ina son sanar da kai Zaid muddin baka tashi ka kwantar mana da hankali i will never speak to you again did you understand"?kamar da mai rai take maganganun tsawon lokaci bata san da kanta kawai take maganar ba da ta ga kuka da surutun ba zai fishe ta ba sai ta shiga yi mai addu'a ta manta dare ya tsala kuma ba a É—akin ta take ba dan haka tana cikin addu'ar bacci yayi gaba da ita dan kanta tayi leaning a bedside..
Chapter 44 · 0% Book details