Sashe 24
Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read
Jin hakan duk sai Dr Hussain ya ruɗe ya kasa zama har dai matar sa ta tambaye sa me ke faruwa a inda ya ma kasa sanar da ita sai dai ya ce mata ta rufe gida shi zai je ya dawo dan abokin sa da abokiyar aikin abokin na sa suna cikin wani hali dama da gidan su a ƙauyen kasancewar hali irin ta fulani ba su wani samin damar sakewa in sun zo hutu saboda kunya shi kuma ba mai kunyar ba ne dan haka ya ga cutuwa yake yi sai kawai ya sa aka fara yi mai gini a ƙauyen far from gidan surukan na sa toh a nan suke hutu in sun zo ƙauyen.
 "Dr in rufe ƙofa ko dai in biyo ka"?ta faɗa kamar zata mai kuka sai ya ce
"A'a ba biyo ni zaki yi ba dan babu mota abin hawa zan shiga bana son ki fita ki zauna a gida kawai and make sure you lock everywhere humm"?sai ta girgiza kai dan bata saba da jan magana ba in bata umarni.
Rako shi tayi har bakin gate É—in su da ya fita ta koma ciki ta rufe tana mai addu'ar Allah ya kai sa lafiya ya dawo mata da shi lafiya dan zuwa lokacin 9 na dare yayi ga tsoron fitar na sa ga tsoron zama ita kaÉ—ao sai abin ya mata yawa ta kasa kwanciya ta dawo parlor da wayar ta a hannu tana duba time..
  Da kyar ya sami rickshaw ya tsare ya mai kwatancen inda zai tafi tiryan tiryan ya kai sa y biya shi kuɗin shi ya fita ya shiga cikin gidan inda ya ga jama'a cirki cirko a tsakar gidan da sauri ya tambaye su inda Dr Zaid yake nuna mai ɗakin sa suka yi bai tsaya ɓata lokaci ba ya shiga ɗakin ya gan shi kwance kamar marar rai shi kan sa ba dan likita bane wanda aka kira akan ya bada taimako ba toh baya jin zai iya taɓuka wani abin dan with the physical eye examination da ya ma Dr Zaid ɗin baya jin zai iya concluding cewa Dr Zaid is still existing but he have to put himself ya samo mafita dan haka fita yayi ya tambayi car key ɗin aka miƙa mai ya ce a saka baby doctor a motan kafin su fito da Dr Zaid hakan aka yi dan har lokacin bata farfaɗo ba sai aka saka ta a front seat shi kuma da muktar suka ƙoƙarta suka fito da shi aka buɗe back door suka saka shi ya rufe ya shiga gaban motar kafin ya tayar da motar ya ce da su
 "Ku harhaɗa masu kayan su zan dawo in kwashe dan muna zuwa asibitin zan bar su in tafi tare masu jirgi dole su bar garin nan a yau ɗin nan"!..ya ja motar yayi gaba dan shi tun farko bai yi supporting Dr Zaid ɗin ba akan kawo outreach ɗin nan ba dan ya sanar da shi ƙauyen akwai haɗari sosai ta yadda mutum ba zai taɓa tsammani ba gashi nan yanzu sun faɗa a tarkon ƴan iskan gari dan yana da tabbacin ƴan iskan garin ne suka masu haka saidai shaf ya manta ya tambayi wanda ya masu wannan abin nevertheless in ya koma karɓo kayan su zai tambaya dan babu abin da zai mayar da su dajin nan sai dai a history dan ko su da ke ƙauyen akwai tazara sosai tsakanin gidan su da na mai gari.
Yana jan motar yana ta tunane tunane sai ya ga wayar Zaid É—in na blinking ya kai duban shi sai ya ga an saka
 'Lil bro Luk' bai san ko wanene ba sai ya ɗaga wayar ya kara a kunne
 "Assalamu alaikum"yayi sallama sai aka amsa mai
"Wa'alaikumul salam please ina yaya Zaid"?aka yi tambayar still bai gane mai maganar ba sai ya ce
"He is safe yanzu ma asibiti zamu tafi ni abokin aikin sa ne sunana Hussain yanzu ake sanar da ni abin da ya faru kuma nima ina gida mun zo hutu shi yasa na yi hanzarin tafiya É—auko su yanzu zamu tafi city hospital É—in Yola daga nan zan tafi booking masu flight dan bana so su kwana a garin nan"
Ajiyar zuciya Lukman yayi daga ɗaya ɓangaren kafin ya ce
"Mun gode sosai ɗan uwa dama fligt ɗin anjima zamu bi mu zo ɗaukan su daga nan mu dawo gida nut since kai kana nan ina ga sai dai mu yi booking masu jirgin Germany dan na san a yadda aka ce an yi attacking ɗin shi ɗin nan Ammi ba za ta yarda a yi treating ɗin shi a nan ƙasar ba ga kid sis ɗin mu duk an ce itama bata farfaɗo ba ina ga tafiyar su chan zai fi".
"Eh toh kai sai ku fara processing masu visa ni kuma zan yi na nan dan abin ya mana sauri"ɓoye mai gaskiyar lamarin yayi dan da zuwan shi ya ɗag kan Zaid ɗin sai ya ga wurin yayi swelling alamun akwai internal bleeding profuse bleeding ma ba kaɗan ba hakan na nufin duk inda aka kai aka komo ba zai farfaɗo nan kusa ba that is in an yi nasarar saving life ɗin shi,sanar da family member ɗin Dr Zaid ɗin da ya kira ba zai taimaka ba instead discouraging zai janyo sai yayi shiru kawai ya bari akan in sun isa chan asibitin a basu taimakon gaggawan da za'a iya kafin ya gama processing komai that means har shi kan sa da matar sa have to leave that same night..
Bayan kamar mintuna arba'in suka iso cikin wani asibitin gari though ba shi ne babban hospital a town ɗin ba amma shine nearby hospital dan haka shiga yayi ya nemi taimakon ma'aikatan aka zo aka ɗauke su aka yi ciki da su zasu fara yi mai surutan police report ya nuna masu licence ɗin sa na Dr ya kuma sanar da su in basu yi sun taimake sa ba yana iya rasa ran sa kuma alhaki a hannun su sannan zasu amshi sammaci daga kotu dan iyayen shi ba zasu bar asibitin ba jin haka suka fara ƙoƙarin su da ya ga sun fara sai ya sako masu labarin abin da ya kawo su ƙauyen da irin taimkon da suka bayar sai hakan ya saka su ƙara himma suka cigaba da aikin taimakon gaggawa daga nan ya sanar da su yana zuwa ya fita ya wuce ya shiga motar sa dare ne dan 10 yayi a lokacin gudu sosai yake ta shararawa har ya isa inda yake son tafiyan bai ji da sauƙi ba dan da ƙyar ya samo visa ɗin mutani huɗu ta POS aka yi komai ya kamo hanya ya dawo gidan mai gari dan kwashe kayayyakin su a nan ya tambayi wanda yayi wannan ta'asar suka sanar da shi sai ya girgiza kai kawai ya wuce suna tambayar sa jikin su sai ya ce shima bai sani ba dan haushi ne ke cin sa sosai ya daɗe yana jin labarin wannan tsagerin Mudan ɗin toh kuwa tunda ya taɓo ɗan gwal zai yi da ya sanin rashin sa'ar sa a duniya dan ya san yadda mahaifiyar Zaid ke ji da shi ɗin nan sam ba zata taɓa ɗaukar wannan shashancin ba sai ta sa an hukunta mata yaron.
 Daga nan gidan shi ya wuce inda tausayin matar ta sa ya kama shi dan idanun ta duk a kumbure suke alamun dai kuka tayi bayan tafiyar sa ai kuwa tana ganin ya shigo ta miƙe da sauri ta rungume shi ta sakar mai kuka a yanayin da yake ciki shi kan shi kukan ne sauƙin zuciyar sa amma bai bari yayi ba sai ya rarrashe ta ya ja ta zuwa bedroom ɗin su ya zaunar da ita ya ɗauko mata hijabin ta ya saka mata ya ɗauko masu jakar tafiya ya shiga shirya masu kayan su cikin sauri ita dai bin shi da ido take yi dan ta kasa tambayar sa me hakan ke nufi har dai ya gama ya janyo jakar zuwa gaban ta ya riƙo hannun ta ya miƙar da ita tsaye ya ce da ita
 "Sweetheart am so sorry zamu koma gida my friend is in serious pains da asibitin garin nan ba zasu iya da shi ba in kuma muka yi delaying toh muna iya rasa sa"jin haka sai ta waro idanun ta waje sai ga hawaye saurin share mata yayi ya ce
"Is okey Allah zai bashi lafiya"daga haka ya rungumo ta ta gefe suka fito gyara parking É—in motar yayi suka fito a ciki ya rufe masu gate É—in suka fara tafiya..
**********
 Sauke wayar yayi daga kunnen sa ya ce
 "Big bro akwai wanda ma yayi aikin da zamu tafi yi a chan"sai ya ɗago ya kalle shi yana jiran jin ƙarin bayani. Zama yayi ya sanar da shi komai sai ya miƙe tsaye ya ce da shi