← Book details Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 157

Sashe 39

Iya Ruwa Fidda Kai Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ni har na fara targeting Bahajjatu thinking ita ce ta fitar da ita daga ɗakin nan ashe ba ita ba ce kai n...."a nan kalmar ta maƙale mata sakamakon fitinannen kukan da ta fashe da shi wanda daga cikin zuciyar ta kukan ke fitowa sai ta yi hanzarin riƙe ta ta shiga tambayar me ya same ta a nan Bilal ke sanar da ita abin da ya faru sai ta yi mamaki kenan dama ranar da ta mata bayanin komai bai shige ta ba kenan ya ɓace mata a memory na ta but kamar wannan kukan ba akan ganin Zaid a halin da yake ciki bane kawai is like there is something hidden beneath the tears but what could it be?rashin samin amsa ya sa ta zaunar da ita a kan gadon ta fara rarrashin ta tare da bata magana ita duk a tunanin ta ganin halin da Zaid ke ciki ne ya saka ta yin kukan though tana suspecting akwai ɓoyayyiya but since she refuse to say a word sai kawai ta ƙyale ta after all bai kamata ta shiga damuwa ba da farfaɗowar ta haka da wuri..rarrashin ta ta ke yi sosai har da gaya mata ai yadda ta farfaɗo ba tare da sun yi tsammani ba haka Zaid zai farfaɗo shima akan ta dai yi mai addu'ar samin lafiya,sauraron Hajiya Madina ya zame mata dole shi ya sa take sauraron ta ba wai dan maganganun ta na tasiri a zuciyar ta ba dan kuwa babu magana ko ɗaya nata da ke shigar ta ko kaɗan har ta kai ayar maganar ta kuka kawai take yi daga ƙarshe dai kiran doctor aka yi ya zo ya mata abin da zai yi seducing ɗin ta ta zamo calm..

Hakan aka yi dan allural anti depressant aka bata wanda babu jimawa bacci mai nauyi yayi gaba da ita sai a nan suka sami kwanciyar hankali,Bilal dai ya kasa ganewa wannan murɗaɗɗiyar al'amari dan shi a iya sanin sa babu wata jituwa tsakanin brother In-law da twin sis ɗin sa kafin su tafi outreach ɗin nan kuwa he can swear that sam ba da niyar ta aka yi tafiyar ba but what later happened bayan tafiyar su?did they manage to get closer to each other?did they understand each other in the course of their outreach?toh wa ma zai ba shi amsa?babu dan haka ya ƙara ba ma Ammi haƙuri akan fitar da ita da aka yi ya sanar da ita shi ke da laifi ba Bahajjatu ba dan sarai ya san halin Ammin sai ta balbale masa apple which he hate more than anything,faɗa ta mai akan ya kiyaye fitar da ita anyhow saboda she is still in convalescence stage bata da damar yin abubuwan da ta saba yi a baya sai a hankali zata mayar da jikin ta,haƙuri ya bata kafin ya mata sai da safe dan yana son tafiya harhaɗa kayan sa na komawa.

  Fitar sa babu jimawa Bahajjatu ta shigo ɗakin duk a ɗan ɗarare dan tsammanin ta Ammi ta san ita ce ta fitar da Bilkisu har fitar ya janyo mata collapsing she thought Ammi is just waiting for her to give her a sound slap dan Ammi bata tolerating shirme hatta da Hakim da ke babba da ita in ya nemi ja da yawa da Ammin sai ta mare shi babu abin da ya shafe ta sai dai in abin ya lafa ta bi shi ta ja shi a jiki a nan zata mai faɗa da nasiha sannan ta ɗora da rarrashi..
   Sai ta ga akasin hakan sai ma ta ga Ammi tana tambayar ta ina ta shiga
"Baha ina kika tafi ga Bilkisu har ta famo rashin lafiyar ta Bilal ya fitar da ita ya kai ta ɗakin yayan ku now she has collapsed ban san me yasa Bilal ya fitar da ita ba alhalin ya san halin da ta shiga i hate to see her sleeping bana so it scares me"jin waɗannan bayanai na Ammi sai ta sami sauƙi a ran ta Allah sarki her apple ya amshi laifin da bai da masaniya a kai duk dan yana gudun kar Ammi ta balbale ta.
  Rungume ta tayi ta ce
"Is okey Ammi she will wake up inshaAllah zasu farka mu cigaba da yi masu addu'a kawai kin ji Ammi na"?girgiza mata kai tayi suka kalle ta daga bisani suka fita suka ja ƙofar suka rufe mata dan ta sami peaceful sleep..

  ************
A nan hotel apartment Hajiya Zeenat ce kwance tana kallon Dr Muhammad da ke ta faman bincike a laptop dan ya kai kusan awowi uku yana faman binciken da ya ke yi wanda binciken ba akan komai bane face akan remedy na rashin farfaɗowar Zaid Maher dan almost 4 days kenan ya fara research ɗin saboda shi kwata kwata bai gamsu da 3-4months da doctor ya faɗa masu a matsayin period da zai yi spending yana unconscious ba sam bai yi buying idea ɗin ba ya fi yarda da ya binciko makarin matsalar da kan sa a matsayin su na iyayen sa dole su nemar mai lafiya dan wannan duk ba zai kawo masu kai ba time is passing ba zai tsaya jiran kowa ba likewise if care is not taken they might loss him Allah dai ya kiyaye baƙar ranar.wannan shine babbar dalilin sa na takura kan sa ba dare ba rana yana binciken abu mafi sauƙi da zai samo masu hanya mai ɓillewa ba wai ya raina taimakon likitocin bane a'a but yana ganin suna ɓata golden hours da suka samu dan su samarwa da Zaid lafiya shi yasa yake bincike binciken da yake yi with the hope that in an dace Zaid na iya farfaɗowa within a month or less ba sai an cigaba da jiran gafara sa ba'a ga ƙaho ba.
  Yana tsaka da binciken sai ya ji hannun ta a kafaɗar sa tana mai massage kaɗan kaɗan,lumshe idanu yayi kafin ya buɗe su ya ce
  "Thank you so much"!!
Murmushi tayi da ta daÉ—e bata yi irin sa ba tace
"It's my pleasure my prof".
Ɗan shiru ne ya ratsa wurin kamar mintuna biyu sai ta ce. 
"But prof me zai hana ka kwantawa ka huta in ya so anjima sai in ta da ka ka cigaba da research ɗin or i might even help you you don't know"!!shiru ya mata dan shima ya san yana buƙatar hutun but he just can't he have a task da dole ya ƙarasa dan haka ya ce
"Nahh sweetheart je ki kwanta zan cigaba i will join you later saura kaÉ—an in gama gabaÉ—aya ma research É—in dan mu sami hutu da sukuni dukkan mu humm"??ya zuba mata idanu amsa mai ta yi tana mai jin tausayin sa na shigar sa madaÉ—in ta kwantan sai ta ta gyara kujerar kusa da shi ta zauna ya dube ta da mamaki ya ce
  "Baccin fah?kin san dai gobe ke zaki tafi asibitin nan dan ya kamata Hajiya Madina ta huta haka nan"!amsa mai tayi ta ce
"I know but ba zan iya ba kin ga saura ƙiris in kammala dan Dr Maher bai da sukuni kuma kin ga after all these hallacin da yaron nan yayi mana kafin Bilkisu ta amshi kwatan ragamar ayyukan nan namu ina ganin kamar ta nan kaɗai zan iya saka wa mahaifin sa da family ɗin ma baki ɗaya i just need your prayers and support"rungume shi tayi ta ce
"I know your purpose Dr na san dalilin ka kuma ina taya ka addu'ar samin nasarar wannan aiki da kaje yi Allah ya ba su lafiya"da amin ya amsa daga haka suka cigaba da zaman shi yana aikin sa ita kuma tana zaune beside him jefa jefa sukan yi hira.
  Sallama suka ji an yi a ƙofar ɗakin sai ta miƙe ta nufi ƙofar,leƙawa tayi ta ga mai sallamar sai ta buɗe haɗe da amsawa,bashi hanyar shiga tayi ya shigo ta mayar da ƙofar ta rufe suka ƙarasa shigowa parlorn tare zama yayi ya gaida iyayen sa amsa mai suka yi kafin ya sanar da su dalilin zuwan sa akan komawa gida fatan alkhairi suka mai haɗe da addu'ar kariya daga sharrin hanya da na ƙarfe..
Chapter 39 · 0% Book details