← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 157

Sashe 76

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiyar 15minutes suka yi ya kawo su wani asibiti inda da shigar su ya tsaya a emergency ya kirawo masu kula da lafiyar dake wurin suka kawo mai agaji aka shigar da ita ciki dan duba ta shi kuma ya hau yin zirga zirga a tsakankanin É—akin yana iya hango su a ciki.
Almost 25minutes sannan doctorn ta fito haÉ—e da kiran sa gefe ya tafi jikin sa na bashi wani abin gaban sa na faÉ—i but sai ya ga ta É—an murmusa ta ce da shi
"She is your wife"?a cikin tsantsar damuwa yake dan haka bai san lokacin da ya shiga girgiza mata kai ba sai ta ce da shi.
"She is fine and she will be fit as soon as she wakes up just experiencing her cycle cramps i guess you know that already,so right now we were able to stabilize her and she is calm by 9 you can take her home if she wakes up because she need yo rest adequately but fir now,she is good"godiya ya mata sannan ta tafi shi kuma ya koma ya shiga ciki haÉ—e da zaman jiran ta har ta farka,shu tausayi ma take ba sa ya É—auka ba duka mata ke shan irin wannan wahalar ba sai gashi bayan baby sis É—in sa Bahajjatu a yau ga matar sa ma na experiencing cycle pains hala ma shi yasa ta yi collapsing É—azu..
Tausayin ta ne ya kama sa sosai dan haka ya shiga yi mata fatar samin lafiya as soon as possible..

Awar sa É—aya yana zaune yana jiran farfaÉ—owar ta amma bata farka ba sai ya bar inda yake zaune ya dawo kusa da ita ya tsura mata idanu yana mata kallon tausayi a ce da ran ka da lafiyar Ka amma kayi losing consciousness naka har tsayin awa É—aya he really felt bad and he curse this pains..
Yana kan kallon ta yana jin tausayin ta sai ya ga ta fara mutsu mutsun farkawa,da sauri ya kuma matsawa kusa da ita yana mai riƙo hannun ta cikin nasa har dai ta gama buɗe idanun ta ta ga inda suke ta kalle sa zata yi magana ya riga ta
"Kar ki yi magana,,am sorry i couldn't understand you ɗazu har sai da na bari kika zama helpless am so sorry,doctor ta ce zamu iya tafiya in kin farka dan kina buƙatar hutu shall we?can you walk or i should support you"?da iya gaskiyar sa yake nuna kulawar sa gare ta sai ta girgiza mai kai alamun zata iya tafiya.
Taya ta tashi yayi sannan suka fito haÉ—e da yi ma doctorn godiya haÉ—e da yi mata sallama sannan suka fita.

_*35 minutes later*_

Tana kwance ya shigo ya same ta haɗe da tambayar ta ko akwai wani abin da take buƙata ta ce mai a'a sai ya mata sai da safe sannan ya koma ɗakin sa but sai me??he couldn't sleep he kept on thinking about her yana ji kamar he is connected to her dan haka ya tashi ya bar ɗakin nasa ya nufi nata ɗakin,ko da ya isa har ta fara bacci but he can't leave her all alone what if ta farka cikin dare tana buƙatar wani abin kuma babu mai yi mata kusa.
Da wannan tunanin ya nemi wuri ya zauna kusa da ita ya riƙo hannun ta cikin nasa yana ɗan murzawa duk tausayin ta ya ishe sa he can't wait to see her fit again dan mood nata duk ya canza har maganar da suke ɗan yi basu yi ba wannan ciwo ai wahalarwa ne.
Shi kaÉ—ai yake ta zancen zuci in yayi ya kalle ta ya ji sabon tausayin ta na kuma shigar sa haÉ—e da wani abin da shi bai san ko menene ba..

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

   👄 °°°     °°°👄
              °°
               °

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀*
     _{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

  *SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

  *25*
*_Conspicuous_*

Kamar wasa sai ga Dr Zaid ya shafe awowi sama da huɗu wanda yayi daidai da ƙarfe 1:30am na dare yana zaune yana kallon Bilkisu,idanun sa duk sun yi ja ja zir sun ƙanƙance dan bacci yake buƙata amma baya jin in yayi baccin nan zai wa kansa adalci duba da yadda ita ta tsaya ta dage a lokacin da shi bai da lafiyar ta kula da shi ta tabbatar da safety haɗe da security nasa bata bar sa ba toh me zai sa shi ya bar ta tana cikin halin nan ya je ya kwanta saboda selfishness bai jin zai iya wannan abin.
  Countless times without number yana jin hausawa na faɗin kalmar *_"IYA RUWA FIDDA KAI"_* amma bai san cikakkiyar ma'anar kalmar ba a hausance all he know shine yadda ake amfani da kalmar cikin magana dan dasawa mutum baƙa hakan ne ma ya saka sa gayawa Bilkisun a lokacin da ta nemi sanin dalilin zuwa da ita da zai yi yola dan yin outreach but apart from wannan bai san ma'ana gamsasshiya da za'a iya alaƙanta kalmar da ba..

  Ɗago kan sa yayi ya kalle ta tana bacci cikin doguwar rigar baccin ta da kaɗan ya rage ya kai mata ƙasa hular baccin ma duk ya fita daga kan ta gashi nan a gefen ta kamar dai kullum tayi twisting sumar kanta ne ta tura ciki babu robber band bare wani abin takura.
   Bayan ya gama ƙare mata kallon ne ya kai hannun sa cikin salon da ba zata ji ba bare ta tashi daga nannauyar baccin da take yi,warware mata suman yayi a hankali sannan ya shiga gyara mata cikin taka tsantsan dan kar ta farka ta kasa komawa baccin.
  Da ya gama gyara mata sumar sai ya cire hannun sa daga kan ta ya kawo ya haɗa da wanda ya riƙe hannun ta da shi ya maida idanun sa kan ta yana kallon ta shi kam bai taɓa jin tausayin mace har haka ba tun da yake a rayuwar sa yana iya cewa ko Bahajjatu dake ƙanwar sa har yake iƙirarin son da yake mata na daban ne toh har ita bai jin ya taɓa yi tausaya mata kamar yadda yake tausaya Bilkisu a halin yanzu,ya kasa tantance ɗaya abin da ke damin sa game da ita dan irin feelings da yake experiencing time to time ba tausayawa bane kawai dole akwai wani abin na daban wanda yake buƙatar ƙarin haske akai.
  Toh wai ma ya aka yi tun da chan baya bai taɓa jin irin wannan abin ba?da da suke tare a kullum da in tayi magana yayi sai dai tayi shiru kuma akan gaskiyar ta take maganar ko da kuwa yin maganar sa na nufin janyo mata babbar disappointment ne bata cigaba da magana sai dai ta yi shiru ko ma ta bar wurin highest in ya ɓata mata rai da yawa sai ta aika mai da mugun kallo ta yi tsaki tayi tafiyar ta but bai taɓa jin ɗigon tausayin ta ba sai yanzu,yanzun ma a yau a wannan halin da ya ganta.
  Dole wannan tausayin ba shi kaɗai bane akwai wani al'amari behind it ba natural bane..
  A karo na sau ba adaɗi ya kuma kallo ta tana baccin ta cikin kwanciyar hankali,mai da idanun sa yayi ga flower vase dake ɗakin sannan ya dawo da idanun sa gare ta sai kuma ya koma duniyar tunanin sa
  A halin da ake ciki yana ganin kamar muhimmancin ta a gare sa is more fragile than the flower vase,yana ji a jikin sa kamar akwai wani babbar al'amari that is yet to come his way sai dai kuma kamar akwai hindrance da zai yi forming babbr rift a tsakanin sa da ita..
  Jin faɗuwar gaba yayi ba tare da ya san dalilin hakan ba,kallon ta yayi sai ya ji faɗuwar gaban ya ƙaru ninkin yadda yake ji,shiru yayi yana son dawowa daidai sai dai abin ya ci tura dan the more thought of separation ya zo mai sai ya ji heart race nasa na ƙaruwa.
  Toh shin me ma yasa yake tunanin wataran zasu iya rabuwa alhalin gasu nan tare kuma in bai manta ba they are married so why is he thinking about separation?ko dai bai da lafiya ne bai sani ba?

  A wannan karon da ya kalle ta sai ya ji yana son kwanciya next to her maybe zai sami sauƙin raɗaɗin da yake ji a ran sa dan haka ba tare da wani doguwar tunani ba ya saki hannun ta ya tashi daga zaunen da yake ya dawo kan gadon ya kwanta a left side adjacent to her ya juyo fuskar sa daidai nata fuskar yana kallon ta.
  Akwai wani maganaɗisun da ke ingiza sa yin abubuwa da dama da bai gama yin shawara da zuciyar sa akan halascin su ba amma yana jin in bai yi abin ba toh kamar a takure zai kasance wannan ne dalilin sa ma na barin ɗakin sa ya shigo nata kenan ba tare da ya tsaya yayi doguwar tunanin abin da zai yi ba sannan yanzu da yake zaune ya tashi daga zaunen da yake ya dawo kan gadon ya kwanta next to he,kuma ikon Allah sai ya ji faɗuwar gaban da yake experiencing ya ragu kusan kashi talatin cikin ɗari,yana kallon nata ne yana tunanin zuci har bacci mai naiyin gaske ya ɗauke sa wanda bai san ba a ɗakin sa yake ba dan he feel very comfortable and free a inda yake sanadiyar samin lafiyayyiyar baccin da yayi kenan..
Chapter 76 · 0% Book details