← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 157

Sashe 119

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_4am_
Buɗe idanun sa yayi a hankali yana fatan ganin ta tare da shi,a hankali ya maido da kan sa ƙasa ya juyo zuwa right side ɗin sa sai ya gan ta kwance duk ta kalailaye sa collar rigar baccin sa ta riƙe gam kamar rayuwar ta maƙale da rigar yake,kawo hannun sa yayi ya ɗora nisa nata hannun da ta riƙo mai rigar ya shiga shafawa a hankali yana jin farinciki da annashuwa na shigar sa dan bai san yadda zai yi ba da ya farka a asubahin ya ga duk abin da ya faru a jiya was all nightmare and not reality,godiya yayi wa Allah da ya sa yayi witnessing wannan safiya mai albarka he can't believe that after the minute of his first night bai kuma kwanciya tare da matar sa ba sai yau abin ya zame mai kamar abin farinciki da nishaɗi..
  Goodmorning kisses yayi brushing mata tun daga goshin ta zuwa cheeks ɗin ta har ya sauko wuyan ta sai a lokacin ta farka dan tun lokacin da ya kai hannun sa saman nata hannun ta ji abin amma sai ta share ta cigaba da bacci dan sama sama take jin abubuwa abaccin ta.
  Buɗe idanun ta ke da wuya sai ya rumtse nasa idanun da sauri abin nasa dariya ya bata kamar wani ƙaramin yaro yayi saurin rumtse idanun sa,ganin kan ta cikin jikin sa sai ta ɗan murmusa tana tuno rashin ta idon da ta yi a jiya daga zuwa office sai kuma ta yi gidan miji har kuma da tsarabar taya sa kwana,murmushi tayi tana hasashen yadda zai kaya tsakanin ta da Umma ko me zata gaya mataas excuse na rashin komawa gida a jiya.
  Jin shirun ta yayi yawa sai ya buɗe idanun sa ya zuba mata dan kallon sa take tana lumlumshe idanu saboda halin da ta tsinci kan ta ciki ya wuce misalin mai tunani dan nishaɗi ne ke gauraye da tsaftatacciyar son sa ya rinƙa shigar ta,bata san me ya faru da shi ba da ya hanasa tafiya ƙauyen koma amma ko ma dai menene dalilin she don't want to know.

  "Uhum,,goodmorning"!!ɗago kan ta tayi ta zuba mai idanun ta suka yi exchanging glance look sai ta ce mai 
"Morning"idanun su haÉ—e da na juna duk wani hali suke ciki daga shi har ita, blinking mata idon sa É—aya ya ce
  "Ya jikin ki"?ɗan shiru tayi tana kallon sa murya can ƙasa ta amsa mai
"Alhamdulillah"!nodding kan sa yayi ya shafo suman ta yana faÉ—in
  "Kin tuna ranar mu da ke na farko?a germany"?saukar da idanun ta ƙasa tayi tana murmushi tana tuno moments ɗin da ya kasa skipping memory ɗin ta she wish abin da ya faru da su never happened da Allah kaɗai ya san irin love da zata yi showering Zaid da shi but unfortunately,,it was a bad past she doesn't wanna remember it..
   "Uhumm"he wasn't satisfied with the response sai ya kuma rungumo ta yana shinshinar sumar kan ta at the same time yana kissing suman
"Won't you forgive your husband"??shiru tayi tana jin kewar sa na addabar ta sai dai still bakin ta nauyi yake mata na bashi amsar tambayar da ya ke kwararo mata but har cikin zuciyar ta tana jin yafe mai shine alkhairi.
  Shafo gefen fuskar ta yayi yana jin kamar su dawwama a haka bai san girman abin da yake ji a zuciyar sa game da ita ba amma ya san he is gradually dancing to her tune and he is copping with her possession and obsession tun ranar da ya bar gidan su ya dawo nan gidan babu ranar da zai farka daga bacci bai farka da ita a zuciyar sa ba haka Throughout zai yi spending ranar sannam duk daren da zai kwanta bacci baya samin cikakkiyar bacci dole da tsakar dare sai ya farka yayi wanka dan baccin sa ba mai daɗi bane mafarke mafarken ta ya dame sa definitely her words are beginning to manifest she once told him that she will be his obsession and yes she is now his obsession safe,rana,yamma,dare yana tunanin ta a ran sa again he feel so suffocated in ya ga wani kusa da ita shi yasa ranar da ya ga Aslam yana magana da ita har ya kira ta da baby sai ya ji ya kasa controlling kan sa all he need shine ya mai gyaran tunani dan ya ƙi jinin ya ga wani kusa da ita muddin ɗa namiji ne toh hakan na tayar masa da hankali he can't take that..
  "Kin yi shiru,,can't you forgive me at least"??jin wani iri tayi sai kawai ya ji ta kuma rungume sa sosai sakamakon da da shi kaɗai ya rungume ta,sosai tayi hugging nasa tight tana jin hawaye na son zubo mata dan ba ƙaramin dauriya tayi ba na rufe idanun ta da doɗe kunnuwar ta dan ta ga zancen Asma'u bai taso mata ba,raɗaɗi da zafin kishin sa ne ya taso mata sai ta shiga dukan sa a ƙirjin sa tana faɗin
"You cheated,,i trusted you,i gave you my heart my soul,my body,my life but you rejected it you forced me to hate you you toyed with my feelings for you,you played with my heart,you played with my love for you because you know that i love and care about you then you decided to give that hate to me why Zaid,?why"??da kuka maganar ta na ƙarshe ya kai sai yi take yi kamar me and he allowed her because iya hanyar da zata iya pouring out nauyin da ke zuciyar ta kenan..
  Rungume ta yayi sosai yana shafa ta bau ce komai ba yana da shafa ta ita kuma kamar a lokacin kuka ya ƙwace mata sai yi take yi iya gaskiyar ta.
   Sama da mintuna tana kuka har sai da nauyin da ke zuciyar ta taji ya ragu sai ta rage yawan kukan ta shi kuma sai ya riga ta magana muryar sa na karyewa yana shaƙewa dan haɗo kalmomin yayi
  "i know,na sani,na san ni na saka ki jin kin tsane ni ni na saka ki jin kin yi babbar kuskure a rayuwar ki by giving me something very precious to you but please....i want you to give me another chance...just give me this one more chance i promise to show you something incredible i promise to take you where you've never been i will be a good husband to you a friend and a guidance just allow me to come into your life one more time please"kamar dai a mafarki haka ta rinƙa jin kalaman nasa kamar almara da gaske yake yi ko dai yi yake yi dan ya faeanta mata rai na wai dan yayi niya ba.
 
  Kallon sa tayi tana son tantance gaskiyar sa cikin kalaman sa sai ta ga pure sincerity a tattare da shi and nothing else but that,ta rasa wani shawarar zata bi dan shawarwari zuciyar ta ke bata daga ɓangare daban daban ta rasa wanda zata ɗauko.
  Leƙo fuskar ta yayi yana jiran jin amsar ta addu'ar sa shine Allah ya sa ta yarda ta amince da shi ya shigo rayuwar ta for the second time matuƙar ta bashi wannan damar zai gyara laifukan sa na baya.
  Wasa da hannun sa yake yi saman sumar ta ta yadda zata sami sukuni cikin zuciyar ta dan tayi hukuncin da ya kamata,tana jin sa yana kai kawo da hannun sa a jikin ta amma ta kasa ce mai komai haka ta kasa hana sa sai ma daɗa yin lamo da tayi a jikin sa shi kuma ya ƙara yi mata mazauni a jikin sa,jim kaɗan ba jimawa ya ji numfashin ta ya canza haka kuma nauyin ta ya fi na ɗazu hakan alama ce ta bacci ne ya ɗauke ta.

  Duniyar tunani ya faɗa tun jiya sai bacci bacci take yi ba gayra ba dalili da ta zauna sai bacci tun jiyan yake observing ɗin ta da ta farfaɗo daga suman da tayi ta koma bacci ba tare da ta sani ba bayan ta idar da sallolin jiya ta kwanta bacci bata tashi ba sai gab da magrib bayan ta idar da sallah ta ci abinci tayi saurin yin bacci bata farka ba sai ɗazu and now....she is sleeping already what could that be?..
  Bai san amsar ba dan haka sai ya ja jikin sa ya kwantar mata da kai bisa pillow ya daɗa gyara mata abin rufe jiki shi kuma yayi toilet,alwala yayi ya zo ya canza kayan sa ya saka jallabiya da wani hular sanyi da yake yanayi ne na winter,.
  Masallacin nan kusa da su ya tafi dan a lokacin biyar ya gota har da mintuna ashirin dan sun ɗau lokaci suna magana shi da Bilkisu har time ya wuce bai yi la'akari.
  Kasancewar ya san ita kaɗai ya bari a gidan ba wani wanda zai kular mai da ita shi ya sa yana idar da sallar ya nufo gida lokacin har gari ya fara wayewa haske ya fara bayyana sai ya ɗan ƙara saurin sa ya iso gida,gaisuwar su da mai gadin sama sama ne burin sa ya isa ciki ya tayar da ita dan lokacin sallah na tafiya kuma ya san har in ba tayar da ita aka yi ba ba tashin zata yi dan bacci mai nauyi ne ke ɗaukar ta..
Chapter 119 · 0% Book details