← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 157

Sashe 120

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Kamar ya sani,yana shiga ɗakin tana gyara kwanciyar ta dan cigaba da baccin sai da ya bar ta ta sami mintuna biyu a haka sannan ya zo har saman gadon ƙafar sa ɗaya dogare da gadon ta ƙasa ɗaya kuma ya ɗora bisa kan gadon ya duƙar da kan sa ƙasa kaɗan ya yaye blanket ɗin ta wuyan ta ya kai lips ɗin sa ya manna a wuyan ta ba kiss ya mata ba amma ya ɗau lokaci da lips ɗin sa a nan tun tana share abin har ta ji ba ta iyawa dan dole ta buɗe idanun ta ta juya zuwa direction ɗin sa cikin kula ya kalle ta ya ce
  "Lokacin sallah yayi baby tashi ki yi"!!shiru tayi na wasu seconds kafin ta fara yunƙurin tashi jikin ta duk ciwo yake mata dan baccin da take yi ba na daɗi bane kawai dai ba yadda zata yi dan duk lokacin da ta kwanta baccin dolen a takure take yin sa sai ta tashi duk jikin ta ya rinƙa mata ciwo tana jin zafi but tana da niyar zuwa asibiti a duba ta dan ita ta kasa yiwa kanta diagnosis mai ma'ana at first ta yi tsammanin tunanin Zaid ne da ta sakaea kan ta sai ta rage tunanin amma still babu wani canji sai ta canza diagnosis ta ce maybe zaman wuri ɗaya ne dan in ba wani aiki ne ya taso da za'a kira ta yi ba shima da ta kammala take komawa gida,bata yin komai but still abin sai ya girme mata fiye da tunanin ta dan haka ta yanke shawarar zuwa ganin wani likita maybe zata sami lafiya.. 

  Tana dire ƙafar ta ɗaya ƙasa yayi saurin zagowa ya riƙo ta yana ce mata
"Easy...slowly"!duk hankalin sa ya koma kan ta sai taka tsantsan yake yi da ita abin sai ya saka ta wondering  me yake ta damuwa da ita har haka,ta san dai ba sauraron sa tayi ba but why all the caring stuffs..
  Hannun ta cikin nasa ya ɗaga ta ta tashi da ƙafafun ta sai ta zame hannun ta ta wuce ciki ta yi brush haɗe da yin alwala tun kafin ta fito har ya ɗauko mata hijabin sallah ya shimfide mata sallaya ita kawai yake jira.
  Wow is this guy for real!?tambayar da ta wa kanta kenan ganin yana ta abubuwa so gentile ta manta shi ɗin haka yake dama chan yanayi ne da rashin fahimta ya sa ta kasa gane hakan sai yanzu da aure ya haɗa su ƙarƙashin inuwa ɗaya..
  Tana hawa kan sallayar ta yi kamar zata tsugunna ta ɗau hijabin sai ya riga ta ya ɗauko ya miƙo mata ta karɓa tana mamakin sa sai dai bata iya cewa komai ba.
  Tada sallar tayi shi kuma ya ɗan kishingiɗa yana kallon ta har ta idar da sallar tayi addu'ar da zata yi idanun sa na kan ta tana gama addu'ar kawai ta kwanta nan ta cigaba da baccin ta dama ba isar ta baccin yayi ba gajiya ne ya saka ta farkawa.

  A ɗan hanzarce ya tashi ya ƙura mata ido me ke damin ta ne wai haka?baya jin tsetse fly na yawo a gidan bare yayi tunanin baccin ta na da nasaba da cizon sa toh anya kuwa lafiyar ta ƙalau...
  Tasowa yayi ya zo inda take kwancen ya tattare mata hijabin ya gyara ta yadda zai rufe ta da kyau shi kuma ya ɗan raɓa ya kwanta a gefen ta yana kallon ta sai sharar bacci take yi.,hannun sa ya sagala da nata hannun yayi creating interlock ymda yatsun su ya kuma matso da fuskar sa kusa da nata ya kwantar da kyau ta yadda duk wani abin da zai yi zata jiyo sa itama haka..baccin ne dai ya kuma ɗauke su. 

_8am_
  Sai yanzu suka farka daga baccin daga ita har shi sai da jikin su ya gaya masu kwanciya a ƙasa bayan sanyi ga ƙarfi da rashin taushi dan ma da darduma kenan,ganin sa kwance kusa da ita sai ya kuma bata mamaki ta kasa gane shin gaske ne ko faking yake yi..
  Ita ta riga sa tashi tana miƙa shi kuma daga kwancen ya ƙare mata kallo ba komai miƙar ta ke haddasa masa ba illah sha'awar ta amma ba halin manifesting dan sai tayi tsammanin dama dan hakan ne ya ke mata abubuwa yake kuma bata kula..
   
  Tana sauke hannayen ta hamma ya biyo baya sai yayi saurin ce mata
"Hungry"!?gyaÉ—a mai kai tayi sai yayi saurin tashi yana faÉ—in
"Ina zuwa ki bani 15minutes okey don't go anywhere"!!da kai ta amsa mai  yana gama faɗin haka ya tashi yayi waje ita kuma ta tashi daga saman sallayar tayi cikin toilet dan yin wanka sai dai babu wasu abin buƙatar ta dan haka sponge ɗaya da ta hango da shi tayi wankan ko cikin bathtub ɗin bata yi gigin shiga ba dan ta san tana shiga bacci ne zai ɗauke ta.
  Cikin kwanciyar hankali tayi wankar ta ta saka rigar wankar sa dan ya fi ƙarfin ta lulluɓe kan ta tayi da towel ɗin sa ta fito kan ta tsaye bata yi tunanin ganin sa cikin ɗakin ba sai dai what shocked her shine tana turo ƙofar ɗakin ta gan sa tsaye babu riga sai boxer da yake sanye da shi,tun daga ƙasa ta fara kallon sa tana kallon ƙafafun sa da ke ɗauke da suma kwance har wani gazar gazar suke yi wanda ta ji tsigar jikin ta ya tashi at once,kaɗan kaɗan ta rinƙa kallon sa har ta kawo jikin sa ta rinƙa kallon bare chest ɗin sa da ke a ɗan buɗe ta kalli right and left side na ribs ɗin sa ta ga ABS packs ɗin sa sai ta tsaya tunanin ita ce ta ɗauki nauyin sa a daren rannan?she can't believe it ta san in aka bar ta da shi a rightful senses ɗin ta toh lallai zata mai kuka wataƙil har da shessheƙa dan shi ɗin ba na wasa bane..
  Yana kallon ta tana ƙare mai kallo yana bin ta da ido har ta gama ta sauke idanun ta ƙasa ta shiga nemawa kan ta hanyar tafiya bai yi gardama ba ya ja gefe ya bata hanya,raɓawa tayi ta gefen sa ta wuce sa shi kuma ya shige toilet ɗin dan yin wanka..

  Da wani irin full force ta zauna bisa gadon tana maganganu da iya gaskiyar ta
"Toh kuma menene na cire kayan jikin sa alhalin ya san ina ciki kuma ma ni ba ce mai nayi ina buƙatar kallon jikin sa ba in ina son kallon jiki ne ga nawa jikin ba sai in kalla ba mtsw"ta ja tsaki sannan ta hau dube duben inda zata ga cream dan ga dukkan alama nan ɗin ba ɗakin ta bane nasa ne saboda babu kayan gyara irin na mata,.
  Hango cream ɗin tayi saman abin shafe shafe sai ta kai hannun ta ta ɗauka ta matso ta shafa a ƙafar ta tana shafawa tana tuno jikin sa da ta gani ba kaya wani bin tayi tsaki wani bin ta girgiza kai..
  Shafe jikin ta tayi da cream ɗin sannan ta koma ta zauna tana jiran fitowar sa dan ya kai ta inda zata sami kayan sakawa,.
  Abin dariya tana kwantawa kawai sai bacci wannan abu ya ba Zaid mamaki ba kaɗan ba dan yana ta kiran ta akan ta kawo mai towel amma bai ji amsbi ba sai ya keƙi da kansa only to see her sleeping,ƙarasa fitowa yayi ya duba ya ga towel ɗin gefen gadon a ƙasa ɗagawa yayi ya ɗaura sannan ya goge jikin sa da ƙaramin towel da ke hannun sa,..

  Shirya kan sa yayi cikin kaftan grey colour ya fito da ƙwarjinin sa fili matsalar ɗaya ce rashin gyaran fuskar da bai yi ba kuma shi ba wannan ne damuwar sa ba damuwar sa shine Bilkisu ta cigaba da zama da shi kar ta ce gida zata tafi dan tana faɗin hakan zasu ɓata because he won't let her go home..
Chapter 120 · 0% Book details