← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 157

Sashe 150

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bilkisu kina ji na"?amsa mata tayi jiki a sanyaye
"Eh ina ji Umma"
"Da kyau toh,,ki saurare ni ki kuma fahimce ni da kyau dan abin da zan sanar da ke ƙila ba zai maki daɗi ba amma dole ni ɗin ce zan sanar da ke..,Bilkisu kina fama da matsananci kishi mai duhun gaske sam babu haske cikin kishin ki wanda shi ya janyo maki rashin fahimtar mijin ki kwata kwata kin kasa gane abin da ke gaban ki sakamakon baƙar kishin sa da kika ɗorawa kan ki Bilkisu,ban ce kar ki ji ko kar kiyi kishin sa ba amma ana sara ana duba bakin gatari shi fah Zaid namiji ne mijin mace ɗai ɗai har huɗu kenan bayan ke yana da ikon ƙara wasu har uku dan ya cike gidan sa,baki da hurumin taso sa gaba kina nuna mai aon ra'ayin ki akan dole shi zai hau ya zauna duk dan kar ya ɓata maki rai...,kija sane yarinyar nan da za'a bar sa auren ta zai yi dan shaƙuwar da ta shiga tsakanin su a baya bugu da ƙari yana mata kallon yarinyar da ta taimake sa saboda wannan dalili kawai Zaid na iya auren ta kuma babu tambayar hakan dan so dama yakan faro ne da tausayi toh a naki case ɗin sai kika tausaya masa fiye da yadda shi yake tausaya maki wanda ya saka ki zurfafawa da yawa cikin son sa da ƙaunar sa har ma kike kishin sa fiye da yadda mutum zai iya misaltawa kwata kwata baki ganin abin da ya dace da wanda bai dace ba iyakar wanda hankalin ki ya kwanta da shi shikenan shi zaki yi which is totally wrong,,namiji ne fah Zaid a ganin ki kin isa hana sa ƙaro mata ne?ko gani kike son da yake maki zai rinjayi faranta ran sa?namiji ba zai taɓa sakewa da ke ba muddin kika zaɓi ki rinƙa canza hanya da shi ta yadda in ya kawo maki magana sai ki nuna cewa baki tare da shi duk saboda wani dalili chan na ki toh kuwa in kika nuna mai haka dole ya fara janye jikin sa da ke daga haka sai ku nesanci juna abubuwa su ta faruwa a tsakanin ku amma baki sani ba rashin fahimta ta shigo tsakanin ku duk sakamakon laifin mutum ɗaya amma in kika nuna mai kina tare da shi ko da kuwa hakan bai maki ba ba ƙaramar ƙima zai ƙara maki a idanun sa ba dan zai rinƙa counting on you zai ga yana da strength bai da wani fargaba saɓanin ture sa da ingiza sa shi da damuwar sa kawai dan baki yi na'am da shawarar sa ba...wannan kishin da kike ganin sa Bilkisu nayi fah,na yi shi a lokacin da yake da riba ba yanzu ba da in kika yi wuya zaki sha dan mazan zamanin nan ba'a nuna masu baƙar kishi tuni suna jin kan su suna ji da kuɗi da ganin zamanin su ne sai su sauya ki,,.. Babu abin da ya fi ƙarfin addu'a i was very prayerful da ƙarfin addu'a Allah ya yaye min kusan 85% cikin kashi ɗari na kishin da nake fama da shi..na daɗe ina maki addu'ar nan taAllah ya sa kar ki yo gado na ta fannin kishi sai dai ban san me ya sa ba sai gashi kishin ki har yana son ɗare nawa kishin,
Ɗazu da kike narrating min matsalar ki sai na gano wani abu is like you are lacking in your prayer point,baki da ƙaƙƙarfar prayer point Bilkisu dan da a ce kin san falala da ƙarfin addu'a da kin damƙe sa sosai dan shi kaɗai ne zai magance maki wannan tsantsar baƙar kishin ta ki da ya saka ki kasa fahimtar mijin ki..
Bilkisu falalar addu'a mai girma ce dan ni zan faɗi hakan kafin ni akwai mutani da yawa da zasu bayyana maki falalar addu'a kafin su akwai amintattu,Mursalai da addu'a haɗe da falalar ta suke magance masu damuwar su kamar Annabi Ibrahim addu'a yayi Allah ya ƙetarar da shi daga sharrin mutanen sa da kuma wutar da suka saka shi ciki,haka annabi Yunus shima yawan addu'a da tasbihin sa ga Allah ne ya sa Allah ya fito da shi daga cikin kifin nan,ga Annabi Musa ma wanda addu'a yayi Allah ya raba sa da kaidin Fir'auna da mutanen sa a inda ya buga sandar sa ruwa ya rabe shi kuma fir'auna ya halaka tare da muƙarraban sa ciki,ga Annabi Nuhu wanda shima addu'a yayi Allah ya saukar da ruwar ɗufana a duniya baki ɗaya,again ga annabi Muhammad S.A.W wanda shima addu'a yayi Allah ya halakar da Abujahil,Utba da Abu-Lahab har ma da sauran mugayen kafirai maƙiya musulunci,,,kenan kin ga girman addu'a da falalar sa in har mutum ya bi ƙa'idar sa kamar yadda Allah da mazon sa suka umarta,Bilkisu falalar addu'a Allah kaɗai ya san sirrin da yake cikin ta dan haka duk wani damuwa,tsanani da tsaurin da bawa zai tsinci kan sa a ciki addu'a ta ishe sa maganin wannan damuwa ta sa..
Muddin kika riƙe addu'ar nan da hannu bibbiyu Bilkisu wannan kishi naki na Allah ya kiyaye toh ina da tabbacin babu wani magani da zaki sha da zai magance maki shi face falalar wannan addu'ar saboda haka ina nan zan taya ki da addu'ar Allah ya yaye maki wannan kishi taki kema dole ki tasho tsaye da addu'a sannan ki gyara halin ki kar ki ga kina mace wai kina da abin jan ra'ayin mijin ki wannan duk shirme ne dan gidan auren da babu ƙaƙƙarfar addu'a a cikin ta kamar kwanko ne marar abu a ciki so you need to buckle up and improve in your lapses ki gyara zaman auren ki ki rinƙa supporting mijin ki ko kina so ko baki so ki nuna mai kina tare da shi hakan zai saka sa ƙara samin sakewa da ke dan haka kar ki ƙara nuna mai cewa baki son ra'ayin sa always show him that you are with him and i bet you zaki ji daɗin zaman gidan mijin ki and you will say it out to other women out there who are very tedious when it comes to jealousy..
Sannan find it in your heart to understand that girl and also know her reason for doing such dan duk zafin da zaki ji a bayan na mahaifiyar sa ne dan ita ta san zafin sa ke tsintar sa kika yi baki san wuya da wahalar da mahaifiyar sa ta sha a kan sa ba amma ita kan ta ta bar zancen ta dangana hakan da ƙaddarar rayuwa ce wanda babu wanda ya isa ya tsallake sa bare ya canza sa but ke kin zurfafa da yawa cikin maganar kin ɗau abin da zafi kina ta blaming yarinyar ba tare da kin sa dalili ba wanda hakan haramun ne saboda na san kin sani dan kin karanta a hadisi inda ake gargaɗin mu da yin zargi aka ce _iyakuwa zanna,fainna zanna,akhazabul akhihi_ wato fassarar sa shine Allah SWT ya ce _ina maku hani da yin zato,domin ita zato,magana ce ta ƙarya_
You see,tunanin ki lies on this dan haka ku canza ki mai da shi kyakyawa ki rage ko ma ki daina gabaɗaya zargin da kike yi dan wataran kina iya jin kunya akan zargin da ba gaske bane kuma na san ki baki da hayaniya so it will be very bad of you a ce ana maki raddi sakamakon zargin da ba gaske bane these are all minor minor things we ignore in our marriages kuma su ke dawowa su zama manyan matsalolin mu dan haka i hope you will transform your perception into a negative one baby and i pray Allah ya ƙara shiryar mana da ku ya daɗa kare mana ku ya ƙara maku fahimtar junan ku da haƙurin zaman tare ya kaɗe duk wani mugun abu da zai shigo maku marar daɗin ji da gani a rayuwar auren ku dan hankulan mu baya kwanciya matuƙar naku ba a kwance yake ba.Allah ya maku albarka"....

Nannauyar ajiyar zuciya Bilkisu ta sauke sakamakon jin wannan extensive exclusive sermon da mahaifiyar ta ta mata wanda is in different form da ya haɗa da faɗa,wa'azi,wayar da kai,jan kunme and most of all tunatarwar da ta mata akan rashin riƙe addu'ar da bata yi wanda shine kamar garkuwa a gare ta ta san she is weak ta wannan ɓangaren dan bata taɓa zaman yin addu'ar Allah ya yaye mata kishin ta ba ba ma ta tunawa da wannan until now da Umman ta ta tunatar da ita then she is lucky for having a mother like Umma Allah ne kaɗai zai saka mata da alkhairi akan ƙoƙarin ta da take yi akan ta da su ƴaƴan ta ma baki ɗaya..

jan numfashi tayi kafin ta ce
"Umma nagode Allah ya saka da alkhairi ban taɓa yin wannan tunanin har na ware lokaci na na zauna nayi addu'a ta musamman akan sa ba sai yanzu da kika ankarar da ni Umma Allah ya baki lada kuma Allah ya bar mana ke ya ƙara haɗe ki da Abban mu"da murmushi mai sauti ta ida maganar wanda ya saka Hajiya Zeenat murmusawa itama tana faɗin
"Allah ya shirye ki Bilkisu kin mai da ni grannyn ki ko"?sai ta dara tana faÉ—in
"Ni na ma isa Umma"darawa suka yi kafin daga bisani ta kuma yi mata ƴar nasiha kafin su yi sallama ta ajiye wayar ta juya ta kalle sa sai sharara baccin sa yake yi hankali kwance sai ta mai da duban ta ta ga yadda lokaci ya ja har ƙarfe ɗaya da rabi ya gota..
Ɗaga hannun ta tayi ta rinƙa kwararo addu'oi kamar ba zata tashi ba har dai ta shafa ta miƙe zuwa lokacin har biyu yayi..
NaÉ—e dardumar tayi sannan ta cire hijabin ta ta dawo kan gadon ta kwanta haÉ—e da sagale yatsun su wu guda tayi addu'ar bacci daga haka ta rufe idanun ta....
Chapter 150 · 0% Book details