← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 157

Sashe 118

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Buɗe closet ɗin sa yayi ya ɗauko boxers ya saka ya ɗauko baƙar jallabiya ya saka ya fito daga ɗakin ya ja mata ƙofar ta waje ya saka mata lock sai ya sauko ya fito farfajiyar gidan inda mai gadin nan ya taso cikin ɓarin jiki yana tambayar sa ko lafiya ɗazu ya shigo hankali tashe,muryanshi ya mai kawai ya ce
"Babu komai nagnagode da kulawar ka gare ni and am sorry for reacting to you in that manner earlier on i wasn't in my rightful senses"da sauri mai gadin ya hau ce mai
"no..no no please sir na fahimta ai Allah ya ba Hajiya lafiya"sai ya amsa da
"Amin thanks"!!daga haka ya bashi oder akan ya kula masa da gidan har ya dawo daga masallaci kar ya bar kowa ya shigo amsa mai yayi yana assuring nasa zai kular mai da gidan daga haka ya fita ya nufi masallaci dan gabatar da sallar zuhur..

Bai dawo gidan ba sai bayan sallar asr yana shiga tana farkawa daga baccin ba ma farkawar tayi ba juyawa tayi dan cigaba da baccin sai dai tana juyawan ta ci karo da fuskar sa yana tsaye da murmushi yana kallon ta rufe idanun ta tayi ta buɗe su sai ta kuma sauke su tarr bisa fuskar sa,shi dai yana tsaye yana kallon ta yana jiran ganin abin da zata yi dan ya san zata yi reacting but to his greatest surprise sai ya ga akasin hakan dan bayan ta kalle sa sai ta maido da duban ta ga kan ta ta ga abin da aka lullube ta da shi sai ta ɗaga comforter ɗin ta leƙa ciki all what she sees shine naked body ɗin ta lulluɓe cikin comforter babu kaya daga bra sai pant cikin ruɗewa ta fidfo kan ta ta kalle sa sai ta ga babu alamun wasa ko tantama kenan da sanin sa hakan ya faru,tunani ta shiga yi ta ya aka yi ta zo gidan nan ya ma aka yi ta tsinci kan ta almost naked did he molest her and take advantage of her?saurin mai da duban ta tayi ga jikin ta tana ɗago kan ta sai ta gan sa zaune kan gadon yana yunƙurin jawo ta sai ta ja da baya tana kallon sa dan bata san abin da ya faru ba kuma tana buƙatar ƙarin bayani.
Daɗa ƙanƙame comforter ɗin tayi tana girgiza mai kai sai ta yi wuf ta sauko daga kan gadon tana jan comforter ɗin,tashin da tayi cikin ƙaraje ne ya haddasa mata wani mummunar ciwon kai ta ji kan ta ya amsa amma ƙarfin hali irin nata ya sa ta fara taro ɗan ƙarfin ta ta fara tambayar sa cikin yin ƙasa da murya dan bata da wani isasshiyar lafiya
"Ina kaya na yake"?shiga juye juye yayi yana duba kayan kafin ya dawo da fuskar sa gare ta ya taɓe baki yana girgiza kai alamun bai gan su ba sai ta cigaba da kallon sa dan kan sa ya taso ta shiga nufo ta a hankali bata dai motsa ba tana nan tsaye sai da ya zo har kusa da ita ta ji ƙamshin sa na shigar ta ta ɗago dara daran idanuwan ta ta zuba cikin nasa sai yayi yunƙurin riƙo ta zuwa jikin sa yana tambayar ta
"Me zaki yi da kayan"?murya chan ƙasa kamar mai koyon magana dan har rawa rawa muryar ke yi yayin da yake mata tambayar sai ta ji muryar ta shige ta har ta lumshe ido bata sano ba sai ya ƙara tightening jikin ta cikin nasa yana son rungumo ta jikin sa gabaɗaya sai dai ta hana sa cikin saurin buɗe idanun ta ta shiga ɗan ture sa tana faɗin
"Am going home"daɗa ruƙo ta yayo yana janyo ta jikin sa da ɗan ƙarfi dan tana son turje mai ne shi kuma yayi alƙawarin holding her tight and he will never let go off her dan baya so yayi ruining destiny ɗin sa for the second time again.
Kasa hana sa tayi sai tayi shiru tana jin abin da yake mata,haɗa ƙirjin sa yayi da nata ƙirjin sai suka lumshe idanu tare haɗe da sauke ajiyar zuciya at the same time,she didn't hug him back amma shi kam ya rungume ta sosai ya ɗau lokaci yana sauke ajiyar zuciya kafin daga bisani ya ce cikin sanyin murya da rashin son hayaniya
"Please don't go,just spend the night with me here in our home,in our room, in our bed,our matrimonial bed,please,..will you"!?shiru ta mai tana sauraron sa bata dai ce da shi ƙala ba amma kam muryar sa yayi tasiri cikin zuciyar ta.
"Please..don't say no"...bata ce komai ba sai ya ɗago da ita ya shiga gyara mata sumar gefen fuskar ta yana jiran jin amsar ta sai ta ƙure sa da idanu har dai kallon sa ya haifar mata da wani kasala mai tsanani haɗe da gajiya da ya dirar mata from no where.
He has been observing her ganin yanayin ta ya canza sai yayi using weakness nata yayi brainwashing É—in ta by pleading her to stay with him tonight,juya mai baya tayi tana jin gaban ta na faÉ—i sai dai bata bari fargabar ta ya fito sarari ba.
Ta bayan ya rungumo ta ya sauke haɓar sa a gefen wuyar ta yana sauke mata numfashin sa sai ta lumshe idanun ta chest ɗin ta na sama da ƙasa

"Please..am lonely"..tausayin sa ne ya taso mata sai kawai ta É—an tura sa baya kaÉ—an ta shige toilet É—in É—akin tana shiga ta saka lock ta É—an zauna tana tunanin Allah ya sa ba wani kuskuren zata kuma yi ba by believing Zaid one more timw in her life..
Kasa yin wankan tayi sai tayi alwala kawai ta fito da comforter É—in a jikin ta dama tun da ta shiga ya É—auka tafiya zata yi in ta fito sai ya ji tana tambayar sa
"Ina kayan sallah"?jiki na ɓari ya buɗe closet ɗin sa sai dai bai ga komai ba related to women weat dan haka ya rufe yana mai ce da ita
"Just give me some second ms am coming please"bata amsa mai ba sai yayi saurin fita ya shiga ɗakin da ke kusa da nasa ɗakin alamar ɗakin mallakin ta ne,dubo mata long gown yayi ya haɗo da hijjabi ya fito ya dawo ɗakin sa ya miƙa mata sai ya fita dan ya bata space na shiryawa da kyau..

Sallar zuhur da asr tayi sai ta É—an jingina tana karantar azkhar daga hakan ne kuma bacci ya kuma yin gaba da ita saman sallayar.da ya shigo sai ya ga har tayi bacci sai ya girgiza kai yana mamakin irin wannan bacci da bata gajiya da yin sa but he have to let her be.
Fita yayi ya ja mata ƙofar shi kuma ya shiga kitchen haɗe da kiran ɗaya daga cikin cooks ɗin sa akan tayi saurin zuwa he wants her to coach him dan yana son yi ma baby doctor girki da kan sa..

*******

_7:30pm_

Bayan ya idar da sallah har ya dawo gida yayi setting abincin cikin tray ya kawo har É—akin ya ajiye komai sannan ya zauna zaman jiran ta ta idar da nata sallar,kamar jira yake tana idarwa ya shiga zuzzuba mata abincin ita dai bin sa da kallo take kamar stranger dan sai acting gentile yake mata..
Abincin ya mata daɗi dan akwai ɗan yaji yaji wanda ya taimaka ya bata appetite har ta ɗan ci abincin da yawa shi kuma sai murna yake yi bata yi wani abin da ya ɗaga mai hankali ba,har suka kammala ya ɗauko mata night wear ɗin ta ya bata,karɓa tayi ta shiga toilet ta canza rigar doguwa ce cotton baby pink colour bai da falmara dan dogo ne har ƙasa,.
Fitowa tayi sai ta gan sa kwance da pyjamas ɗin sa kalar nata kayan baccin already ya kashe light ɗin ɗakin ba wani haske sosai dan haka gadon ita ma ta je ta kwanta a hankali ta juya mai baya sai da ya bari ta gama gyara kwanciyar ta har da jan blanket ta rufe jikin ta sai ya saka hannun sa ya juto da ita bata mai gardama ba bare hayaniya shi kuma rashin hayaniyar da bata mai ba ne ya bashi ƙwarin gwiwar ganin zai gyara kuskuren sa,.
Kan ta ya kwanta saman ƙirjin sa ya warware mata sumar da ta tufke ya baza mata su ta baya duk tana jin sa bata dai ce komai ba,hannayen sa biyu ya sa ya rungumo ta jikin sa ya riƙe ta gam,addu'ar bacci ya masu sannan ya ce da ita
"Goodnight baby"bata bashi amsa ba amma ta ɗan juya kan ta saman ƙirjin sa alamar ta ji ta kuma amsa.ba jimawa bacci ya ɗauke su duka..

*_S,Ibraheem_*
Folliw@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

   *35*

  *_Back to love_*
Chapter 118 · 0% Book details