← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 157

Sashe 57

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sharewa tayi ta yi kamar zata fita sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon jin numfashin mutum kamar yana gasping sai ta juya a rikice tana baza idanun ta dan ganin daga inda numfashin ke fitowa bata san lokacin da ta dira a gaban sa ba sakamakon ganin ɓarin flower verse a gefen gadon sa,saurin yaye comforter ta yi hannun ta na ɓari tana gama yaye comforter ɗin sai ta ga shi ke numfashin kuma taimakon gaggawa yake buƙata dan haka ta fita cikin gaggawa bata tsaya ko ina ba sai a ofishin likita da ƙarfin ta ta shiga office ɗin tana ta kwala mai kira a rikice ya fito daga cikin bathroom da shigar sa kenan yana tambayar ta ko lafiya ta rasa me zata sanar da shi sai kawai ta shiga kirawo mai room number tana faɗin
  "405...405..405."ganin ta ruɗe sai ya ce da ita
"Is okey let's go"da gudun ta ta fita shima ya biyo ta suka ranƙaya zuwa ɗakin da shigan su ya riga ta zuwa kan gadon.ganin Zaid yayi yana jacking yana gasping da sauri da sauri sai ya cire mai mask ɗin ya yi regulating device da zai rinƙa bashi iska,fita yayi cikin hanzari ya nufi office ɗin sa babu jimawa ya dawo shi da wasu doctors biyu a nan ne aka buƙaci baby doctor da ta fita girgiza masu kai ta shiga yi tana kuka tana faɗin ba zata iya fita ba,hayaniyar da ke fitowa daga ɗakin ne ya janyo hankalin Hajiya Madina da Hajiya Zeenat da ke kwance a ɗakin masu kula da majinyata fita suka yi gabaɗayan su zuwa hanyar da hayaniyar ke fitowa,ko da suka tafi sai suka ga abin tashin hankali wato Bilkisu ce ke faman risgar kuka while ga doctors nan uku a ɗakin da Zaid yake kamar dai so suke su yi stabilizing nasa sai Hajiya Madina ta ɗan janyo Bilkisu tana tambayar ta me ya faru.
In banda kuka babu abin da take yi hakan ya sa Hajiya Madina jan ta suka bar wurin a inda Hajiya Zeenat ta tsaya tana hango abin da ke gudana a ɗakin duk hankalin ta a tashe yake ko me ya sami Zaid ɗin sai Allah dan haka zirga zirga ta shiga yi a bakin ƙofar Hajiya Madina dai bata dawo ba dan bata jin zata iya cigaba da witnessing abin da ke faru sai ta tsaya tana rarrashin Bilkisu kawai.

  An hour + kafin doctors ɗin su sami damar saisaita Zaid dan sun fahimci cewa ya farfaɗo ne kuma da ƙarfin sa ya farfaɗo dan kuwa so yake ya farka gabaɗay sai dai ciwon da ke kansa wanda ya janyo masa surgery bai warke ba dan haka dole komai sai a hankali zai saba da shi they were able to seduce him dan ya koma bacci kuma he is calm shi yasa suka fito a nan Hajiya Zeenat ta tare su tana tambayar su ko me ya faru shi babban likitan ne ya yi inviting ɗin ta zuwa office ta bi sa cikin hanzari.bayan sun zazzauna ne ya kalle ta at first moon face ya saka sai daga baya ya murmusa da smiling face ɗin ya ce da ita 
  "I must say,congratulations your son just regain consciousness and he is in good state of mind he will wake up in not less than an hour or more with full strength and ability what a surprise i guess"!!faɗaɗa murmushin sa yayi yayin da Hajiya Zeenat ta tafi ƙasa tayi sujjada bata ce da likitan komai ba sai da ta ɗago sannan ta kalle sa fuskar ta jiƙe da hawaye idanun ta sun yi ja ja zir tana dariya tana fidda hawaye ta ce da shi
"Thank you,thank you doctor,thank you"!!shima murmushin ya mayar mata da shi yana girgiza mata kai ya san tana cikin farinciki dan haka bai ga laifin ta ba dan ta zage tuƙuru tana kuka.daga office ɗin ɗakin zaman su ta nufa inda ta ga Hajiya Madina na rungume da Bilkisu tana rarrashin ta ita kanta mai rarrashin ta take nema dan haka ta ƙarasa shiga ɗakin ta ce cikin muryar kuka
  "Hajiya tashi ki ma Allah godiya our Zaid is back"ba ita kaɗai ba hatta da Bilkisun sai da ta razana dan maganar a matsayin abin almara ya zo masu da mamaki da al'ajabi sai suka tashi tsaye baki ɗayan su hawayen Bilkisu ya ƙafe yayin da Hajiya Zeenat ta buɗe baki cikin mamaki tana son yin magana amma ta kasa Hajiya Zeenat ta gane state of shock da ta shiga dan haka ta matso kusa da ita ta riƙe kafaɗun ta ta shiga girgiza ta tana cewa
  "Yes yess Hajiya Zaid is back for good yanzu na fito daga ofishin Dr kuma ya sanar da ni cewa Zaid ya farfaɗo kuma any moment from now yana iya farfaɗowa cikin ƙoshin lafiya abin godiya ne ga Ubangiji"!!sai ga hawaye sharr na fitowa daga idanun Hajiya Madina cikin farinciki da jin daɗi ta rungume Hajiya Zeenat ta saki kukan farinciki petting bayan ta Hajiya Zeenat ta shiga yi tana ƙara tabbatar mata da cewa eh Zaid ya dawo masu irin farinciki da suka tsinci kan su a ciki understatement ne sun manta da Bilkisu a ɗakin wacce ta yi suman tsaye sakamakon jin an ce Zaid ya farka a nan ta bar su ita kuma ta nufi hanyar ɗakin da Zaid yake.
   An saka dokar kar wanda ya shiga ɗakin har sai ya farka amma ita kam kai tsaye ta shige ta rinƙa bin sa da kallo tana jin wani abu a ran ta game da farfaɗowar Zaid a haka ta zauna gwiwa a sage ta kafa mai dara daran idanun ta waɗanda suka chanza launi zuwa jajjaye saboda kukan da ta yi saƙe saƙe kala kala take yi a zuciyar ta mafi akasarin saƙe saƙen sun ta'alaƙa ne ga mafitar rayuwar ta in Zaid ya farfaɗo ya kuma gane cewa shi da ita sun zama ma'aurata wanɗanda zasu rinƙa zama inuwa ɗaya tun farfaɗowat sa har izuwa ƙarshen rayuwar su ya zai karɓi maganar?shin da wani siga zai fahimci maganar?zai amince da ita kokuma a'a?zai ma yarda ya ɗauke ta a matsayin abokiyar rayuwa ta har abada?waɗannan tanbayoyi sun tsaya mata a rai she knows that tomorrow will be her wedding day ranar da ba zata taɓa mantawa da shi ba a rayuwar ta saboda tambari ne that will signifies a new life,a new beginning and a new world to her.but is she well prepared and ready to accept it?sai ta kuma kallo sa ta ga yadda yake fidda numfashi a hankali har yanzu bata san me take ji game da shi ba it's somehow mix the chemistry is over reactive reaction ɗin na boiling ko wani ɓangare da saƙo na jikin ta,kanta ne ya fara ɗebar chaji sai ta tsagaita da tunane tunanen ta cigaba da kallon sa.

  _1:00am_
  Suna a haka shi yana baccin sa ita kuma ta kasa runtsawa tana ta bin sa da kallo already nervousness ya gama yi mata dabaibayi ya hana ta sukuni,tana kan kallon nasa sai ta ga ya fara juyawa da kansa idanun sa a rufe ruf sai ta tashi ta matso kusa da shi tana gyara mai abin numfashin da aka saka mai ɗazu sai ya dakata daga juyawar da yake yi ya tsaya da kan sa a wu ɗaya itama sai ta natsu kamar mai son haddace wani abu kusan 5 minutes bai motsa ba sai ta ji ran ta ya fara mata ɗaci ɗaci ta ji ɗakin ya mata wani iri dan ta gama sadaukarwa ba gaske bane kawai yaudarar ta idanun ta ke yi sai ta haƙura ta koma kan kujerar ta kafe sa da idanun ta wanda zuwa yanzu sun ƙara girma sakamakon takura da suka samu daga gare ta dan kuka ne ba kaɗan ba tayi ɗazu ga rashin baccin da bata yi ba ga tunani duk sai suka taru suka haddasa mata damuwa dan har barkono barkono idanun ta ke mata amma bata cire tsammanin sake haɗa kwayar idanun ta da Zaid ba.
 
  Gradually,synchronously ya buɗe idanun sa kaɗan sai ya maida ya rufe duk bata lura ba sai da ya kuma buɗe su a karo na biyu ya sauke su kanta duk bata sani ba sai da ta ji a jikin ta kamar mutum ya kafe ta da idanu sai ta yi wuf ta ɗago with the hope of seeing him fully awake,.
  Gani tayi kamar idanun ta gizo yake mata ɗan murza su tayi ta tsaya sai ta ga still ita yake kallo abin bai mata ba sai ta rufe idanun ta for a moment ta buɗe su taga ita ce dai yake kallo dan haka sai ta shiga pinching hannun ta but the reality is well set shi ɗin ne dai ba mafarki ba ba kuma imagination ba sai a hankali kamar mai sanɗa ta fara takawa kaɗan kaɗan tana kallon fuskar sa sai ya bita da idon ta kuma dawowa ta gaban sa still ya bita da kallo sai ta dawo gaban sa ta tsaya shima idanun sa suka tsaya a kan ta ya tsura mata idanu kamar bai taɓa ganin ta ba.
  She was out of words sai kawai ta juya cikin hanzari ta fita ta nufi ɗakin iyayen nasu ta gan su zaune dan tun da ta bar ɗakin suka neme ta suka rasa sai Hajiya Madina ta fita duba ta ganin ta a ɗakin Zaid ya sa ta girgiza kai ta dawo ta sanar da aminiyar ta abin da ta gani sai suka zauna zaman jiran farfaɗowar sa basu koma baccin ba.
  Da shigar ta cikin extreme euphoria ta ce
  "Umma Zaid..Zaid ya tashi..wallahi ya tashi baya baccin..idanun sa a buɗe suke zo muje ki gani"tausayi ta bama iyayen nasu dan sun gano mummunar son Zaid ya gama kamata har yana shirin illata ta ba tare da ta sani ba.
Sai da ta ja hannun Umman sannan suka biyo ta zuwa É—akin Zaid É—in suna fatar ganin abin da Bilkisu ta faÉ—a.
Chapter 57 · 0% Book details