← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 157

Sashe 11

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai amma na ji daɗi da ni duk kallon da nakewa ƴan birni basu da kirki kuma basu saka ire iren kayayyakin mu ashe ba haka bane" daga haka ta kawo mata abinci cikin tray babba ga kunun fulani da ya sha kindirmo ga sugar a ɗan ƙaramin kwano mai murfi ga alale mai rai da lafiya a food warmer ga soyayyun kaji nan an masu pepper chicken sai ƙamshi suke yi ga plate nan da spoon haɗe da ruwan wanke hannu komai dai MashaAllah

Zama tayi a dardumar da aka shimfiÉ—e mata ta zuzzuba ta fara ci tana kaÉ—a kai alamun girkin ya mata daÉ—i ta É—ago ta ce

"Amma wa yayi girkin nan hala"?dariya ta yi ta ce

"Ni ce na yi ya miki daÉ—i"? Jijjiga kai tayi tace
"Ya min sosai gaskiya zaki koya min"daÉ—i ne ya kama ta tace

"Ai ko zan koya miki kala kala"rage murya tayi ta ce
"Kin san kuwa saboda iya girki na ta sa mai gidan mu ya fi so na?duk sauran tsohuwar hannu gare su basu iya girkin zamani ba in kuma aka ce badu yarda ba su ƙi yarda"dariya maganar ya bata dan haka ta dara ta ce
"Yayi kyau toh ai zaki koya min dai ni"ta ce sosai ma
"Yauwa toh bari in yi in gama"
"Toh likiciya"darawa tayi dan sunan dariya yake bata daga haka suka cigaba da hira kaɗan kaɗan har ta gama lokacin har 2 ya wuce a nan ne kuma matan gidan suka rinƙa zuwa gaishe ta ɗaya bayan ɗaya kowa na son samin shiga a wurin ta ita abin ma mamaki yake bata kishi muraran babu ɓoyo sai dai ayi ta dariyar fatar baki

Bayan fitar su ta tafi wun mai gari suka gaggaisa ya mata ya hanya suka ɗan taɓa hira sai duddubawa take dan ganin ta inda zai fito amma bata hange sa ba kuma babu wanda ya sanar da ita inda yake dan haka bayan sun koma ciki suna tsaka da hirar su ita da zulfa'u aka shigo kiran ta wai ta zo su tafi
Ta zo su tafi ina kuma?ta ma kanta tambayar dan haka ta ce da zulfa'u tana zuwa ta fita

Ɗan duba shi tayi kafin ta hango shi cikin half jumfa da hula baƙaƙe kallon seconds ta mai kafin ta fara takawa zuwa wurin shi ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta ce
"Gani"sai da ya ƙare mata kallon ƙuril har ta fara tsarguwa kafin ya ce

"Ba cewa nayi ki zo empty handed ba cewa nayi ki zo mu tafi hakan na nufin ki zo da kayanki mu tafi ainihin masaukin mu"! Kallon shi ta yi ta ce
"Akwai wani masaukin da ya fi wannan ne"?É—an jan aji yayi kafin ya ce

"Yeah cikin ƙauyen zamu tafi inda a nan zamu gabatar da outreach ɗin nan kawai somintaɓi ne ai kin fahimta"? Ya wani sha mur wannan abin da mamaki yake cikin ƙauye kuma?jin kai irin nata ya sa bata kuma mai tambaya ba ta juya ta koma cikin gidan cikin wani yanayi ganin haka ya sa zulfa'u tambayar ta ko lafiya bata ɓoye mata komai ba ta sanar da ita ai kuwa ta ce bsta san da zancen ba babu inda zata tafi da haka ta wuce zuwa wun mai garin bayan mintuna ta dawo ta ce da ita

"Ai an gama mai gari ya ce babu inda zaki tafi tunda kin ce nan ya miki kuma shima bokan turan ai nan ya kamata ya zama masaukin sa ba chan da yake son ku tafi ba"wani sanyi ta ji at least ba zai kai ta ƙauyen da ya fi wannan typical ba dan haka ta share zancen nasa ta cigaba da sabgogin ta har dare bata kuma ji daga gare sa ba bata kuma damu ba.

A ƙaida ranar monday zasu fara gabatar da outreach ɗin wanda zai ɗauki steps uku ne a cikin sati ukun da zasu yi,satin farko zasu binciko su zaƙulo matsalolin mutanin garin dan su yi creating rapport da mutanin garin a sati na biyu kuma zasu gabatar da outreach ɗin sai satin ƙarshe kuma zasu ƙara koyar da su abubuwa dangane da lafiyar su.

Bata sami network ba ma a ranar haka ta kwanta washegari da ya kasance litinin kuma ranar zasu fara wanda zai yi taking place ne a wani primary school ɗin ƙauyen tun safe ta gama shiryawar ta ta zauna zaman jiran sa ya zo su tafi bai aika a kirawo ta ba sai da ƙarfe tara na safe ya buga sannan ya aika a korawo ta,sallama suka yi da ƴan gidan ta fita cikin shigar mutunci doguwar riga maroon da gyalen ta ta yafa ta ɗau ƙaramar jaka inda ta saka wayar ta da pens ɗin ta tana jiran sa babu daɗewa aka aika kiran ta har ƙofar gida zulfa'u ta rako ta suka yi sallama

"Goodmorning"tace da shi ya ji mamaki dan haka ya tsaya kallon ta kafin ya ce
"Morning"daga haka suka kama hanya babu uhm babu umumh haka suka cigaba da takawa har suka iso inda zasu sami abin hawa suka shiga ya masu kwatancen inda zasu sauka ba wata doguwar tafiya suka yi ba suka iso inda zaau sauka dama mai gari ya aika a sanar da su cewa ga bokayen turai nan tafe su haÉ—u a inda suka saba haÉ—uwa dan haka a cike suka tarar da wurin.

A hankali suka taka zuwa gare su sai hayaniya ake ta yi dan ganin mace tare da tsohuwar fuskar da suka saba gani murna sosai matan suka yi dan akwai matsaloli da dama da suke son a magance masu amma rashin ƴar uwar su mace yasa ba su son sanar da Dr Zaid Maher gashi su ba wani ƙarfi ne da su ba bare su rinƙa zuwa asibitin cikin gari wahala suke sha sosai dan sai sun yi dakon mazajen ke samin abin masarufi matan kuma sune sai da kayan gida dangin su waran fulani, barkono, kindirmo da dai sauran su dan haka kullum akan sana'ar abin da zasu rufawa kansu asiri suke dan haka cuta na cin su amma da ya fara sai dai a yi na gida ya lafa da zarar ya tashi a kuma banka concoction a lafar da rashin lafiyar,ƴaƴan su babu makarantar boko ba wai dan basu da burin saka ƴaƴan ba sai dan basu da hali toh mutanin da lafiya ma bai gimshe su ba ina wani karatun boko ga matsalolin mata da ke ɗawainiya da matan yankin amma babu wasu ƙwararru sai na gargajiya

Toh a wata tafiyar da Dr Zaid Maher yayi ne zuwa garin Adamawan ɗaurin auren wani abokin aikin su wanda ya zaƙulo matar sa daga cikin garin dan ko da yake ba su labarin inda ya samo ta mamaki suka ji ba kaɗan ba sai da ya masu bayanin kirki da dattako irin na ƴan garin wanda shi ɗin ganau ne ba jiyau ba shi yasa ya ga match ɗin sa a nan she was just 16 years da ya aure ta ya ce da su zai saka ta a makaranta a kan rainon shi zata taso wanda hakan ya ja ra'ayin Dr Zaid har ya yi takakkiya zuwa garin _koma_ a nan ko ya shaida dan tun daga gidan mai gari ya ga kara da martabawa har dai ya ci karo da sanyin idaniyar sa kamar yadda ya laƙaba mata dan haɗuwar su ta farko kare shi ta yi daga ƴan iskan gari da suka kawo mai hari a hanyar sa ta komawa masaukin sa kasancewar ta budurwar mudan ɗan gayu sai suka rabu da shi da ta ce masu tare suke kuma duk wanda yake cikin ƙauyen _koma_ ya san labarin ta da mudan kuma kowa ya san mudan babu kirki dan akan budurwar sa yana iya shukawa mutum rashin mutunci duk kusancin ku kuwa,

Tun daga lokacin ya tambayi gidan su ta mai kwatance har dai ya kai mata ziyara kafin ya bar garin wanda sai da ya bar garin ya fara zargin kamar a kwai shaƙuwa mai girma a tsakanin su sai dai bai yi concluding ba outreach ɗin shi huɗu a garin kuma ko wanne a gidan su ake masa masauki wanda hakan ya kuma janyo kusanci tsakanin shi da sanyin idaniyar sa sai dai still bai sanar da ita abin da yake ji game da ita ba though bai gama yarda ba kuma bai jin giyar son na fixgar sa ko me yasa ohon mai,toh a wannan tafiyar ne ya yanke hukuncin gaya mata not knowing she have a man da take mugu mugun so da ji da shi.

Toh ko a tafiyar da ya so su yi a daren jiya da baby doctor gidan su sanyin idaniyar sa ya so su tafi dan hankalin shi ya fi kwabciya a chan amma kuma alfarma da mai gari ya nema a wun shi a daren jiyan ya sa ya ji wani iri ya amince akan zasu zauna a nan but da sharaɗin zai rinƙa tafiya chan gefen da ya fi wayo. ko da ya koma ɗakin sa ya fi dangana laifin da baby doctor ya yi fushin ita ce ta hana sa zuwa gidan da ya saba zuwa but babu komai ita ta jiyo dan shi chan zai rinƙa wuni in ta gan ta zaume ita kaɗai ta yi bayani ai,sai ka ce wani abin ya ke mata dama chan..

"Sannun ku da zuwa bokayen turai muna maku barka lale lalen ku"da murna suka masu sannu da zuwa suma suka gaida su inda suka natsu dan jin da me suka zo

"Ni sunana Dr Bilkisu Muhammad kuma ni ce sabuwar fuskar da ta zo tare da likitan ku da kuka saba zuwa ni maɗin likita ce zan mayar da hankali da kuma aiki na a fannin mata shi kuma zai yi fannin maza da fatan zaku bada haɗin kai"?jin daɗin su ya kasa ɓoyuwa har sai da suka nuna dan kamar haske ne ya bayyana a birnin rayuwar su ganin likita mace.

"InshaAllah likita zamu baki haÉ—in kanmu"first impression last long dan haka ta yi murnar haÉ—in kan da suka bata dan haka ta kalle shi ta ce mai
Chapter 11 · 0% Book details