← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 157

Sashe 67

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da fitan su suka shiga cab da ke tsaye a wajen hotel É—in dama basu ci abincin safe ba dan haka da mai cab yayi tambayar inda zasu tafi sai ya ce da shi ya kai su nearby eatery sai mai cab ya ja suka yi tafiyar da bata wuce mintuna ashirin ba ya ja ya tsaya ya yana mai ce da su sun zo.
  Fitowa suka yi ya miƙo mai kuɗin sa ya ja yayi gaba su kuma suka shiga takawa har suka iso glass translucent four sided sliding door ɗin eatery ɗin suka yi sliding yayi ciki da su a juyi na biyu wurin madaidaici ne ba babba ba ba ƙarami ba ga wun regular nan a gefe ga vip a gefe nesa da wun regular sai kuma vvip da ke saman upstairs.
  A ran sa ya fi son su tafi saman wun vvip dan yana da sociophobia when it comes to eating in public hakan na ɗaya daga cikin dalilin sa na ajiye ice da ta kawo mai the other day dan baya iya cin abinci a gaban jama'a da yawa ko family ɗin sa ba kasafai yake son zama suna cin abinci tare ba dan baya taɓa sami comfortability in yana cin abinci ana kallon sa ko ba'a kallon sa yana samin nervousness.
  Dan haka yana gama ƙare ma wurin kallo ya mata alama da su haura sama,ita dai bata san dalilin sa na cewa su haura saman ba dan ta ga akwai tables a ƙasa but ya ce su haura sama.
  Gently suka haura saman inda ɗaya daga cikin host ɗin ta yi leading nasu har zuwa desired choice ɗin Zaid dan shi ya nuna inda yake son su zauna.
  Wurin rufe yake dan wanda yake zaune a nan fannin ba zai iya shaida wanda yake zaune a chan fannin ba saboda yanda aka yi designing wurin an yi designing nasa ne cikin yanayin sirri privacy is ensured a wurin sosai komai naka a tsare yake dama baturi na ba ma tsari haƙƙin sa sai wurin ya ma Zaid sosai har yake tunanin for the main time of their staying a germany nan zasu na zuwa cin abinci dan wurin ya birge shi sosai.
   Round glaas table ne mai ɗauke da attracting bouquet a vase ƙanana ƴan gudil gudil sai light candles dake cikin glass container gefe kuma sparking lights ne masu different colours suna walwal bayan already akwai hasken farin wutar lantarki dake fitowa daga bulb dake sagale daga saman vvip ceiling arena ɗin wanda shi kansa ado aka mai abin kallo dan glass ne mai kalar golden da silver yayi kamar oval ta ƙasa sannan yayi curving daga sama kujerun na mutim biyu ne kawai sai dai in mutum na buƙata sai a ƙaro wasu like in case of family eating outing treat..

Ba shi kaɗai ba har ita wurin ya birge ta har take tunanin sanar da shi ko nan zasu rinƙa zuwa cin abinci kafin su koma because privacy na gaba da komai kuma su biyu ɗin na son privacy sosai..  
  Shi yayi gaba ya iso kan ɗaya daga cikin kujerun ya ja mata baya alamun ta zauna sai ta kalle sa da murmushi a saman fuskar sa ya ce
"Ladies first"sai itama ta mai murmushi ta zauna a hankali tana wani basarwa kamar ba mamaki ne ke damin ta ba sakamakon manly treats da yake ta mata tun da suka fito har zuwan su nan ba..
  Juyawa yayi ya koma fannin ɗaya kujerar yana mai ƙoƙarin cire jacket ɗin sa kafin ya zauna.
  Hanging jacket ɗin yayi a wani abin hanging kaya da ke bayan sa sannan ya kalle ta haɗe da ɗaga mata gira ɗaya sama kafin ya ce
"You"??yana mai nuna jacket É—in ta da chin É—in sa sai girgiza kai alamun a'a
"Okey"ya bata amsa sannan ya zauna yana mai miƙo hannun sa ga host da ke tsaye a daga gefen sa dan jiran ya nuna ordern sa kafin ta ba ma bBilkisu itama ta nuna nata sannan a kawo masu.

  Bayan ya karɓa sai ya kalla kusan sau biyu sannan ya ɗago ya miƙo mata ba tare da ya ce komai ba sai ta tambaye sa cikin sakin fuska
  "What did you need sir"?kallon ta yayi for a second kafin ya buɗe baki ya ce da ita
"Give her let her choose"!!daman haushi ya fara kama Bilkisu ganin yanda ta wani tsaya mai a kai tana murmushi but jin ya ce a bata ta yi zaɓin sai ta ji sauƙe kenan bai ma san host ɗin na kallon sa ba kenan.
 
  Miƙo mata tayi tana murmushi ta ce
"Here ma'am"karɓa tayi a ɗan fusace ta kalla sai ta ɗago ta kalle sai sai ya juyamata eye balls na sa haɗe girgiza kai alamar ya bar mata zaɓi dan haka sai ta kirawo host ɗin da hannu ta nuno mata abin da suke so wato black apple mixed with meant flavour tea marar sugar sai hamburger haɗe da wani African dish course wato Passion La Braise wanda ta mata alama da ta kawo masu su biyun.
  Da murmushi ta yi nodding kai haɗe da fita suka rage su biyun su ta fiddo wayar ta ta shiga searching security na wurin sai ta ga akwai full security safety dan haka ta mayar ta ajiye a kan table ɗin ta ɗago sai ta ga ita yake kallo ɗan murmushi ta yi ta ce
  "Da matsala ne"??sai ya girgiza kai sai tayi shiru itama.
  Babu jimawa host ɗin ta dawo da order da suka yi placing saman trolling table da zuwan ta ta sassauke su a saman table ɗin duka rufe suke da food covers manya manya saboda gudun kar wani abin cutarwa ya faɗa cikin abincin unknowingly.
  Da ta gama jere masu sai ta matsa ta ce da su
  "Have a nice breakfast"babu wanda ya tanka mata har dai ta juya ta tafi dama akwai alarming device handle da ke ajiye a saman table ɗin dan in sun kammala su danna sai a zo a kwashe plates da dirts ɗin dama mostly da disposable items suke amfani dan kar wani mai cuta ya yi amfani da wani abin sannan marar cutar ya kwasa wannan yana ɗaya daga cikin abin da ya sa eatery ɗin ya fito sosai a cikin Berlin city na ƙasar germany ɗin.

  Da host ɗin ta so tsayawa buɗe masu covers ɗin amma Bilkisu ta nuna mata ba komai ta tafi kawai basu buƙatar hakan shi yasa ta tafi.
  Daga zaunen Bilkisu ta shiga bubbuɗe food covers ɗin har ta kammala.
Ƙamshin tea ɗin ne ya bige shi sai ya shaƙi ƙamshin duk Bilkisu na kallon sa sai ta ji daɗi choice ɗin da ta masu ya mai daidai a nan ta gano cewa yana son black apple mixed meant flavour tea ta sami exposure ɗaya sai ta ga ya zurfafa a son jin garɗin abin furtawa ne kawai bai yi ba dan haka ta ce da shi cikin tsokana
  "Dr Zaid Maher...your breakfast is ready feel free"!!!
  Buɗe idanun sa yayi yana jin wani yanayi na ziyartar sa a yayin da ta kirawo sunan sa sai dai bai san dalilin da ya sa ya sakar mata murmushi ba
  Silently suka fara cin abincin su hankali kwance garɗin abincin na riskar su a hankali har suka yi rabin abincin babu wanda ya ce ƙala a cikin su iyaka dai sun ɗago sun haɗa idanu a tare sau huɗu a course of cin abincin nasu in sun haɗa idon sai su sakarwa junan su murmushi su cigaba daga dukkan alamu abincin ya masu daɗi dukkan su..

  _1 hour later_
 
  Sun kammala cin abincin suna goge bakin su da tissue sai ya kalle ta ya ce
"Are you okey..i mean you're satisfied"??sai ta gyaÉ—a mai kai sai suka zauna zaman jiran zuwan host É—in dan yayi pressing alarm bottom É—in some seconds ago.
  Babu jimawa sai ga ta ta iso da fara'ar ta ta nuno mai bill ɗin su ya miƙa mata  master card tayi amfani da shi a manual pos transaction machine device ta tambaye sa pin ya bata ta ce thanks daga haka tayi abin da zata yi ta cire ta miƙo mai haɗe da ce mai
  "Hope you enjoyed and you will make a return next time"!!!abin takaici harara Bilkisu ta banka mata haɗe da jan tsaki wanda ya saka su su biyun kallon ta sai dai ta basar ta miƙe tana mai gyara jacket ɗin ta.
  Shima miƙewar yayi yana mai ɗaukar hanged jacket ɗin sa dan sakawa.
Ta riga sa barin wurin shi kuma ya biyo ta a baya bai dai ce komai ba but he can sense the mood swing that occur in her just a while ago..

Rai a ɗan ɓace ta ja ta tsaya a bakin cab da ke jiraye a wajen eatery ɗin,ko da ya fito ya same ta a tsaye tana jiran sa sai yayi joining nata a tsayuwar bata ce da shi komai ba har sai da dan kansa ya ce sa ita
"So where should we go now Dr Bilkisu Muhammad Sulaiman"wato rama abin da ta mai ɗazu acikin eatery ɗin nan yayi amma nashi har da ƙarin sunan grandpa ɗin ta.
Instead ta bashi amsar tambayar da ya mata sai tayi shaking kan ta tayi shigewar ta cab leaving him smiling all alone.
Biyo ta yayi ya shiga ciki sai mai Cab ya tayar da mota ya fara ja suka hau tafiya basu ce da shi ga inda zasu tafi ba har sai da ya tambaye su sai shi Zaid É—in ya ce da shi ya kai su museum da ke a cikin Berlin city.
Chapter 67 · 0% Book details