← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 157

Sashe 82

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Da dariya ta ƙarasa shigewar ta ɗakin dan ta san ta ƙunna sa dan dolen sa ma ya ji a jikin sa saboda ta san yanayin maganar da ta mai sai ya ji wani abin all she need is for him to realise and keep her in his head kuma ba zata iya yin hakan ita kaɗai ba dole sai da sanin sa da kuma yardar sa..
   Kwantawa tayi bisa kan gadon ta tana jin wani sassanyar annashuwa na  shigar ta from no where,juyi tayi tana tuno wasu moments da suka yi tare da shi most especially jiya da ya nuna damuwar sa gare ta,tunowa tayi da lokacin da ya ruɗe a jiyan yana ta tambayar ta ko me ke damin ta sai ta tsinci kan ta da yiwa kanta dariya lallai ta shiga sabuwar duniyar da bata san da akwai shi ba a duniyar nan the feelings is extraordinary abin ya mata nauyi da yawa tana buƙatar mai taya ta riƙon abin da take ji a zuciyar ta..
 
  Tana duniyar tunanin ta ne ta ji an turo ƙofar ɗakin kamar ba'a son turowa hakan ya tabbatar mata da Zaid ne dan shi kaɗai ke tare da ita a gidan.
  Tashi tayi daga kwanciyar riginginen da tayi tana mai kallon sa da murmushin son da take mai shi ko shagala yayi yana kallon ta yana jin wani abu na fizgar sa sai dai yayi ƙoƙarin controlling kan sa dan yana ganin kamar yana overreacting da yawa.
  Gyaran murya yayi game da riƙe ƙofar ɗakin yana mai sauke mata idanun sa cikin wani salo hakan kuwa yayi tasiri a kan ta dan kallon yayi affecting nata sosai sai dai itama tayi controlling kanta dan so take ta gama tabbatarwa ko shima yana jin abin da take ji ko ita kaɗai ke jin abin..

"an kawo mana breakfast zaki yi joining É—i na ne a parlor ko in kawo maki nan"?cikin salon jan ra'ayin sa ta ce
  "Hmm Zaid kenan..,ai duk inda kake nan nake duk inda ka zaɓar min nan zan zauna"
  Ya ilahi,me yarinyar nan ke son yi mai ne haka shin?sam yakan kasa ganewa kan sa in har tana kusa da shi shi dai ya san abu ɗaya ne tak wanda ya san ko a baccin sa zai iya shaidar sa sai ya sami mai warware mai..

  Kallon kallo suka shiga musayar yi da juna kafin ya ce da ita
"Toh ki zo mu tafi parlor in yaso sai mu kalli theater show"tashi tayi da fara'ar ta ta ce
"Hakan ma yayi"!!ta rigasa fita falon shi kuma yana biye da ita a baya yana saƙe saƙe..

  Shi ya ɗauko plates biyu da spoons ya zo ya juye masu abincin cikin different plates ɗin sannan ya zuzzuba masu chill drink a tumbler,tana bin sa da kallo har ya kammala tana kallon sa bata ce da shi ƙala ba sai da ya kammala duka ya ɗago ba yabo ba fallasa ya ce
  "Bismillah"!!...wani irin kallon kashe jiki ta mai dan ƙanƙance idanun ta tayi tana mai kallon ƴan boko,shi kuma ya kasa furta komai sai bin ta da ido da yake yi kan sa duk ya ƙulle ya rasa dalilin ta na nuna mai wannan attitude ɗin.
  Bai gama tunanin nasa ba ya ji muryar ta kamar mai jin baccin tana faɗin.
"Bismillah??toh bismillah"ta faÉ—a cikin halin ko in kula haÉ—e da É—aukar spoon da side table knife tana kallon sa dan kamar statue ya koma a zaunen yana mamakin ta sam bai san ta shahara har haka ba sai yanzu.
  Alama ta mai da ido irin ina jiran ka ɗin nan dan kuwa babu alamar wasa a fuskar ta kenan bata ji daɗin yadda ya mata tayin abincin ba.
  Kallon ta yake kyar dan dai ya fara shiga duhu da ɗabi'un da tayi adopting tana displaying mai.
  Saka cokalin yayi cikin plate ya fara ɗibawa zai kai bakin sa sai ya ƙaƙare ya kasa sakawa ya tsaya kallon ta sakamakon ganin nata cokalin cikin plate ɗin abincin sa hankali kwance ta ɗibo sai ta dakata bata saka a bakin ta ba ta aika mai da wani kallon kashe jiki sannan cikin taushin murya ta ce
  "Bismillah"ai bai san lokacin da ya fara tari repeatedly babu tsagaitawa ba sai ta ɗan nuna alamun damuwa a kan fuskar ta sannan ta tashi cikin kula ta ɗauko mai ruwan sha dan organic drink ɗin na iya increasing mai rate na tarin bit water will be more suitable for him.
  Bashu ruwan tayi a baki ya ɗan yi sipping sannan ya ɗaga kan sa yana kallon ta,haɗa ido suka yi ta mai sannu da idon haɗe da gyaɗa mai kai irin it is well ɗin nan sai kawai ya sauke idon sa haɗe da furta
"Nagode"sai ta ce mai
"Ba komai ai aiki na ne"da murmushin ta ta faÉ—i hakan sannan ta dawo ta zauna ta É—ebi abincin ta kawo bakin sa haÉ—e da ce mai
"Haaa"sai ya kalle ta a kasale bai buɗe bakin ba har sai da ta mai alama da kai sannan ya buɗe bakin yana mai yin bismillah,saka mai cokalin abincin tayi a baki ya karɓa sai ta cire ta kuma ɗebo wani ta ƙara bashi ya karɓa,a taƙaice dai ita ta ciyar da shi har ya ƙoshi sannan ta ɗau nata plate ɗin ta saka same spoon da ta bashi abincin da shi ta ɗauka zata tashi dan komawa ɗakin ta cin abincin.
  Yana ganin haka kuwa ya kawo hannun sa ya riƙe nata hannun da take da nufin ɗaukar tumbler,dakatar da ita yayi yana mai cewa
  "Zauna mana ina kuma zaki tafi"??sai ta ji gaban ta ya ɗan faɗi dan riƙon da ya kawo mata ya shige ta ba kaɗan ba.
  Haɗa ido suka yi sai ta kawar da nata idon kamar marar gaskiya ta ce
"Dinner zan yi having"!!still yana kallon ta ya ce
"Wayo dai zaki min,kin gama bani na ci sannan ke ki ce guduwa zaki yi ki ci alone dan kar in ga menene"?dariyar mamakin sa tayi sannan ta ce
"Ban gane ba?abinci zan tafi in ci,,ina son shan magani kai ma ya kamata ka sha night medicine naka"sarai ya gane so take tayi dodging tambayar da ya mata dan haka shima sai yayi claiming ai bai ma san inda maganar tata ta dosa ba yayi pretending dan dolen ta ta dawo ta zauna ta ɗau cokalin zata fara ciyar da kanta sai ya riga ta riƙo cokalin,ta zuba mai idanun ta bata ce komai ba sai ta ga yana ƙoƙarin fara feeding nata abin ya ɗaure mata kai but bata dai ce komai ba.
  Sai da ya ɗibo iya bakin ta sannan ya ce da ita
"Haaa"kamar dai yada ta mai sai abin ya saka ta darawa wato shi ba'a mai bai rama ba..
  Share ta yayi dan shi dai duk abin da yake yi ji yake kamar ingiza sa ake yi yayi su dole dan haka baya jin wani damuwa ko da ta mai dariya in dai zai sami sauƙin damuwar da yake damin sa he is okey..
  Buɗe bakin tayi ya saka mata,a ƙalla sai da ta yi rabin plate ɗin nan sannan ta shiga girgiza mai kai alamun ta ƙoshi sai ya tambaye ta
"Are you sure"?ta kuma girgiza mai kai sai ya miƙo mata drink ta sha haɗe da karɓa daga hannun sa tana ce mai
"Thank you"ya ɗan murmusa sannan ya tashi ya kwashe kayan dama tana da niyar taya sa kwashen kayan amma ya ce ta bari ita da ba lafiya sai ta yi zaman ta haɗe da ƙunna plasma ta kamo tashar da ya kamo ranar da suka kalli theater da dare.
  Zama tayi haɗe da crossing ƙafafun ta tana ɗan kaɗa su a hankali ta natsu tana kallon yadda ake feɗe wata mace ana son cire mata fibroid mayomas,ta zurfafa a kallon har ya fito bata sani ba sai da ya zauna yana mai faɗin
  "Interesting"sai a nam ta kalle sa tana mai yin murmushi haɗe da gyaɗa mai kai,daga haka suka mayar da hankalin su kan kallon har aka gama sai dai ana gab da ƙarasa ɗinke feɗan suka shiga yiwa kan su tambayoyi a course of tambayar ne suka shiga arguing da juna har ma da abin ya masu sugar suka koma yin raffle draw sai da aka kammala show ɗin sannan suka natsu sai suka koma yiwa kan su dariyar shirmen da suka rinƙa yi,gaskiya ta ji daɗi abin nan dan ko ba komai yana copping da internal response nasa ta ji daɗi ba kaɗan ba..

  *3 hours later*

  Bayan sallar azahar ya shirya cikin ƙananan kayan shan iska ya duba ta a ɗakin ta dan yana son su ɗan zaga hotel ɗin tare since they have no where to go..
  Ganin ta yayi kwance babu doguwar rigar sai ƙananan kayan da ta saka a ciki,bacci take sosai hankali kwance sai ya mata kallon ƙurilla tun daga ƙasar ƙafar ta har ya kawo kan sumar kan ta yana kallon ta yana admiring jikin ta sai ya ji baya son takura ta sai kawai yayi tafiyar sa shi kaɗai ya zaga ilahirin hotel ɗin baki ɗaya yana zagawa yana tunanin ta har dai la'asar ta yi sannan ya dawo ya yi sallar sa ya kuma komawa ɗakin ya ga still baccin take sai yayi murmushi haɗe da girgiza kan sa irin wannan bacci nata haka ina zata kai sa..
Chapter 82 · 0% Book details