← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 157

Sashe 152

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin ta na daÉ—a girma yayin da suke shirin dawowa gida Nigeria wanda yayi daidai da bikin su Baha,kenan saura 2weeks..
Washegari zasu bar ƙasar dan haka all night suka yi sai da ya saukar mata da gajiya sosai dan ya san in suka koma babu shi babu samin kan ta dan bikin aminiyar ta zata mayar da hankali akai..
A gajiye suka yi baccin har wayewar gari da suka isa filin jirgi gabaÉ—aya a gajiye suke,jirgi na tashi suka shiga yin baccin gajiya...

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

👄 °°° °°°👄
°°
°

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

_This page is for u my chubby Fatima Tijjani{Fati-Teejay}💋_

*44*

*_EDD Phobia_*

_Abuja Nigeria_
_9:55pm_

Dai dai wannan lokacin suka sauko daga jirgin yayin da Lukman ya buɗe masu mota dan tun ɗazu ya iso filin jirgin yana jiran isowar su,duk a jigace suke bacci kawai suke buƙata dan haka cikin sauri Lukman ya taya su kwashe kayan su yana mai taya su murnar dawowa,saka kayayyakin yayi cikin motar su kuma suka shiga ya ja su suka wuce gidan su tun a motar take jin bacci bacci..
Mai gadin gidan ne ya taimaki Lukman suka shigar da kayan ciki lokacin har 10 ya wuce dan haka sallamar su yayi yana masu fatar hutawa lafiya..

Wanka da sallah suka yi abincin ma kasa ci ita dai tayi dan tun a motar ta ci abinci shine ma ya ƙoƙarta ya ɗan taɓa abincin sannan ya zo yayi joining nata a gadon wanda ita tuntuni ta daɗe da yin bacci kuma bai takura mata ba dan ya san wahalar da ya bata a jiyan nan ko kusa wasu matan ba su iya ɗaukar wahalar,godiyar sa ɗaya ciki ne da ita kuma dama wasu masu cikin yawan buƙata ne da su kuma ta faɗa a cikin jerin mata masu ciki dake tattare da irin wannan symptoms ɗin hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yake saka shi ji ba dan bata taɓa gudun sa ko buƙatar sa she is always at the peak kuma tana welcoming nasa a duk lokacin da ya iso ta da buƙatar sa..

°°°°°°°°°°°°°°°°°
_Next morning_
Tun wuraren ƙarfe tara na safe aka fara zuwar masu barka da dawowa saboda lokacin bikin ba wani shagali aka yi ba bayan bikin kuma suna asibiti da suka dawo gida kuma duk basu wani zauna ba suka wuce honeymoon,toh shine ƴan uwa da abokan arziƙi suka zo yi masu barka da dawowa haɗe da murnar biki da ƙaruwar da suka samu dan izuwa yanzu cikin Bilkisu ya fito is very visible dan komai na siffar masu ciki ya bayyana a jikin ta ga yadda cikin ya ɗan yi protruding kaɗan sakamakon shigar sa early second trimester..

Hidima sosai suka rinƙa yi da jama'a wasu na zuwa wasu na tafiya hatta da abokanan aikin su duk sun zo taya su murnar bikin su da samin lafiyar Zaid ɗin kaf family ɗin su Zaid babu wanda bai zo ba dan har ɗan ƙwaryaƙwaryar shagali aka haɗa masu wanda ya ƙayatar da taron dan wuraren ƙarfe biyar ne aka fara taron taya murnar dawowa su da samin lafiyar Zaid ga daɗin abin farinciki ƙaruwar da Allah ya ba Dr Zaid da matar sa..

Sai chan cikin dare wuraren ƙarfe goma shaɗaya suka sami sa'ida dan an gama tafiya har an gyare gidan tsaf kamar ba'a yi komai ba..
Wanka suka yi tsaf suka dawo makwancin su suka kwanta bacci take ji sosai sai dai har baccin ya fara ɗaukar ta sai ta ji wani irin labari Zaid na laluɓar ta ai ba shiri ta tashi ran nan a haɗe ta haɗe girar sama da na ƙasa
"Ka san Allah ɗaya Zaid,in ka takura ni komawa gidan mu zan yi haba dan Allah baka gajiya abu ɗaya ɗaya ɗaya kamar numfashin ka wallahi tallahi ka kuma takura ni hero tafiya ta zan yi in bar ka haba sam baka gaji ba ga sha'anin nan da aka yi na yau ga gajiyar jiya ga na shekaranjiya duk ni kaɗai amma wai baka tausaya min ba ga ciki haba Zaid please stop being selfish for crying out loud"...ran ta ɓace tayi maganar sai ya sake baki yana kallon yadda take sauke mai kwandon bala'in ta da ta daɗe bata yi shi ba dan haka ya shafa ma kan sa lafiya ya janyo ta jiki sa yana faɗin
"Am sorry babes zo mu kwanta toh in maki massage"ran nan a haɗe ta kwanta ya shiga matsa mata ƙafa har bacxi yayi awon gaba da ita dan gani take in ba taka mai birki tayi ba toh sai ya ɓarar mata da ciki sannan ita kan ta ya lahanta ta dan sam Zaid baya wasa da zancen buƙatar sa...

Da ƙyar da ƙyar yayi baccin azaba dan wani irin buƙatuwa ne ya rinƙa taso masa kewar ta yake ji kamar me amma ganin yadda ta ɓata fuska ɗazu da masifar da ta mai sai ya rungumi haƙuri ya tursasawa kan sa baccin dole...
Da asubahin washegari ta riga sa tashi dan bai yi bacci da wuri ba,kallon fuskar sa tayi sai ta ji tana jin tausayin sa tana blaming nasa akan ya cika jaraba da buƙata da yawa amma bai kamaci hakan ba dan kuwa bai kasance mazinaci ba bai taɓa sanin mace ba sai a kan ta dan yayi zumuɗin ta bai kamata ta bijire mai ba,kai duban ta tayi ƙasa sai ta ga morning glory ɗin sa wato morning erection ɗin sa girgiza kai tayi ta kai hannun ta ta ɗora bisa erection ɗin sai ta ga ya ƙara length wato har a cikin baccin Zaid jarababben maitar sa na nan kenan,,cire hannun ta tayi ta dawo da kan ta kusa da nasa ta haɗe wu guda sai ta haɗe lips ɗin su wuri ɗaya ta kai mai kiss a hankali..
Cikin baccin sa ya ji saukar lips ɗin ta saman nasa lips ɗin sai ya ƙara tamke idanun sa yana jiran cigaban abin amma ya ji shiru dan haka ya yunƙura ya buɗe idanun sa sai suka sarƙe cikin na juna..
"Goodmorning hero"da É—an fara'ar sa ya amsa da
"Morning heroin"sai ta ce
"Heroin"?gyaÉ—a mata kai yayi yana faÉ—in
"Ko sunan bai maki ba ne"?da murmushin ta ta ce
"Of course no,sunan ya min daÉ—i sosai hero"..
Murmushi yayi kafin ya ce da ita
"Lokacin sallah yayi ne"?gyaÉ—a mai kai tayi sai ya rungumo ta suka sauko tare suka nufi hamyar toilet inda suka yi alwala tare suka fito shi ya chanza zuwa jallabiya ya nufi masallaci ita kuma ta saka doguwar riga ta tayar da nata sallar..
Addu'oi sosai ta masu ita da mijin ta ta É—ora da addu'ar da ya zame mata jiki zuwa yanzu wato addu'ar yayewar kishin tsiyar da take da shi dan a tsarin Zaid É—in sati na biyu da dawowar su zasu tafi Yola kafin bikin su Bahajjatu da na Afzal...
Chapter 152 · 0% Book details