← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 157

Sashe 114

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Iya ƙoƙari tana yi dan ta kama kan ta ta nuna mai ko babu shi rayuwar ta zai cigaba in kuma ya gane ya dawo gare ta duk ɗaya zata karɓe sa hannu bibbiyu dan son sa ya gauraye ko ina na jikin ta bata iya dakata kan ta daga urge da take yi saboda shi.
  Wasu lokutan takan yi kukan ta ita kaɗai in kuma Bilal na nan sai ta tasa sa gaba ta rinƙa kuka tana dukan sa tana assuming da Zaid take yi dan tun ranar da ta ɗauko sa daga office yayi mata alƙawarin backing out cikin plan ɗin.
  Tunanin sa na yawan addabar ta ba kaɗan ba sai dai she prefer staying alone ta fi so sai Zaid dan kan sa ya yi realising cewa yana son ta yana mararin ta yana son kasancewa tare da ita without these bata da right na kiran kanta matar sadan bai damu da ita ba haka bai san mutuncin ta ba..

Yau tun safe da ta tashi take jin kasala da bacci bacci haka kawai a ƴan kwanakin nan kawai sha'ani kawai ake yi amma bata cikin lafiyar kan ta komai baya mata daɗi bayan baccin nan sai marmari marar ma'ana tun tana iya daurewa har ta kasa in ta fara craving ba sauƙi ne kawai managing kan ta take yi kuma bata bari kowa ya sani ba dan gani take duk rashin mijin ta ne kusa da ita sai ta rinƙa shashare abin tana basarwa..
  Wani lucky thursday ta tashi cikin farinciki copping with stressors da ke kawo mata farmaƙi a ƴan kwanakin nan bata tashi cikin farinciki but yau tun tashin farko da tayi da asuba ta tsinci kan ta cikun annashuwa da jin daɗi marar misali is not like she enjoys staying at home but ko ba a kula ta tana jin daɗin zaman saboda Bilal bai barin ta cikin kaɗaici hakan na rage mata kewa..
  Saukowa tayi cikin kuzarin ta tana anmashuwar ta hatta da ahalin baki ɗayan su sun ji mamakin wannan annashuwar nata na yau sai dai Bilal bai yi mamaki ba.
Gaisuwa tayi sama sama da su ta kama hanyar fita sai Umman ta dakatar da ita
"Bilkisu wait"!!dakatawa tayi cak sai ta juyo da murmushin ta ta ce
"Na'am Umma"irin ko a jikin ta ɗin nan tayi responding sai abin ya ba su mamaki tasowa Hajiya Zeenat tayi ta tako har gaban Bilkisun ta tsaya tana examining nata,sai da ta gama ƙare mata kallo tsaf sannan ta ce
"Why are you over excited"??surprise look ta ba ma Umman nata kafin ta ce
"Don't i have the freedom and right to be happy"?sai ta girgiza mata kai tana ce mata
"Of course you do baby"sai Bilkisun tayi murmushi tana faÉ—in
"Alright zan tafi dan ina da surgery da zan yi"gyaÉ—a mata kai tayi ta ce
"Wish you success"
"Thanks"ta bata amsa daga haka ta sa kai tayi ficewar ta..

A wurin aikin ne har ta canza zuwa scrub sai ta ga kamar tana buƙatar wani abin sai ta cire ta yi waje cikin sauri dan bata yi zaton crave ɗin nan zai taso mata ba.
Cikin sauri sauri ta nufi hanyar fita tana zuwa bakin ƙofar hankalin ta na wani wurin bata ankara ba ta ji ta bangaje mutum cikin sincerely apology voice ta ce
"Am do sor....."maƙale mata kalmar tayi ta kasa ƙarasawa sakamakon ganin sa duk ya canza kamanni,suma ne cike a fuskar sa gashi dai yayi shiri mai kyau amma da an gan sa an ga wanda kwanciyar hankali ya ƙauracewa.
Rass ta ji gaban ta ya faÉ—i yanzu Zaid É—in nata ne ya dawo haka wani iri kamar marar gata?ya rasulillahi me ya same sa
Muryar sa ne ya mata amo a kunnen ta
"Be careful please"sai ta ɗaga ƙwayar idanun ta daga saman lips ɗin sa da take kallo ta mayar cikin ƙwayar idanun sa sai kuma suka tsaya kallon kallo ita so take ta san me ya mayar da shi haka duk ya canza mata son sa ne ke fizgar ta kamar zata yi hauka son sa na bala'in yi mata tafiyar tana a kafatanin jikin ta shigar ta son sa ke yi da a ce bata mallake sa ba da ta tafka asara har da present situation da suke ciki tsakanin su bata taɓa daina son sa ba,thank Goodness that jesus is a muslim at least he is her's ko basu kusa ko basu tare mijin ta ne,she is entangled what to do?...

Ƙura mata idanu yayi yana kallon ta kamar kar ya daina kallon ta kamar su dawwama a haka har ƙarshen rayuwar su kwata kwata ya manta a asibiti suke sai ya maida duka hankalin sa gare ta yana kallon ta sai ya ga kamar ma ƙara masa kyau da ƙwarjini tayi a ƴan kwanakin da bai gan ta ba..
Ita ce tayi ƙarfin halin ɗan ja da baya tana son hana kan ta fallasa damuwar ta a gaban sa sai dai ta kasa dan crave ɗin abin nan ya assasa mata dan haka ta ɗan raɓe ta gefen sa ta wuce sa but unfortunately tana kaiwa tsakiyar passage ɗin ta yanke jiki tayi ƙasa saura kaɗan ta faɗi amma hakan bai faru ba dan tsintar kan sa yayi ta bayan ta ya taro ta dama yana biye da ita amma a tsanake yake tafe dan kar su yi bumping juna tana faɗi jikin sa haka ta tafi sululu idanun ta lumshe numfashin ta na fita wani iri.
A birkice ya shiga jijjiga ta yana kiran sunan ta haÉ—e da tapping cheeks É—in ta
"Baby..baby...oh no baby common...please...please, open your eyes...bana son irin wannan wasar please wake up"ko motsi bata yi ba haka yana kiran sunan ta yana jijjiga ta har ya É—au lokaci rungume da ita a jikin sa.
Ɗago kan ta yayi ya manna a ƙirjin sa yana kai kawo a durƙushe kamar zai yi kuka dan tsoron sa da fargabar sa shine ba dai wani ciwon ne ya kamata ba kamar yadda yake gudu,tsoro ne mai tsanani ya shige sa gashi in har ta shiga halin rashin lafiyar nan sam mantawa yake da yadda ake bada taimakon gaggawa sai ya ɗau lokaci kafin yayi nazari brain nasa ya gaya mai daidai..

Kiran sunan ta yake kamar marar hankali tsawon lokaci bai yi tunanin yi mata wani abin ba sai da wata ta zo wucewa daga cikin clients dake asibitin sai ta ga abin da ke faruwa ai kuwa ta buɗe murya tana ƙwala kiran a kawo ɗauki da sauri aka shiga firfitowa tuni aka cike wurin cikin ƙwarewa wani doctor ya yi azamar janye ta daga jikin sa yana son ɗaga ta ai tuni ya hankaɗa sa gefe yana faɗin
"Can't you see that she is my wifee huh"?sai doctor É—in ya ja baya yana mai ce da shi
"Am sorry Dr ZM but she is losing her consciousness do something please"sai a sannan ya dawo da duban sa gare ta yana gwalalo idanun sa waje cikin fargaba kamar wawa ya maido da idanun sa ga doctorn yana mai ce da shi
"She is losing consciousness"???gyaÉ—a mai kai yayi saumi ya dawo da idanun sa kan ta kamar an tsikare sa yayi wuf da ita a jikin sa ya fara tafiya da ita yana ce ma mutanin da ke hanya
"Get lost...excymuse me...ku matsa min a hanya"haka ya rinƙa faɗe faɗe kamar marar hankali ya zauce da yawa what could possibly happen to her why the sudden entanglement.
Mamakin sa jama'an wurin suka yi sun É—auka zai shigar da ita ciki ne sai a duba ta amma sai suka ga yayi hanyar waje da ita duk a hargitse bai ma gani sosai dan rashin lura ne ya sa har ya wuce Dr Muhammad bai sani ba har yana ce mai
"Move...get out of the way will you"!!da matuƙar firgici yayi maganar ya shige da ita motar ya yi saurin zagayawa ya shige yana haki ba ɓata lokaci ya ba motar wuta ya fige ta da matuƙar speed yayi gaba while Dr Muhammad has been wondering me ya sami Baby doctor ɗin da Zaid ya ruɗe haka again ina zasu tafi?girgiza kan sa yayi ya shige daga cikin asibitin dan jin ko akwai wanda yayi witnessing abin da ya faru dan shi zuwan sa kenan...

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

*34*

*_Autonomy_*
Chapter 114 · 0% Book details