← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 157

Sashe 145

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

Cikin jin daÉ—i ta ce da shi tana mai matsowa kusa da shi
"Are you sure babu inda yake maka ciwo"?da Æ´ar murmushin ta ta faÉ—i hakan sai ya juyo da kan sa yana kallon ta kafin daga bisani ya ce
"Akwai"!!!cikin faÉ—uwar gaba ta ce
"Ina ne kuma"?idon ta na ciccikowa da hawaye yayin da ta mai tambayar sai ya mata shiru ita kuma ta tsani wannan shirun dan kashe ta yake yi a hankali...
Hannun ta na rawa ta kawo kan nasa hannun ta haÉ—e wuri É—aya ta fara murzawa a hankali ta kuma maimaita mai tambayar
"Ina ke maka ciwo hero"??hannun sa na hagu ya É—aga a hankali ya yi amfani da index finger nasa yayi pointing mata direction na zuciyar sa..
A wani irin haukace ta raba hannun ta da nasa ta ja baya tana mai rufe bakin ta sakamakon jin wani ihu da ke son kufce mata...
Kallon ta yayi ya rasa me ya razana ta da ta firgita haka sai dai bai iya ce da ita ƙala ba..
Faɗuwar gaban ta ya tsananta ta ji ko ina na jikin ta yana mata wani iri sai ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya..
For a while yayi shiru yana kallon ta har dai ya magantu
"Lafiya"??muryar sa chan ciki yayi tambayar sai dai ita da ke a ruÉ—e ta kasa gane cewa tambayar ta yake sai ta kuma fashewa da wani kukan har dai ya gaji ya matso kusa da ita...
Bata sani ba sai dai jin ta tayi a jikin sa yana mai rubbing hannun sa a bayan ta..
Ai kamar ya kuma ingiza ta ta kuma fashewa da wani sabon kukan sai yi take yi shi kuma yana rarrashin ta..
Tsagaitawa tayi daga kukan da take yi ta natsu sai ta ji kamar daga sama muryar sa na mata amshi a kunnen ta
"Me yasa kika min haka"??É—if ta ji ta É—auke wuta sakamakon tambayar da Zaid ya mata dan out of the blue ta ji tambayar...
Ɗagowa tayi niyar yi sai ya ƙi barin ta ta ɗagon ya kuma mayar da ita ya rungume ta..
A ƙarƙarshin zuciyar sa shi ya san sam bata da mummunar nufi a bisa ga abin da ta aikata mai sai dai ta saka sa duhu son sanin dalilin ta na yin hakan kawai yake...
Silent tears ne ke biyo mata fuskar ta a hankali suna sauka saman rigar jikin sa bata iya ce mai komai ba haka shima bai iya furta mata komai ba yana sauraron ta...
Share hawayen tayi da hannun ta ta ja hanci tana mai jin zafi da raÉ—aÉ—in abin da ta mai a zuciyar ta...
Kaf abin da ya faru ranar a dajin ƙauyen koma ta mayar mai sannan ta dawo ta sanar da shi rayuwar sa a asibitin germany ta ɗora da bayanin da Dr Gabby ya mata da ɓoyewar da ta ma family ɗin su har kawo ga bayyana mai dalilin ta na aikata mai abin da ta aikata ta ɗora da sanar da shi kyakyawar labarin ya warke kenan har abada babu shi babu wani matsala mai firgitarwa
"You can now leave a normal life just as everyone does"..hawaye duk ya gama wanke mata fuska dan tsakanin ta da Allah ta ke jin tausayin sa na bin duk wasu sassa na jikin ta sai dai itama bata da yadda zata yi shi yasa ta kasa fidda abin a ran ta but yanzu da ya nemi sanin dalilin hakan ta mai bayani sai ta ji sauƙi a ran ta at least ko ba zai cigaba da son ta ba ko nuna damuwar sa da kulawar sa a kan ta ba ta san zai iya yafe mata wataran...

Ajiyar zuciya mai ƙatfi ya sauke yana mai jin wani irin baƙin ciki da haushin Mudan na shigar sa from no where all he wants yanzu shine yaui tozali da shi ya san tabbas sai dai mahaifiyar sa ta haifi wani Mudan ɗin dan sai ya tabbatar da ya lahanta shi for causing him a long hospitalization har yayi undergoing surgery sau biyu again abin takaicin shine pregnant wife ɗin sa na hana kan ta sukuni all because his illness is affrcting her kuma duk Mudan ne ya janyo hakan,,...
Tunowa yayi da Asma'u da ya gani ganin ƙarshe a dajin nan sai ya maido da kan sa ya kalle ta yadda ta rumtse ido tana faman kuka..
"Ina Asma'u take"??tsorl,firgici da mamaki ne ya mamaye ta sai ta rasa abin faÉ—a..
"Ina Asma'u take"??É—ago kan ta tayi tana share hawayen fuskar ta ta ce
"Hero...Asma'u.,,tana gidan su me ya faru"?jijjiga kai ya shiga yi kafin ya ce
"And Mudan"??yana kallon ta kyar ita kuma ta ruÉ—e sai ta sanar da shi abin da ya faru da Mudan É—in ta É—ora da yi mai bayanin masu alhakin faruwar abin da ya faru da shi..
"Tun yaushe hakan ya faru"?ya tambaye ta cikin dakiyar zuciya sai ta ji tsoron sa ya kama ta
"Tun lokacin da muka dawo gida daga ƙauyen"!!shiru yayi sannan ya ce mata
"Ina waya na"??abu yake yi mata kamar ba Zaid É—in da ta sani ba sai ta fara fargabar sa.
Tashi tayi a natse ta je ta ɗauko mai wayar ta miƙa mai tana bin sa da ido..
ganin son kira yake yi sai ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar ƙwace wayar tana faɗin
"Me kake ƙoƙarin yi"??wani irin kallo ya mata wanda ya saka ta kasa ganewa Zaid ɗin da ta sani ne ko kuma wani new formed Zaid ne wannan ɗin
"Miƙo min waya ta"ƙin ba sa wayar tayi ta cigaba da riƙewa tana mai ƙoƙarin tashi daga kusa da shi sai ya wani saka ƙafar sa takawar da zata yi dan tsallake sa sai ta ji tayi langa langa zata faɗi ƙasa sakamakon ƙafar sa da ya saka mata..
Ta sadauƙar faɗi zata yi sai ta ji akasin haka dan hannun sa ne ya riƙo ta saura ƙiri ta faɗi ƙasa amma hannun sa ɗaya ya saka ya riƙo hannun ta sai bata faɗi ƙasan ba...
Cikin tsoro da firgici ta buɗe idanun ta sai ta gan sa riƙe da hannun ta kenan shi ya saka ta kusan faɗi sannan ya taimake ta me hakan ke nufi??..
Jawo ta yayi ta baya sai ta juya da baya ya zaunar da ita,,tana numfashi mai ƙarfi ya riƙo hannun nata wanda ke ɗauke da wayar ya ƙwace abin sa zai yi dialing sai kawai ta saka mai kuka mai sauti da gangar duk dan kar yayi kiran..
Chapter 145 · 0% Book details