← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 157

Sashe 79

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Shi ya ɗauko plates biyu da spoons ya zo ya juye masu abincin cikin different plates ɗin sannan ya zuzzuba masu chill drink a tumbler,tana bin sa da kallo har ya kammala tana kallon sa bata ce da shi ƙala ba sai da ya kammala duka ya ɗago ba yabo ba fallasa ya ce
  "Bismillah"!!...wani irin kallon kashe jiki ta mai dan ƙanƙance idanun ta tayi tana mai kallon ƴan boko,shi kuma ya kasa furta komai sai bin ta da ido da yake yi kan sa duk ya ƙulle ya rasa dalilin ta na nuna mai wannan attitude ɗin.
  Bai gama tunanin nasa ba ya ji muryar ta kamar mai jin baccin tana faɗin.
"Bismillah??toh bismillah"ta faÉ—a cikin halin ko in kula haÉ—e da É—aukar spoon da side table knife tana kallon sa dan kamar statue ya koma a zaunen yana mamakin ta sam bai san ta shahara har haka ba sai yanzu.
  Alama ta mai da ido irin ina jiran ka ɗin nan dan kuwa babu alamar wasa a fuskar ta kenan bata ji daɗin yadda ya mata tayin abincin ba.
  Kallon ta yake kyar dan dai ya fara shiga duhu da ɗabi'un da tayi adopting tana displaying mai.
  Saka cokalin yayi cikin plate ya fara ɗibawa zai kai bakin sa sai ya ƙaƙare ya kasa sakawa ya tsaya kallon ta sakamakon ganin nata cokalin cikin plate ɗin abincin sa hankali kwance ta ɗibo sai ta dakata bata saka a bakin ta ba ta aika mai da wani kallon kashe jiki sannan cikin taushin murya ta ce
  "Bismillah"ai bai san lokacin da ya fara tari repeatedly babu tsagaitawa ba sai ta ɗan nuna alamun damuwa a kan fuskar ta sannan ta tashi cikin kula ta ɗauko mai ruwan sha dan organic drink ɗin na iya increasing mai rate na tarin bit water will be more suitable for him.
  Bashu ruwan tayi a baki ya ɗan yi sipping sannan ya ɗaga kan sa yana kallon ta,haɗa ido suka yi ta mai sannu da idon haɗe da gyaɗa mai kai irin it is well ɗin nan sai kawai ya sauke idon sa haɗe da furta
"Nagode"sai ta ce mai
"Ba komai ai aiki na ne"da murmushin ta ta faÉ—i hakan sannan ta dawo ta zauna ta É—ebi abincin ta kawo bakin sa haÉ—e da ce mai
"Haaa"sai ya kalle ta a kasale bai buɗe bakin ba har sai da ta mai alama da kai sannan ya buɗe bakin yana mai yin bismillah,saka mai cokalin abincin tayi a baki ya karɓa sai ta cire ta kuma ɗebo wani ta ƙara bashi ya karɓa,a taƙaice dai ita ta ciyar da shi har ya ƙoshi sannan ta ɗau nata plate ɗin ta saka same spoon da ta bashi abincin da shi ta ɗauka zata tashi dan komawa ɗakin ta cin abincin.
  Yana ganin haka kuwa ya kawo hannun sa ya riƙe nata hannun da take da nufin ɗaukar tumbler,dakatar da ita yayi yana mai cewa
  "Zauna mana ina kuma zaki tafi"??sai ta ji gaban ta ya ɗan faɗi dan riƙon da ya kawo mata ya shige ta ba kaɗan ba.
  Haɗa ido suka yi sai ta kawar da nata idon kamar marar gaskiya ta ce
"Dinner zan yi having"!!still yana kallon ta ya ce
"Wayo dai zaki min,kin gama bani na ci sannan ke ki ce guduwa zaki yi ki ci alone dan kar in ga menene"?dariyar mamakin sa tayi sannan ta ce
"Ban gane ba?abinci zan tafi in ci,,ina son shan magani kai ma ya kamata ka sha night medicine naka"sarai ya gane so take tayi dodging tambayar da ya mata dan haka shima sai yayi claiming ai bai ma san inda maganar tata ta dosa ba yayi pretending dan dolen ta ta dawo ta zauna ta ɗau cokalin zata fara ciyar da kanta sai ya riga ta riƙo cokalin,ta zuba mai idanun ta bata ce komai ba sai ta ga yana ƙoƙarin fara feeding nata abin ya ɗaure mata kai but bata dai ce komai ba.
  Sai da ya ɗibo iya bakin ta sannan ya ce da ita
"Haaa"kamar dai yada ta mai sai abin ya saka ta darawa wato shi ba'a mai bai rama ba..
  Share ta yayi dan shi dai duk abin da yake yi ji yake kamar ingiza sa ake yi yayi su dole dan haka baya jin wani damuwa ko da ta mai dariya in dai zai sami sauƙin damuwar da yake damin sa he is okey..
  Buɗe bakin tayi ya saka mata,a ƙalla sai da ta yi rabin plate ɗin nan sannan ta shiga girgiza mai kai alamun ta ƙoshi sai ya tambaye ta
"Are you sure"?ta kuma girgiza mai kai sai ya miƙo mata drink ta sha haɗe da karɓa daga hannun sa tana ce mai
"Thank you"ya ɗan murmusa sannan ya tashi ya kwashe kayan dama tana da niyar taya sa kwashen kayan amma ya ce ta bari ita da ba lafiya sai ta yi zaman ta haɗe da ƙunna plasma ta kamo tashar da ya kamo ranar da suka kalli theater da dare.
  Zama tayi haɗe da crossing ƙafafun ta tana ɗan kaɗa su a hankali ta natsu tana kallon yadda ake feɗe wata mace ana son cire mata fibroid mayomas,ta zurfafa a kallon har ya fito bata sani ba sai da ya zauna yana mai faɗin
  "Interesting"sai a nam ta kalle sa tana mai yin murmushi haɗe da gyaɗa mai kai,daga haka suka mayar da hankalin su kan kallon har aka gama sai dai ana gab da ƙarasa ɗinke feɗan suka shiga yiwa kan su tambayoyi a course of tambayar ne suka shiga arguing da juna har ma da abin ya masu sugar suka koma yin raffle draw sai da aka kammala show ɗin sannan suka natsu sai suka koma yiwa kan su dariyar shirmen da suka rinƙa yi,gaskiya ta ji daɗi abin nan dan ko ba komai yana copping da internal response nasa ta ji daɗi ba kaɗan ba..

  *3 hours later*

  Bayan sallar azahar ya shirya cikin ƙananan kayan shan iska ya duba ta a ɗakin ta dan yana son su ɗan zaga hotel ɗin tare since they have no where to go..
  Ganin ta yayi kwance babu doguwar rigar sai ƙananan kayan da ta saka a ciki,bacci take sosai hankali kwance sai ya mata kallon ƙurilla tun daga ƙasar ƙafar ta har ya kawo kan sumar kan ta yana kallon ta yana admiring jikin ta sai ya ji baya son takura ta sai kawai yayi tafiyar sa shi kaɗai ya zaga ilahirin hotel ɗin baki ɗaya yana zagawa yana tunanin ta har dai la'asar ta yi sannan ya dawo ya yi sallar sa ya kuma komawa ɗakin ya ga still baccin take sai yayi murmushi haɗe da girgiza kan sa irin wannan bacci nata haka ina zata kai sa..

  Bayan kamar awa huɗu a tsakani lokacin har an fara shirin bacci dan sun gama cin abinci har sun yi sai da safe sai ya ga kawai ba zai iya ba dole ya dawo ɗakin nata ya tura yana doka mata sallama daga kwancen da take ne ta amsa mai tana mamaki dan har tayi addu'ar bacci. 
  Lighting ɗakin yayi sai ya hango ta kwance ta ɗan leƙo ta blanket ɗin tana kallon sa,rasa abin faɗi yayi sai ya faƙe da cewar
"Dama zuwa nayi dan ƙara yi maki goodnight"da fara'ar ta ce
"Alright goodnight"sai ya tsinci kansa da waving nata yana murmushi itama martanin hakan ta mayar mai,ya ja mata ƙofar haɗe da kashe hasken ɗakin.
  Komawa baccin ta tayi shi kuma ko da ya isa ɗakin sa baccin kasa ɗaukar sa yayi dan haka ya rinƙa juye juye shi bai san me ke damin sa ba sam wannan baƙon al'amari bai mai adalci ko kaɗan.
  Da ƙyar da yaya baccin ya sace sa babu labari,baccin kusan baccin wahala ne dan kan sa ya kusa bugawa tsabar takura mai da yayi da tunani marasa mafita...

*7 days later*
  _*Last night in Germany*_

  Misalin ƙarfe takwas da mintuna ashirin da biyar na dare tana kwance da ƙaramar nightie tana tsara abubuwan da zata yi a washegarin in sun koma gida saboda daga Ammi har Umman ta sun gama zuzuta mata kyawun gidan ta sun sanar da ita yadda aka tsara masu gidan very portable kuma an gyare ko ina jiran zuwar su kawai ake yi dan har abincin da za'a masu washegarin an gama harhaɗa su a row suna kamo hanya za'a fara dafa masu,duk sun saka mata kwaɗayin gidan nata a ran ta ga ƴan uwan ta sun gama kwaɗaita mata jin daɗin rayuwar da zasu yi a gidan su dan gida ne mai tsarin gaske wanda yake situated a Apo Hills birnin tarayya na ABJ..
  Juyawa tayi bisa kan gadon tana ƙara tuno rayuwar da suka yi a gidan har zuwa goodnight da suka yi da juna cikin ƴar kwanakin nan da suka zauna inuwa ɗaya.
  Wato wano irin zama ne suka yi wanda ke tattare da tsantsar kulawa da daraja juna haɗe da taka tsantsan dan gudun ɓacin ran wani a cikin su ga so da ke girgiza su a karkace for her,she is aware amma shi kam bai ɗaukar hakan a bakin komai ya fi dangana hakan da zaman taren da suka yi wa da shi ya janyo masu jituwa mai tsananin gaske..

  Ita kaɗai ta rinƙa analysis ɗin ta sam babu wani abin da ya shiga tsakanin su tun da aka ɗaura auren har kawo yau da yake masu daren ƙarshe a ƙasar,kuma abin bai dame ta ba dan ta san duk wani abin da zai rikita sa ta mai kuma ta san ya ruɗe ba kaɗan ba..
Chapter 79 · 0% Book details