← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 157

Sashe 89

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana shigewa daidai lokacin da ta yi shutting door ɗin a lokacin ne kuma shutting ɗin ya sauka saman fuskar sa dan yana kawo kan sa tana shutting ƙofar cikin baƙin ciki da nadama.
Buga ƙofar ya shiga yi yana kiran ɗaya sunan ta since she prohibited him from calling her name,gabaɗaya ya rasa da wanne zai ji ciwon kan da yake fama da shi ko kuwa matsalar da ta saka su ciki shi ya ma ji damuwar ta shine matsalar sa amma ta hana sa kusantar ta..
"Baby talk to me common stop acting like a small kid for crying out loud ki fito ki faɗa min laifin da na maki please am begging you ki fito"!!da iya ƙarfin sa yake maganar amma ko ta san mutum na wurin ta mai banza ta cigaba da kukan ta har sai da ta ji ya kuma tambayar ta sannan ta ce mai cikin masifa
"Ka bar min ɗaki dan wallahi in ka bari na fito i promise to do something smelly that both of us will not appreciate"sai kuka dan ta kasa gane dalilin da ya sa ta kasa jin tsanar sa ko da na sili ɗaya ne a zuciyar ta tun ɗazu da yake mata maganganun nan madaɗin ta ji tsanar sa ta ji haushin sa sai ma ta ji kamar ƙarawa son sa fertilizer ake yi a zuciyar ta a ƴar tsakankanin nan sai kawai son sa yayi boosting a zuciyar ta ta ji kawai in har bata same sa ba toh banu wata macen da ta isa ta same sa.
Kuka take yi kamar zata ƙarar da hawayen ta dan azaba da cin rai sakamakon abin da ya mata bata san lokacin da ta fara fitar da kalaman ta waje ba tana cewa
"Me ya sa Zaid?me yasa zaka min haka?me na maka da zaka saka min da wannan abin?tsanar da ka min ya kai har haka dama ban sani ba?ya zaka kashe ni ka ɓoye wuƙar ba tare da tsoron ana iya kamaka ba?ya zaka min yankar baya Zaid"??kuka take mai tsanani dan tsakanin ta da Allah take kukan nan dan abin da ke cikin zuciyar ta take faɗi a bakin ta ta gama sakankancewa Zaid ya zama nata amma kawai a daren farkon su sai ya zo mata da wannan zancen ashe dama can da ya bar ta kallon ta kawai yake shi yana nan yana kan bincikar halin da yarinyar nan take har ma ya gama ƙiyasta tafiya zai yi wurin ta in sun koma wannan wani irin masifa ce..

Saka kunnen sa yayi ya natsu yana sauraron duk maganganun ta sai ya kasa bada meaning ma kalaman ta dan duka kamar open ended questions tame ta yi ma kanta bai gane inda maganganun nata suka dosa ba but sai ya tambaye ta
"Me na maki baby....please baby say it out....ki faÉ—a sai mu sami solution"...
Cak ta dakata daga kukan da take yi ta tashi tsaye cikin ƙunar rai ta buɗe lock ɗin bayin ta buɗe ƙofar cikin ɓacin rai ta tura ƙofar baya da ƙarfin ta sannan ta zubo mai *_raged_* eyes ɗin ta ta ce
"Me ka min ka ce?so kake ka san me ka min Zaid"??da ɓacin rai ta mai tambayar wanda ya kuma ƙulle masa kai kafin ya ce
"Yes..ina son sanin me na maki...why the sudden change...what happened"??a tsawace ta ce da shi
"That stupid indecent ingrate villager,that heartless girl Asma'u,the girl that almost caused your death your final abode is that same girl whom you called a saviour,innocent and responsible,har a gaba na Zaid kana kiran sunan yarinyar nan....ka san sau nawa ka kira sunan ta?ka kira sunan ta fiye da yadda zan iya ƙitgawa,,Zaid....my first nuptial night with you...ka rinƙa min maganar wannan ballagazar yarinyar har kake cewa ita ta fitar da mu daga cikin dajin nan???are you that low cheap to be after such undisciplined girls??ina matar ka a daren farkon mu ka zauna kana min zance wata yarinya,,yari yar da bata so ka kasance a raye ba,har kake cewa kana gudun kar ta auri ɗan iskan sauratin ta da suka gama lalacewar su tare"?cikin tsantsar ɓacin rai yayi interrupting nata
"Don't you ever call her with such names because she doesn't deserve them,how can you say that ita tayi causing min shiga halin da nake ciki na taɓa gaya maki cewa ba dan ita ba da an manta da labari na a doron ƙasar nan?iyee?na taɓa sanar da ke cewa she waz my first saviour?and i am still thinking that ita ta kuma saving namu daga hannun yaron nan? yari yar da tayi risking rayuwar ta dan taimaka mana sannan ki rasa da me zaki saka mata sai ƙazafi da awful words marasa daɗin ji how could you"!!??a tsawace ya ƙarasa maganar.
Kallon sa take yi kamar bata san sa ba sai kawai ta shiga tafa hannu tana dariyar da ta fi kuka ciwo a zuciya ta buɗe baki zata yi magana amma sai maganar ta gagare ta sai kawai ta shiga girgiza kai tana ƙare mai kallo tsabar mamakin sa da ya gama kama ta da ƙyar ta haɗa kalma taƙaitacciya ta faɗi
"Tell me something Zaid...,,fushi ka yi dan na faɗi gaskiya akan yarinyar nan?ka ji ran ka ya ɓaci ne dan na kira ta da sunayen nan?gaya min ina jin ka"??sai yayi mata shiru yana kallon ta dan bai san me ya sa ta zama so interested in the girl's affairs ba.
Muryar ta ya kuma ji cikin taushin murya kamar ma tsoraciya idanun nan ta ƙara girman su tana faɗin
"Yauwwa ina sauraron ka Zaid yi hanzarin bani amsar tambayar da na maka,shin takaici ka ji dan na aibata wannan ballagazar yarinyar"?ran sa a ɓace ya ce
"Eh..rai na ya ɓaci dan kin aibata ta kuma bata cancanci haka daga gare ki ba"cikin zafin rai da ƙaraje ta furta out of the blue
"Did you have feelings for that stupid illiterate villager"da tsantsar ɓacin rai ta mai tambayar shima cikin ɓacin rai ya bata amsar da ya jijjiga ta ya dagula mata lissafi haɗe da haifar mata da baƙin ciki da tsanar yarinyar farat ɗaya
"Yesss..i have feelings for her what can you do about it"??cak ta tsaya kamar an dasa ta a wurin,for almost 1 minute suna a haka duk ran su a ɓace babu wanda ya iya taɓuka komai dan gabaɗayan su faɗar nasu ya shammace su basu san dalilin da ya saka su yin wannan faɗar ba.
Sai bayan ya gama furta kalaman nan sannan ya dawo hayyacin sa sai ya ɗago kan sa cikin wani hali halin tsanani da tsagwaran tashin hankali mai tattare da nadamar kalaman sa ya buɗe baki ya kawo hannu zai taɓa ta kenan ta sauke mai wani razanannen mari da ya gigita sa wanda saura kaɗan ear device ɗin sa ya fita sai dai bai kai ga fitan ba dan magnetic board ɗin ya manne sosai da kunnen sa..
Ɗauke wuta yayi na wucin gadi he can swear that tunda Ammi ta haife sa bata taɓa laying hannun ta a fuskar sa da nufin mari ba but yau ga matar sa ta mare sa..
Hannun sa na ɓari ya ɗaga ya fara kawowa kan jikin ta tana kallon sa kamar ba ita ta ɗauke sa da mari ba sai haki take kamar wacce tayi gudun fanfalaƙi,hannun sa na taɓa jikin ta ta tsala wani ihu haɗe shiga kokuwar ƙwace kan ta amma hakan ya ci tura dan damƙa ne ya mata mai tsauri tana ihu yana mata magana
"kin yi hauka ne ban sani ba Bilkisu?kina cikin normal senses ɗin ki kuwa?i am your husband and you raised your hand and slapped me what is wrong with you"a tsawace ya ke maganar amma madaɗin ta amsa mai sai kawai ya ji wani irin zafi na ratsa hannun sa da ya riƙe ta.
Cizo mai É—ankaran zafi ta gatsara mai hakan ne ya saka sa sakin hannun ta dan dole,yana sakin ta ta ingiza sa tayi bayin haÉ—e da saka lock again..kuka ta shiga yi fiye da wanda tayi É—azu ita yake gayawa eh yana da feelings ma Asma'u what can she do about it..ya salam..

Buga ƙofar yake yi yana kiran sunan ta amma sautin kukar ta kawai yake ji,gajiya yayi dan saura kaɗan kan sa ya buga tsabar ciwon da yake mai.zama yayi a wurin amma sai ya jiyo muryar ta cikin faɗa tana ce mai
"Ka tashi ka fitar min a ɗaki kafin rai na ya ɓaci,just leave my room"salin alim ya tashi ya bar mata ɗakin ya koma nasa ɗakin,neman maganin sa yayi ya sha duk jikin sa yayi zafi yana gama sha ya kwanta a ƙasa yana sauke ajiyar zuciya dan in yayi wasa maybe ya koma asibiti washegari dan zazzaɓi ne mai tsanani ya sauko mai...
Chapter 89 · 0% Book details