← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 157

Sashe 155

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

************
A haka rayuwa ta tafi masu har kawo lokacin bikin su Baha da Afzal,Allah yayi an yi biki lafiya an ida lafiya sai kuma fatar samin dawwamammen rayuwar aure mai albarka..

Watanni sun ja Bilkisu cikin ta yayi girma dan har ya shiga watanni takwas tun tana watan ta na shida ta yanke alaƙa da zuwan asibiti da sunan yin aiki dan wasu lokutan tare da shi suke aikin wasu lokutan ya ce da ita ta huta but yanzu tayi nauyi da yawa duk jarabar sa haka yayi transforming ya dawo tsantsar tausayin ta da son kulawa da ita dan gani yake yanzu tafi buƙatar kulawar sa fiye da da,tashi da ƙyar zama da ƙyar ga tsoron ranar haihuwar nan bata bar ta ba ita gani take kamar mutuwa zata yi a ranar haihuwar shi kuwa ya tsani ta kirawo mai sunan mutuwar nan dan hankalin sa tashi yake yi..
Yayin da amare kamar haɗin baki suka yi anko Ammi an kuma samin ƙaruwa abin da ta daɗe tana biɗa wato ƴan dugwi dugwi a gidan ta Allah ya bata ga Bilkisu da ta kusa haihuwa nan da wata ɗaya ga Baha dake ɗauke da cikin wata huɗu sai matar Afzal dake ɗauke da cikin wata uku abin ba'a cewa komai Ammi murna kamar me zata yi jikoki har uku ko ma sama da haka wannan baiwa da kyauta ai sai ubangiji duk zumuɗin iyaye matan har ya ɗare na su Prof da Dr Maher dan su maza ne suna iya ɓoye over happines ɗin su...

Hira suke yi da shi yana matsa mata ƙafa tana kishingiɗe duk jin kan ta take wani iri ita dai gata nan kamar lafiya kamar ba lafiya ba hirar da yake mata ma ba shigar ta yake ba kawai jin sa take..
Lura yayi da yanayin ta sai ya dakata daga yin tausar ya tambaye ta
"Mom twins anya lafiyar ki ƙalau kuwa tun jiya ban cika gane maki ba"!!
"Hmm hero kamar ban da lafiya"hankali tashe ya ce
"Ina ke maki ciwon"hannun ta ta kai waist É—in ta ta nuna mai sannan ta kai bayan ta,tuni Zaid ya birkice
"Could it be labour"!?zaro idanun ta waje tayi sai ga hawaye ita ta daÉ—e tana tsoron zuwar wannan rana gani take kamar mutuwa zata yi
"I don't wanna die hero bana so in mutu ka kirawo min Umma na ta taimake ni wallahi bana so in mutu"sai kuka sai shima ya ji kamar ya taya ta kukan tun da ta shiga watar haihuwar ta take tsananin tsoron zuwar ranar haihuwar wanda har shima ya fara tsorata da zuwar ranar dan ya ma yi concluding ba zai karɓi haihuwar ba sai dai su tafi asibiti..
Riƙo sa tayi tana battling da numfashin ta da ƙyar take faɗin
"Zaid kamar amniotic sac ɗin nan ya fashe ina jin ciwo sosai help me please.....i don't want...to die"..abin sai ya ƙara rikita sa ya rasa abin yi sai da ya ga da gaske tana yi kamar wacce zata yi passing sannan ya hau birkita drawer ɗin yana nemar car key sai sannu yake mata tsabar ruɗewa jallabiyar da ya dawo da shi daga masallaci bayan sallar asr da shi ya fito sungume da ita a jikin sa tana nishi tana damƙe sa da gudu ya isa motar ya buɗe ya saka ta ciki shima ya shiga ya rinƙa danna horn aka buɗe gate ɗin a tsiyace ya bar gidan yana sharar gudu dan gani yake in ya ƙara yin wani delay toh yana iya rasa matar sa a motar ya kira Ammin sa ya sanar da ita daga haka yayi wurgi da wayar ya cigaba da ba motar wuta..

*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*âšœBWA*

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_

👄 °°° °°°👄
°°
°

*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_

*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*

*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim

_Ina alfahari da ku ƙungiya ta wato Brilliant writers Association bcoz u'v always been there 4 me,u supported me i have nothing more 2 say to u except a special prayers tncu all🙏💋_

_Godiya ta musamman ga ɗaukacin masoya na masu ƙaunar rubutu na i want to thank u in a special way Allah ya bar ƙauna tncu so much 4 d unconditional luv dearies🙏_

_Friendy Ahumaggahress i wanna tell u that u are d best out of all u'v been very supportive and encouraging Te Amor Friendy Surayyahms sakhallahu khair_ 😘

*45*
*_The love saga_*

A tsiyace ya taka burkin motar a sa'ilin da ya shiga harabar asibitin hankali tashe cikin rashin natsuwar zuciya ya sungume ta suka yi cikin asibitin lokacin Bilkisu ta fara losing consciousness nata ji take kamar ta fasa ihu kawai ta hutu tsabar azabar da ke addabar ta tun da Umma ta haife ta bata taɓa experiencing intensive pains har haka ba dama haka haihuwar take shine wasu ke gasar ɗaukar ciki ita ba zata kuma yarda Zaid ya ƙara yi mata wani ciki ba tana haife wannan shikenan irin wannan azaba da me yayi kama...

Yayi tunanin zai iya ɗaukar zafin raɗaɗin da take ciki sai kuma ya ga abin ba nasa bane,matsawa yayi gefe yana mai yi mata addu'ar sauka lafiya da fatan samin ta cikin ƙoshin lafiya after delivery ɗin.
Battling take da rayuwar ta cikin É—akin haihuwar nan ihun dai ta kasa yin sa amma azaba da raÉ—aÉ—i kam babu wanda bata sha kalar sa ba,shafewar kusan awa gyda babu haihuwa babu labarin sa abin ya firgita Zaid ba kaÉ—an ba dan tuntuni su Ammi da Baha suka taho asibitin yayin da aunty Zee matar babban yayan Bilkisu ta biyo su a baya hankali duk ya tashi sai faman calming nasa ake amma shi gani yake each passing second kamar life É—in ta ne ke tafiya cikin battle field É—in nan..
Da abin ya ishe sa sai ya tashi yana faÉ—in
"Ammi zan tafi ciki ban san me suke mata ba da ya hana ta haihuwa tun ɗazu at least ai labour ɗin ta has been a progressive one tun jiya take labour ɗin nan abu ɗaya har yau bata sami sukuni ba sannan na kawo ta nan sun kasa bata natsuwa,i have to do something Ammi"ya faɗa cikin tashin hankali wanda ya saka Ammi restricting move ɗin sa ta riƙo hannun sa cikin girgiza mai kai ta ce
"No Zaid,you can't predict a labour and delivery, yakan zo ne a yanayi daban daban ko ka shiga ciki muddin lokacin haihuwar bata kai ba babu abin da zaka yi kayi inducing labour É—in nan the only thing she needs from you right now is your prayers and nothing but that okey?dan haka ka dawo ka zauna,just pray for her har Allah ya sauke ta lafiya"...dafe kafaÉ—ar sa tayi sai ga idanun sa sun yi ja tausayin matar sa yake sosai shi yasa take ta faÉ—in tana tsoron zuwar ranar haihuwar nan Allah kaÉ—ai ya san abin da take ji da ya sa take tsorata da ranar haihuwar...

Suna zaune a wurin Ammi na ba sa magana Baha na kan waya da Bilal akan halin da ake ciki na haihuwar,sai aka kirawo mijin mai naƙuda
"yes am hear"ya amsa cikin zaƙuwa sai matar tayi murmushi sannan ta ce
"Congratulations sir your wife just gave birth to a bouncing cute baby boy"direct ƙasa yayi yayi sujjadar nuna godiyar sa ga ubangijin sa da ya mai wannan rahama da falala tasa ba tare da ya biya ko sisin sa ba...
Ammi ce ta ƙarasa cikin ɗakin sai ta ga improvising aka yi aka nannaɗe jikan nata da towel ai sai ta dawo da hanzari ta aiki Baha ta tafi gida ta dubo mata ma'adanar ta akwai baby carriage sky blue ta ɗauko duka ta taho da shi..
Cikin sauri ta bar asibitin gashi itama tana ji da kan ta amma saboda murna da farincikin sun yi É—a ya sa duk bata lura da wannan ba ta baza iska saman titi ta nufi gida komai a hanzarce ta yi sa ta dawo asibitin..
Lokacin da ta dawo har an kai Bilkisu ɗakin hutu tana ma wanka dan hana Zaid shiga Hajiya Madina tayi wai sai an gyara Bilkisu da baby kar ya shigo ya ga ta canza mai farat ɗaya shi kam abin bai wani ɗaɗa sa da ƙasa ba so yayi ya riga kowa gani da ɗaukar ɗan sa sai dai Ammi ta hana ta rufe hanya shi kuwa duk rashin kunyar sa ba zai iya yin sa gaban Ammin sa ba..
Chapter 155 · 0% Book details