← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 157

Sashe 43

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

  For a long while tana ta kai kawo daga ƙarshe ta gaji ta zauna haɗe da matsowa kusa da Bahajjatu ta yi lowering voice ƙasa
  "Baha can't you please help me just last help ban kuma roƙan taimakon ki regarding this but please do me this last favour ki taimaka ki tsallake maganar Ammi ki bar ni na shiga ɗakin nan dan ganin sa wallahi am restless bana jin ina iya samin natsuwa matuƙar ban gan shi yadda nake so ba please baha do something i might create a big calamity here"!!a dame ta ida maganar wanda hawaye yayi accompanying maganar ta ta ƙarshe sai tausayin ta ya kama Bahajjatu but ya zata yi Ammi ta gindaya sharuɗɗa ita kuma bata shirya amsar faɗar Ammi ba sai ta janyo ta jikin ta tana share mata hawayen
  "Beelove ba fah ƙin son shigar ki ake ba a'a,kin ga jiya ɗaya da kika hango sa sai da kika birkice mana kija yi collapsing har sai da aka maki antidepressant kafin mu sami hutu again apple ya amshi laifin da ba shi yayi ba a jiyan nan sannan yau Ammi ta ja min kunne dan Allah kaɗai ya san me zai faru matuƙar kika yi tozali da shi kamar yadda kike son yin kin ga ko ba komai kin jawo min magana da Ammi shi yasa na ƙi barin ki ki shiga ciki ko daga nan ma kina iya hango shi ba sai kin shiga ba ki ƙara haƙuri wataran zaki shiga very soon"!ta cigaba da rarrashin ta dan ita dai bata son shiga matsalar Ammi.
  Dan ji kam ta ji ta bjmut bata jin tana iya rintsawa ba tare da ta ga fuskar sa ba,kuka take yi sosai wanda ya sa Bahajjatu tambayar ta ko dai wani abin aka mata da bata son faɗa sai ta ce a'a ta share hawayen ta a daidai lokacin kiran Bilal ya shigo wayar Bahajjatu saurin picking ta yi ta matso da Bilkisu kusa dan su gana tare,fuskar sa ne yayi appearing da rabin jikin sa da wanda banda white singlet babu kaya a jikin sa ai yana ganin fuskar twin sistern sa yayi saurin kife wayar yana tunanin me yasa Bahajjatu zata mai haka itakuma Bahajjatun da ta ga bai da kaya sai singlet sai tayi saurin kashe wayar dan kar Bilkisu ta gani saboda lokacin da ta saita wayar ita tana faman goge running tears da ke tsere a kan fuskar ta bata ɗago kan ta ba shi yasa bata lura ba sai da ta gama ta ga an kashe wayar
"Me ya faru naga kin kashe wayar"!!tayi mata tambyar sai ta bata amsa da
  "Babu ina ga matsalar sadarwa ne kin san kayan bature"!jijjuga kai tayi ta share maganar idanun ta na kan sa ta transparent door da ke ɗakin ita in da zasu mata adalci da sun yarda ta shiga ta gan shi.
  Kira ne ya kuma shigowa wayar Bahajjatu ta ɗauka Bilal ne sai ta yi saurin dubawa sai dai ba shi ta gani ba numbern kelita ta gani kuma video call ne ɗauka ta yi haɗe da ɓata fuskar ta ta ce
  "Yes"! a halin taimako da agaji kelita ta fara magana
  "Ma'am how are you,how is your brother's health i was informed this morning"!
"Uhumm,,he is fine.anything else"?ta mata tambayar cikin ɓata fuska sai ta ruɗe ta rasa abin cewa tsaki Bahajjatu tayi ta ce
"Am hanging up"da sauri ta dakatar da ita ta hanyar ce mata
"Ma'am is still on the issue,please do something and save a soul i don't know where to go of i leave here please help me"hmm lallai wasu dai basu iya samun wuri ba in banda haka ke ba gidan ku ofishin ma ba na ubanki ba an kore ki amma kamar karya kin ƙi barin wuri sai ta ran ta ya ɓaci a zuciye ta ce
  "Hey drama queen i don't have time for your drama as i have said you should evacuate my office before i return back and that's final"katse kiran tayi tana ta jero tsaki dan haushi da takaici wanda ya saka Bilkisu tambayar ta ko lafiya amma ta ce da ita ta share maganar kawai,sharewar tayi dan dama ba a mood na magana take ba so take kawai ta gan sa ko zata sami sassaucin fargabar da ke ɗawainiya da zuciyar ta..
  Miƙewa tayi ta kama hanyar shiga ɗakin ta dan tana ganin ko kwana zata yi ba barin ta Bahajjatu zata yi ta shiga ɗakin ba,bin bayan ta tayi tana tambayar ta
"Beelove wai ki gaya min wani magana mana"!tana tafe ta ce
"Ina jin ki"!
"Wannan saurayin naki na asibitin ku Dr Aslam ko wa yake?ina yake halan ko bai san baki da lafiya bane dan tun da aka dawo da ku har aka kawo ku ƙasar nan ban ga ya biyo ba bai kiuma kira ba me yasa"??dakatawa tayi ta tsaya kafin ta juyo ta zubama Bahajjatu idanun ta kamar zata yi magana sai kuma ta shiga tunani,.
  Aslma?ina ya shiga?ita ta manta da shi kwata kwata saboda last time da suka yi waya da shi ta wayar Zaid ne kuma a ranar ta mai kaca kacan in kiran ta zai yi ya rinƙa yi ta wayar ta ba wayar Zaid ba dan a lokacin basu fara jituwar sosai da Zaid ba kuma tun daga ranar bai kuma kiran ta ta wayar zaid ba sai dai ta nata wayar and if he call bata ɗagawa dan bata da wani sauran magana da shi but still yakamata a ce ko ba dan personal issues da suke da shi ba as professional colleagues kuma ma'aikacin da ke ƙarƙashin ta ya kamata a ce ya zo ya gaida su daga ita har Zaid but bai zo ba bai kuma nuna ya sani ba yana rayuwar sa comfortably lallai ma Aslam za kuwa ya haɗu da ita wani irin mutum ne shi marar sympathy wa mutani,tana cikin tunanin ta ga hannun Bahajjatu na moving kusa da fuskar ta sai ta ɗan lumshe idanun ta ta buɗe su
  "Bilkisu tambayar ki fah nayi amma kika shiga tunani halan menene"?sauke ajiyar zuciya tayi ta ce
"Babu,about Aslam kuma ki manta shi kar ma ki kuma min magamar sa please ba shine a gaba na ba"tana gama faɗa ta juya ta fara tafiya sai abin ya ma Bahajjatu daɗi dan dama so take ta kuma tabbatarwa koh eh Bilkisu na da wani special feelings ma Dr Aslam but thank goodness hunch ɗin ta bai zama gaskiya ba kuma dama hakan take so dan ita kam bata mafarkin wani ya mallaki aminiyar ta sama da yayan ta ta san duk rashin fahimtar junan su ne ya sa suke ganin kamar ba zasu taɓa iya zama inuwa ɗaya ba kuma a rayuwa yanzu *iya ruwa fidda kai* ne in shi bai iya takun sa ba ita ya kamata ta iya in ita bata iya ba shi ya iya kuma ta ma san dole ne zasu saba dan dukkan su masu sauƙin kai ne kawai rashin sanin ainihin hallayar juna ya sa suke ɗaukar junan su a matsayin wani yana da jin kai but a hakan ma ita ta hango rayuwar su nan gaba matsalar dai shine a ɗaura auren but muddin aka ɗaura ko za'a haɗa sama da ƙasa bai isa ya datse auren ba bai kuma usa ya ƙaro wata ba sai dai ya gama bulaguron sa ya dawo kan hanya because she knows her friend more than anyone ita ɗin ƴar son soyayya ne kuma ta san zata samu daga wun yayan ta dan haka bata da wata ragowar damuwa.
  Saurin rungume ta tayi tana cewa
"Apple dagaske ba shi bane a gaban ki"?mamakin tambayar ne ya kamata sai ta ce
"Are you alright at all baha"??
"Yes..yess am alright am just happy"
"Happy"?ta maimaita maganar Bahajjatun tana kallon ta sai ta girgiza kai ta cugaba da tafiyar ta har suka shiga É—akin bata kuma cewa komai ba sai da suka zauna Bahajjatu ta kuma tambayar ta
"Bilkisu wai ina maganar yarinyar nan da kika ce wai yaya na na so a ƙauyen nan"?sai ta ji ranta ya ɓaci sakamakon tunowa da Asma'u da ta yi sai ta ce
"Baha ki daina ɓata min rai please i don't wanna hear or say anything about that ingrate"a harzuƙe ta yi maganar ƙarshe wanda ya bama Bahajjatu damar tantance eh aminiyar ta kishi take yi da so called girl lover na yayan ta kuma ta hango tsantsar so da takewa yayan nata sai dai in ɓoyewa junan su zasu yi but ko ma dai menene what goes around comes around zasu gane hakan nan gaba.
  Dariya kawai ta yi wanda ya sa Bilkisu kallon ta a tsorace ta ce
"Anya baha ba za'a duba lafiyar ƙwaƙwalwar ki ba kuwa kafin mu koma gida ba"?wani dariyar farinciki tayi kafin ta ce
"Friend i saw what you were unable to see for the past few days humm"!!ƙyale ta tayi dan kamar Bahajjatu ta fara zarewa biye mata bai da amfani.
Chapter 43 · 0% Book details