← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 157

Sashe 60

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Share hawayen ta tayi tana saka murmushin dole ra ce
"Babu"sai ya juyar da idanun sa alamun bai yarda ba sai ta É—an yi dariya dan dai kar ya mata tambayar sai ta mai bayanin dalilin ta yin kuka,saidai da yake shi É—in É—an boko ne bai bata opportunity na gujewa wayon da take son yi mai ba,kuma yi mata magana yayi ya ce
  "Ban yarda ba ki gaya min dalilin ki na kuka"!a hankali ya mata maganar sai taji tsigar jikin ta ya tashi at the same time ta ji kamar sanyi sanyi na shigar ta hakan ya bada gudunmawar ƙin ba shi amsar tambayar sa dan haka ta shiga rera kuka ba ji ba gani shi kuma sai ya ruɗe gashi kan sa na banging kamar me sai ya shiga bata haƙuri
"Am sorry ban san tambayar tawa zata ɓata miki rai ba ki daina kukan"sai ta ji wani iri mijin ta na bata haƙuri akan laifin da bai sani ba sai tayi saurin ce mai
"A'a Zaid ni ya kamata in baka haƙuri dan ni na maka laifi,tambaya ta kayi na ƙi baka amsar tambayar na shiga yin kuka am very sorry am so sorry please forgive me"ta haɗe tafukan hannayen ta wu ɗaya ta shiga ba sa haƙuri tana zubda ƙwalla.  
 
  She is acting strange but why?ya ma kansa tambayar dan sarai ya san halin ta ba mai saurin karaya bane amma me ya sa take kuka haka dan ya tambaye ta kuma sai ta ƙara yawan kukan nata abin ya ɗaure masa kai sai dai bai ce komai ba dan baya son tursasa ta akan lallai lallai sai ta mai bayanin dalilin kukan ta zai bar ta har sai ta ji kan ta daidai kafin ya tambaye ta,ga tambayoyi da yawa da yake son yi mata sai dai bai san ya zata ɗau tambayoyin ba wannan ɗaya kenan amma ta shiga yin kuka.
  Shiru yayi yana kallon ta tana kukan har dai ta tsagaita ta kalle sa tana jimamin lamarin ko in ta mai bayanin dalilin kukan ta zai kalli bayanin da fuskar fahimta kokuma zai ƙi amincewa Allah ne masani
  Ta san yana da tambayoyi da yawa da yake son yi mata dangane da zuwan su nan,wani wuri ne nan ɗin,a wace ƙasa suke,me ya same sa,ina family ɗin sa and she knows maybe a ƙarshe yayi tambayar ina....a zafaffe ta ce
"No way"bata san ta furta shi a zahiri ba har ma ya isa kunnen Zaid sai ya kalle ta da kyau yana mamakin halin da take demonstrating dan bai san ta da wannan halin ba me kuma ya dame ta har take magana ba tare da ta san ta furta ba??
  Dawowa hayyacin ta tayi sai ta ji kunya ta kama ta bayan ta san a zahiri ta yi maganar da ta yi a haka ta warawre gyalen ta ta ja ta rufe har dai idanun ta suka ɓuya ƙarƙashin mayafin.
Shi dai kallon mamaki yake mata ya kasa furta komai dan abin nata ya fara zarce tunanin sa why is she covering her face?ya tambayi kan sa. 

  Zaune suke babu wanda ya kuma furta komai har tsayin lokaci sai ta yanke kawai is better ta sanar da shi a wuce wurin dan haka ta yi ƙarfin halin riƙe hawayen ta ta gyara murya
"Zaid"bai ce komai basai idanun sa da ya zuba mata sai dai ta daure bata cire nata idanun daga cikin nasa ba

"Abin da ya faru da mu ba yin mu bane haka zalika ba wai mun fi ƙarfin faɗawa a ƙaddarar ubangiji bane..sai ta ja fasali kafin ta ɗora da,satin ka kusan huɗu kana unconscious sakamakon abin da ya faru da mu a ƙauyen koma ban sani ba ko ka tuna da abin da ya farun but bana fatar ka tuna dan ba abu mai daɗin ji bane ina so ka sani ba da gangar na bari aka kai maka harin da ya illata ka ba kuma ina so ka sani am always ever ready dan kare ka daga wani harm ba'a fata but i promise never to let any harm come your way again,,,a last two weeks aka maka cerebral surgery wannan shine dalilin saka maka ear device da aka yi saboda accident da ka samu ba a iya cerebral region ɗin ka ya tsaya ba yayi affecting maka pineal gland wanda ya tilastawa kunnuwan ka amfani da device ɗin nan dan taimaka maka wun rage shigar sharp and lousy noises amma doctor ya sanar da mu cewa akwai tsawon period da amfanin shi zai yi elapsing sai a cire maka and you will be back to normal but before then please kar ka sakawa kanka damuwa da yawa in ka ga ba zaka iya ɗaukar damuwar kai kaɗai ba ka yi sharing da ni am at stand by now and always kuma dama doctor ya ce ba nan kusa zaka farfaɗo ba sai ka kai 3-4months but ikon Allah sai ka farfaɗo in less than 2weeks ka ga kenan tunda har ka iya farkawa kafin expected time wannan ear device ɗin ma ana iya cire sa kafin lokacin da suka ƙiyasta ka ga ba sai ka shiga damuwa ba dan am here and our parents are also here to help us da fatan ka fahimce ni and please don't react i know you will get well soon and all these minor pains will be done and over with just trust me"!!ba ƙaramin dauriya tayi ba a yayin da take sanar da shi dan kuka ne ke ta son taso mata ta sani it won't sound superb a kunnen sa dan ba abu mai daɗin ji bane a ce da kai ga abubuwan da suka same ka kuma yet baka gama warkewa ba especially ga wanda shine ya saba sanar da wasu sai a ce yau ana sanar da shi abin babu sauƙi definitely ta san he will be hurt amma gwara da ta sanar da shi tun yanzu dan bata san me zai faru ba in aka ɓoye mai asalin abin zai iya jin zafi in aka jinkirta sanar da shi but yanzu ta san ta sauke wani ɓarayi na nauyin da ke damin ta a zuciyar sa but inda gizo ke saƙar shine ta yaya zata sanar da shi matsayin ta a gare sa as his wife will he wacce or reject her bata sani ba kuma bata san lokacin sanar da shi ba har da ma dai tana tunanin by now either Bahajjatu,Hakim or Ammi must have inform him but a yadda yake yi sai take gani kamar bai da masaniya.

Ko da ya gama jin jawabin ta sai ya tsinci kan sa da son sanin cikakken labarin dan ya san ba duka labarin ta ba sa ba saboda je can sense phobia da ke damin ta dan har a muryar ta hakan ya nuna,he barley remember what happened that night but ya san ko ma dai menene it must be awful and ugly dan tsoro ne taf a tattare da ita sai ya yi interrupting tunanin da take yi ta hanyar kiran ta
  "Bilkisu ba duka labarin ba kenan,ina son sanin cikakken labarin"!!dumm ta ji gaban ta ya faɗi dama zagaye ta mai dan ta tsani ta kai kan gaɓar labarin inda Asma'u came to play dan sam bata so ya tuna da yarinyar saboda ba ƙaramar hatred take da shi ma yarinyar ba and she thinks bayan hatred akwai wani abin da take ji game da yarinyar wanda bata san ko menene ba.

 
  sauke idanun ta tayi ƙasa dan tsakani da Allah sai dai yayi fushi da ita amma ba zata taɓa gaya mai gaskiya ba..
  "Ka ga Zaid ka daina sakawa kan ka damuwa saboda wannan labarin da na baka iyakar ta kenan babu wata believe me"tana gama faɗa ta tashi ta yi hanyar waje tana jin sa yana kiran ta amma ta ƙi dawowa dan bata shirya sanar da shi ainihin labarin ba sai dai peripheral ɗin. 
  Da kuka ta ƙarasa ɗakin ta kuka mai tattare da cin rai take yi dan pains da agony da ke zuciyar ta bata iya riƙewa kanta ita kaɗai gashi bata so ya san abin da ke damin ta dan kar ya gane cewa maganar da ta sanar da shi ba cikakkiya bace.
  Tana tsaka da kukan ne ta ji ƙarar wayar ta sai ta yi kamar ta share amma wata zuciyar na bata ta ɗau kiran sai ta kai duban ta ga wayar cikin saurumi ta ɗaga kiran ta kara wayar a kunnen ta tana mai sakin wani kukan
  "Yaya Zaid zai fasa min zuciya ta da son sanin abin da ni kaina nake kan binnewa tun kafin yanzu,sai tambayoyi yake min i can't withstand it na gaji please yaya help me am too young for all these problems"ta fashe da kuka mai tafe da shesheƙa sai yayan nata da ya kira dan yi mata congrats saboda jiya wayar ta a kashe take kowa ya kira sai a ji wayar a kashe toh yana gwadawa ya ji ya shiga sai ya saka a speaker dan tare da Bilal,Lukman da Zainab matar Jamil ɗin suke da fari ma video call yaso yi sai dai ya chanza ra'ayi ya kira kawai,jin abin da ta furta sai yayi saurin cire wayar a hands free ya tashi daga inda yake zaune yayi isolating kan sa a waje ta gefen pool side cikin natsuwa ya kira sunan ta
Chapter 60 · 0% Book details