← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 157

Sashe 59

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

A halin ɓoye ɓoyen ta kai har dare sai dai tana muradin ganin sa but she can't she feel she can't see him at that moment dole ta bari har sai sun tafi.a haka ta kwana ta tashi ba tare da ta saka sa a idanun ta ba,da yake jirgin wuri zasu bi ita kuma tana bacci lokacin sai Ammi ta bar mata note suka yi tafiyar su

Ko da ta farka bata lura ba sai ta yi harkokin ta na yau da kullum but ta saka a ran ta cewa dole ne ta gan sa ko da kuwa suna nan dan ta gaji tun shekaranjiya rabon da ta saka sa a idanun ta.she dress in an alluring way shiga mai kyau tayi ta É—an yi makeup kaÉ—an ta saka flat Zara pams ta nufi É—akin sa dama bai da nisa da nata dan haka da zuwan ta shiga tayi kai tsaye ba tare da tunanin maybe iyayen nasu na ciki ba.
Zaune yake a kan gadon ana bashi abinci sai ta ƙarasa zuwa inda suke tana kallon mai bada abinci sai ta ga baturiyar mace ce sai ta mai da idanun ta kan sa ta ga yana kallon mai bashi abincin ai tuni ta ji ran ta ya ɓaci ta fara tunani marar kyau a kan mai bada abincin gashi ta ga dai matar yake kallo sai ta zuciya ta karɓe abincin daga hannun matar haɗe da saka fake grin ta ce da ita
"Thanks you may leave please"baturiyar sai ta maida mata da murmushin sannan ta fita.
Zama tayi a kujerar da ke kallon gadon sa ta shiga ƙoƙarin bashi abinci sai dai ya girgiza mata kai dan dama ɗazu da yake kallon matar nan nuna mata yake son yi akan ya ƙoshi sai dai ita bata gane ba.ita kuma Bilkisu ganin ya nuna alamar ya ƙoshi bayan ta ga yana ta karɓa a wun waccan baturiyar sai ta ji ran ta na suya dan haka cikin ɓacin rai ta ajiye abinci ta tashi da nufin fita ta bar mai ɗakin in yaso Ai ko Baha ko ma ita baturiyar su zo su basa since he doesn't need her help.
Ko da ta juya dan fita a zuciye sai ta ji deem voice na sa na kiran sunan ta
"Bilkisu come back"!!sai yayi shiru itakuma ta ƙame a tsayen bata juyo ba bata fita ba ta rasa me ke mata daɗi is it her name that he called?or the care he puts in while calling the name?ko dai kawai unique feelings ne?sai ta tsinci kan ta tana mai annashuwa haka kawai...

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

  *19*

   A hankali ta juya ta yi ƙasa da idanun ta ta shiga takawa a hankali har ta iso kusa da shi sai ta tsaya ba tare da ta ce da shi komai ba sai da ya kuma yin magana
"Bilkisu zauna"!!sai ta zaunan tana mai kallon ƙasa shi kuma ba hakan yake so ba so yake ta kalle sa dan ya mata tamnayar da yake da niyar yi sai dai sam ta ƙi yarda su haɗa idon sai da ya kuma furta wata maganar
  "Ki kalle ni mana"!!sai ta ji saukar maganar a tsakiyar kan ta itama bata san me yasa ta ke shakkar haɗa ido da shi ba ita da ta daɗe tana muradin ganin farfaɗowar sa dan dai ta haɗa ido da shi sai gashi yanzu da ya farfaɗon ta kasa kallon sa cikin ido.
  Bai san menene dalilin ta na ƙin son kallon sa ba sai ya mata shiru ba tare da ya kuma ce mata komai ba har sai da dan kanta ta ɗago a hankali ta sauke idanun ta a kan fuskar sa tana son haɗa courage ɗin magana da shi,dama ya juyar da kan sa gefe sai ya ganta ta gefen ido sai da ya ja lokaci sannan ya juyo ya zuba mata deem eyes ɗin sa da har yanzu basu gama dawowa normal ba sakamakon jinyar da yayi.

  Sarƙewa idanun su yayi a na juna,doguwar lokaci suka ɗauka suna kallon juna wanda kallon nasu cike yake da ma'anoni kala daban daban wanda su kaɗai suka san ma'anar sa sun daɗe a haka shi bai cire idanun sa ba ita ma bata cire ba dan kasa cirewar tayi ta rasa dalili.
  Ba su suka daina kallon juna ba har sai da aka turo ƙofar ɗakin aka shigo haɗe da faɗin
  "Good morning"da fara'a a kan fuskar wanda ya shigo,ita ta riga sa ɗaga kai ta kai duban ta ga wanda ya shigon sai ta ga Dr ne dan haka ta tashi tana tambayar sa
"Morning anything"??amsa mata yayi da
"Yeah i want to check his system to assess his body function"sai ta girgiza kai cikin gamsuwa ta matsa mai ya matso kusa da shi yana gaida sa haÉ—e da tambayar sa ko da akwai wani abin da ke damin sa amsa ya basa da a'a illah son sanin blockage da ke kunnen sa a nan doctorn ya rasa abin faÉ—a mai dan bai shirya wa tambayar tasa ba kuma dama shi dai duba sa ya zo yi ba wai shine main doctorn Zaid É—in ba.
Sai ta ba Zaid amsa ta hanyar amfani da yaren hausa ta ce da shi
  "Zan faɗa maka dan ba shine ainihin likitan ka ba zuwa yayi duba ka in ya tafi zan maka bayani"!sai ya tsura mata ido hakan kuma creating mat wani abu yake yi wanda bata iya withstanding sai ta kawar da idanun ta ta mayar ga likitan
  "Is okey i will explain to him"jijjiga kai yayi ya cigaba da dube duben sa kafi daga bisani ya mai fatan ƙara samin lafiya ya fita ya bar ɗakin sai ta koma mazaunin ta ta zauna ta yi ƙoƙarin danne hawayen da ke cike a ƙwayar idanun ta sakamakon tunowa da tayi da matsalar da Zaid ya ke da shi wanda yayi necessitating masa zama da ear device ɗin for a long period of time ga final healing and recovering stage da ke jiran sa a nan gaba wanda alƙawari ne ta ɗaukar wa kanta babu yadda zata sanar da kowa ita kaɗai zata yi handling komai thank goodness yanzu ita ɗin matar sa ce so ko ma me ta yi ta san is for their own good.kallon sa tayi ta ga shima ita yake kallo sai ta ji ta kasa daurewa dan haka t bar hawayen suka zubo wanda ya saka sbi cikin duhu dan bai san ma'anar kukan nata ba sai ya ce da ita
  "Menene kike kuka"??muryar sa ƙara saukar mata da tausayin sa yayi sai ta rasa ta ina zata fara kamo zaren bayanin da take son yi mai a kan rashin lafiyar sa..
Chapter 59 · 0% Book details